Page 3•

82 8 0
                                    

BAYAN WUYA

© ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION

® Basira Sabo Nadabo

Bismillahir-Rahmanir-Rahim

3•

"Aradun Allah kika fashe tulun nan a jikin ki zan haɗa wani donni Hajjo bana ɗaukan asara balle nasan wata aba wai hakuri, don bana yinta tunda jajayen sawuna balle yanzu da girma tazo min ke don shanun gidan ku nace ki tafi ɗibo min ruwa ki zauna acen rafi kina watsewarki da maza ko Inna Wuro?"
   Ruwan tayi saurin juyewa a mazubi sannan ta durkusa ƙasa tace

"Inna Hajjo aradu ba watsewa nake da maza ba kuma ni ban tsaya wasa ba rafin ne na tarar da maza cike a gurin shine na janye kafa suka tsahirta sannan naje na ɗibo ruwan amma don Allah kiyi hakuri"

"Rufe min baki makira mai makircin tsiya wato kema an titsiyeki a ɗaka an koya miki makirci ko toh ahir ɗinki Inna Wuro, don aradu nikam bazan jure makkrcinki ba uwarki tayi kema kiyi makira wacce tayo gadon annamimancin tsiya"
     Gyaran muryan Imamu Demba ne yasa tayi shuru karasowa yayi ya zubawa Inna Wuro ido sannan yace

"Inna Wuro me yake faruwa naga shatin tsumagiya a jikin ki?"

"Lakaufun Alaihi yanzu Malam kana kallona amma ka tsallake ni kake tambayar Inna Wuro abinda yake faruwa, lallai ina kara yadda da abinda mutane ke faɗa an dafa kanka a tukunya kuma an baka kaci lallai Malam, toh nice na duketa ko zaka rama mata ne? Nace ko nima zaka ɗauki maduki ka dokeni ne?"
      Girgiza kai yayi yana jinjina halin irin na Hajjo sannan yace

"Kullun ina kara tunatar dake girman ɗan adam a gurin Allah da kanshi wanda shine ya halicci ɗan adam kuma saboda kauna da soyayya dake tsakanin mu dashi sai ya ɗauki wannan abinda ya halitta domin yayi mana kyautar da zata faranta ranmu, kuma ina kara tunatar dake Hajjo a lokacin da Allah ya bamu ƴaƴan nan bai banu da tabo a jikin su amma idan suka tashi komawa ga mahaliccin su sai su koma da tabo a jikin su kuma kisani wallahi Allah sai ya tambaye ki me yasa ya baki ita babu tabo amma kuma da zata koma yaga da tabo a jikinta me zakice da Allah (SWT) Hajjo? Toh ina shawartarki da tun yanzu ki tanaji abinda zaki faɗawa Allah domin nidai Allah da Mala'ikunsa shaida ne a kaina ban taɓa ɗaukan hannuna na doki wani da yake ƙarƙashin ikona ba balle harta kaiga nabar masa tabo a jiki, kema ina addu'ar Allah ya shirye ki Hajjo yasa ki gane gaskiya a koda yaushe gaskiya ce"
     Fashewa tayi da kuka ta ɗaura hannu aka haɗe da cewa

"Yau nikam na shiga ukku na yau Malam ni zaka kalla kaciwa mutunci agaban makiyana, Malam me nayi maka hakane da kake min wannan azabar a gaban abokan gabana"

"Allah ya shirye ki Hajjo yasa ki gane kuma ki daina wannan wautar a gaban ƴaƴanki tunda ke har yanzu baki girma ba, Allah ya ganar dake"
    Ita dai Inna Wuro tana tsugunne a inda take kukanta sai tsanta yakeyi don Allah ne kaɗai zai ceceta yau kam, Inna Ƙariba tana jin duk abinda yake faruwa kuka takeyi na tausayin ƴarta gashi babu damar zuwa kwatarta, domin duk bafilatin asali koda yanka ɗanshi za'ayi akan idonshi bazai ɗaga ido yace don me ba wannan alkunyar itace take cutar Inna Ƙariba akan ƴaƴanta, musamman Inna Wuro don ita macace su kuma sauran basa zaman gida kullun sune ke kora shanu zuwa kiwo, Lukman ne ya fito ya watsa mata kaya a jiki yace

"Gasu nan yanzu nake son ki wanke minsu kuma ba'a rafi zakiyi wankin ba a cikin gidan nan zaki wanke, sannan yanzu nake son ki wanke su don dasu zani shaɗi yau"

"Haba Ya Lukman kabari mana tayi mana abinci donni wallahi yunwa nakeji kuma zani bikin shaɗin Hajara kuma an kusa farawa amma kuma kace wai tayi maka wanki, nidai gaskiya saita fara mana abinci" ta karashe maganar a shagwaɓance

"Ana magana kin kuremu da manyan idanunki kina kallon mu zaki tashi kiyi musu abinda suke so ko kuma so kike Aisha tamin kuka, kitashi nace ko kuma saina kara zuba miki tsumagiya"
     A tsawace tayi maganar har saida Inna Wuro ta rasana da gudu ta tashi ta nufi madafi ta ɗaura sanwar tuwo miyar yakuwa da kuɓewa, sannan kuma tayi saurin zuwa rafi ta ɗibo ruwa ta wanke kayan Ya Lukman, saboda horo da tayi da aiki yasa nan da nan yasa tayi saurin gama aikin kuma ko data gama aikin babu abinda ta tsira dashi sai tuwo kwarya ɗaya kuma gaba ɗaya ɗakin ne akan wannan tuwon, koda ta kaiwa Inna Ƙariba taga tuwon bata damu ba saboda tayi ɗan karamin murhu a ɗakinta inda take dafa abinci ba saita jira kwaryan Inna Hajjo ba, kuma su Ya Umar suna kokarin kawo mata abincin da zasuci basai sun jira kwaryar Inna Hajjo ba, tuwon data kawo Inna Ƙariba ta kalla sannan tace

"Inna Wuro kece ya dace kici abincin nan tunda kece kikayi wahalarsa" tausayin yarinyarta ne kwance akan fuskarta

"Toh amma Inana kuf...."

"Kinga Inna Wuro bana son jin wani magana a bakin ki saboda in bakici abincin nan ba toh kila zai zama haramiyarki don Innarki baza tabarki hakanan ki zauna ba, kiyi maza kici Inna Wuro nasan duk inda Innarki take yanzu tana tafe don kiranki don bazata taɓa barinki ki huta ba kamar kowa, ke dai kallar taki ƙaddarar kenan Inna Wuro Allah ya dubeki da idanun rahamar sa"
      Maganarta kaɗai zai tabbatar muku da irin tausayin da take binnewa a kasan zuciyarta ita dai Inna Wuro sai aikawa cikinta sakon tuwon da yasha man shanu takeyi, ɗaga azaren akayi cikin gatsali tace

"Ke Inna Wuro jirana kikeyi nata buɗe murya ina kiranki duk makwafta su shaida ko?"

"A'ah daman yanzu nake son zuwa saboda nasan zaki nemeni wanke hannuna zanyi yanzu inzo" duk ta wani rikice jikinta har rawa yakeyi

"Auho ashe dai da gangan kenan kika ƙi fitowa saboda kinajin huɗubar tsiya ko?"
      Inna Wuro ta kalla Innarta taga ta sunkuyar da kai kasa yasa tayi saurin girgiza kai tare da shanye kukan da yazo mata, murmushi Inna Hajjo tayi haɗe da cewa

"Kina kallon munafukar uwarki ce toh itama ta buga dani tabarni balle ke karan kaɗa miya, zaki tashi kije tatsa ne ko kuma kina jiran nace kije ki gyara makwancin dabbobi ne?"

"Yanzu zanje nayi Inna Hajjo don Allah kiyi hakuri inna ɓata miki rai"

"Shegiya makira kin iya kalallame mutun da magana abin kaɗan ki haɗani da Allah bayan ba fina sanin Allahn kikayi ba, gashi kinayin abu da isa haɗe da takama koda ke jinin sarauta ce amma kuma a gurina ke ba kowa bace face kaskantacciyar baiwa wacce da ita da tafin kasan takalmi na duk abu ɗaya na ɗauke ku, ko Aishatu batayin abinda kikeyi kuma kina zaune Aishatu zata auri gangariyar namiji ke kuma kam sai dai ayi sadaka dake makira"
     Wannan ba sabon zagi bane a tattare da Inna Wuro don inda zagi yana tsiro a jikin mutun toh da babu inda zagi bayyi ya banya a jikin Inna Wuro ba har a samu a fitar da amfanin zagin, turken shanun ta shiga ta hau gyarawa kamar dai kullun shanun ma inhar suka ganta har wani kukan murna sukeyi saboda sun san ita ɗin mai tausayin suce, inko Imam yace Aisha ce zatayi aikin to ina tabbata muku da jikinta duk kashi zata fito saboda ketar da take musu shiyasa suma suke rama ketar da take musu, fara tatsar tayi tanayi tana waka suma shanun suna amsa mata kuma wannan ɗabi'arta ne shiyasa suma da sunji ta fara zasu fara amshi amma da kuka suke mata amshin kuma hakan ba karamin nishaɗi yake sata ba don har mantawa takeyi da damuwar Inna Hajjo, kwankwasa kofar akayi tayi saurin dawowa cikin nutsuwarta haɗe da cewa

"Waye?" da rawar murya tayi magana

"Uwar kice kinji ko, ba cewa nayi kiyi maza ki gama aikin nan ba don zakije min kasuwa ko Allah zaisa ki samu wanda zai shin-shina ki, ya kwasarwa kansa jaraba da tsiya don zai kwasarwa kasan ne gadon baƙin jini masu irin tsiya"

"Babu inda Inna Wuro zata da magariban nan don bamu ce miki mun gaji da itaba ko kuma mun gaji da ganinta a cikin gidan nan ba, kuma wallahi duk abinda kikeyi ba tsoronki  mukeji ba kawai muna bin maganar Innar muce inba haka wallahi da nayi kasa-kasa dak....."

"Kai Umar!! Ashe baka da kunya baka data ido saboda rashin ɗa'a shine zaka tsaya kana sa'insa da mahaifiyyarka ko? Nagode Allah yayi maka albarka kuma ina roka maka shiriyan Allah da gaggawa Umar"
        Cewar Inna Ƙariba dake gefen ɗaki tana zaune don tun shigowar Umar ɗin ta lura dashi a zuciye yake, shiyasa tayi saurin kauda idonta gefe kuma ta gamayi masa magana bata juyo ta kalleshi ba balle ta kalla inda Inna Wuro take don duk abinda Inna Hajjo take faɗawa Inna Wuro akan idonta takeyi kuma bata ɗaga ido tace mata don me ba

ƳAR NADABO

BAYAN WUYA (On Hold)Where stories live. Discover now