BAYAN WUYA
© ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION
® Basira Sabo Nadabo
Bismillahir-Rahmanir-Rahim
Wannan shafin ɗungurugun ɗinsa naki ne Besty na Bieeborh'n mu kuma nagode da shawarar ki sannan da yardan Allah zayi aiki dashi a aikace ina tabbatar miki zaki gani da idonki, Nagode Bieeborh Mii Allah yabar so da kauna da zumunci me ƙarfi. Amin Ya Rabbi
8•
"Daɗi na dakai kuka kamar mace gaka da zuciyar jarumta amma abu kaɗan in baka samu damar aikata shiba sai ka zauna kata kuka kamar mace, haba Usmanu maganin maza banji daɗin wannan kukan da kakeyi ba ita kuma wacce kake kukan don itafa me kake son tayi ko itama kana son ta zauna kuta kukan tare ne?"
Ya girgiza kanshi duk da haka hawayen bai daina zuba akan fuskar shiba Bakaam ya cigaba da cewa"Toh don haka kai kayi shuru itama ka rarrashe ta tayi shuru saboda inhar kai bakayi shuru ba itama ba daina kukan zatayi ba, duk hakuri zamuyi da yanayin rayuwar da muka tsinci kanmu In Shaa Allahu BAYAN WUYA sai daɗi kuma da yardan Allah daɗin zaizo, Innan mu kema kiyi hakuri ki ƙara akan wanda kikeyi saboda yau badan hakurin kiba da muma bamu a cikin gidan nan amma saboda hakurin da kikeyi shiyasa Allah ya baki mu, ko kina tunanin mu ƴaƴanki da Allah ya baki ba saboda hakuri bane?"
Ta gyaɗa kanta tana kokarin maida hawayen da yake barazanar sauko mata, Bobboi ne ya lura da halinda yake ciki sannan ya cigaba da cewa"Wallahi bazanyi kaffara Allah baya taɓa barin masu hakuri suna taɓewa, koda kika ga Imam yayi shuru a lamarin gidan nan hakan ba yana nufin baya sonki bane saima ƙaunar ki da yakeyi kuma yana girmama ki sannan ya ɗaukaka darajar ki a cikin zuciyarsa, duk muhaɗu mu cigaba da bawa junan mu hakuri akan halinda muka tsinci kanmu a ciki kunji?"
Duk suka ɗaga kai suna mai masu gamsuwa da abinda ya faɗa musu kuma tabbas babu karya a cikin bayanan shi
Inna Hajjo na fitowa taci karo da Umar tsuggune a kofar ɗakin Malam, wani faɗuwar gaba taji haɗe da kasa kallon inda yake amma da yake masifar a cikin jinin jikin ta yake yasa ta mazge tanayi masa kallon kaskanci, kallon tsanar data hango ne a idon Umar ya tabbatar mata da yaji duk abinda Malam ya faɗa, cikin faɗa tace"Mutun sai naci kamar uwar sa in banda halin iskanci da nuna cewa ba Malam bane uban daya haife ka, me zaisa da Malam yace kabar kofar ɗakin shi kaƙi bari don taurin kai irin na ɗan shege"
Murmushi Umar yayi maimakon maganar ta bayyana ƙunar da zuciyar shi takeyi masa, saima kokarin danne abin yayi ya sassauta muryar sa haɗe da cewa"Ba Imam ba hatta tsofaffi da yaran wancen lokacin sun tabbatar da zuwan budurcin Inna ta, wata kuma fa? Na barki da sauran zancen"
Yana kaiwa nan ya shige ɗakin Imam ya barta da sakakken baki tana jinjina karfin hali da zuciya irin na Umari da zai kalli tsabar idonta ya faɗa mata wannan maganar, yana shiga ɗakin ya saki fuskan shi ya zauna a inda ya tashi, Imam ya kalleshi haɗe da cewa"Badai laɓe kamin kaji tsirrin matata ba?"
Murmushi Umar yayi sannan yace"Nasan girman zunubin mutumin da yakeyin laɓe toh ni akan me zanyiwa mahaifina laɓe naji tsirrin ɗakin shi tsakanin shi da matar shi, kawai dai ina zauna ne a kofar ɗakin kuma ni banji abinda kuke faɗa ba domin hankalina ya tafi cen guri me nisa yana tunanin amsar da zaka bani, kaga ko babu yadda za'ayi naji abinda kuka faɗa"
Shima murmushin Imam yayi haɗe da cewa"Hakane kuma na gamsu da bayanan ka kuma sannan akan wancen maganar, Umar a gaskiya kayi babban nazari da tunani game da abinda zai kawo cigaba a cikin wannan kauyen namu dako wutan lantarki bamu dashi balle kuma ace an janyo mana ruwa kamar yadda nagani a Maya Balwa, wato Umar samun wannan damar ba abu bane da za'ayi watsi dashi ko kuma ayi masa gurguwan fahimta, kuma abinda ya birgeni da kaga ina kallon ka daɗi ne haɗe da murnar nima kauyen da nake zai samu cigaba ta dalilin ɗan cikina da kuma abokinsa, bazan musalta irin farin cikin da nake ciki ba saboda jin wannan bayanan daga bakin ɗana kuma koda kaga na ɗauki littafi ina kara nazarin wani wasiƙar da ciyam ɗin gundumar nan ya aiko min da larabci ne, ko dana duba wasiƙar banga inda yace zaisa amin makarantar boko a kauyen nan ba ko kuma makamancin wani abun cigaba a cikin kauyen Jaada ba toh wannan abin shine ya ɓata min rai, sannan kai kuma in zanyi magana saika katse ni shine abinda ya kuma ɓata min rai amma tun farkon bayanin ka nayi na'am da zancen ka dama duk abinda zakazo min dashi Baba na"
Saboda murna Umar ma kasa magana yayi sai daya nutsu murnar tabi jikinsa sannan yace
YOU ARE READING
BAYAN WUYA (On Hold)
Tarihi Kurgu"Inna Hajjo don Allah karki kashe ni wallahi ba laifina bane duwatsun ne sukaƙi kamawa kuma kince kar insa makamashi, don girman Adda Aisha karki duke ni na tuba Inna bazan ƙaraba wayyo Allah" Tana maganar tare da kare duk inda Inna Hajjo tak...