BAYAN WUYA
© ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION
® Basira Sabo Nadabo
Bismillahir-Rahmanir-Rahim
12•
"Lafiyarka ɗaya kuwa ɗan uwa me yasa kayi wannan ajiyar zuciyar?"
"Lafiya lau Umar sai dai ina tuna wani abune daya faru jiya a gida nima sai ɗazu Lukuman yake lamunta min"
Fuskarshi cike da tausayi, Ya Umari yayi saurin cewa"Me yafaru har haka ni banda labari?"
Kallon Umar ya karayi sannan ya girgiza kai haɗe da cewa"Akan wannan maganar karatun boko ne shine Ahmad da Sunusi sukace su zasuyi karatun shikenan fa ta'inda Aliyu yake shiga bata nan yake fita ba, har wani ikirarin raba Ahmad da duniya yakeyi kuma yayiwa kanshi alkawarin ɗaukan rayuwar Ahmad, wallahi tunda naji wannan maganar hankalina yake tashe saboda bamu san abinda zai faru ba nan gaba" Duk suka ɗauki salati
"Yanzu ina suke?" cewar Hashimu
"Wallahi dani da Lukuman ɗin babu wanda yasan inda suke domin Inna Hajjo tace ta yafesu a cikin ƴaƴanta, wai tabawa Inna Ƙariba su sannan shi kuma Ali be daina faɗin sai yayi ajalin Ahmad kuma shine sanadin ɗaukan rayuwar Ahmad, toh wannan shine ya fusata Ahmad da Sunusi sukabar ɗakin ba tare dasun ƙara waiwayar ɗakin ba kuma har yanzu da nake baku labari babu wanda yasan inda suke" Ya karashe maganar cike da rauni
"Tabbas Aliyu yayi kuskuren furta wannan kalmar kuma aradun Allah inhar Aliyu yayi sanadiyar mutuwar Ahmad, ni kuma sai nayi sanadin rabashi da farin cikin rayuwa dama duk abin jindaɗi nima alkawari na ɗauka" Da zafin zuciya yayi maganar
"Haba kai kuwa haba Umar ina ruwanka dasa baki a cikin wannan maganar kuma koma menene nina tabbata Aliyu bazai taɓa aikata abinda yafaɗa ba, sai dai kawai ya faɗa hakanne don yana cikin ɓacin rai amma banji daɗin abinda kaima kafaɗa yanzu ba gaskiya bai dace ba kwata-kwata"
Nan Hashimu yayita yiwa Ya Umari faɗa akan mugun furucin daya furta kuma yana guje mishi abinda zaije ya dawo haka suka cigaba da hira har Hashimu yayi musu sallamar komawa birni, suma suka dawo gida Ya Umari ya wuce ɗakin su yayin da Marzooq ya faki idanun mutanen gidan yayi saurin faɗawa ɗakin Inna Hajjo, don har sai data razana ta ɗago kai haɗe da cewa"Haba ɗan birni meye amfanin hakan kafaɗo min ɗaki babu sallama balle kajira ince kashigo, inda kafaɗo ina mummunar yanayi fa ai daka gama dani aradu" Da gefen ido ya harare ta haɗe da cewa
"Meye zan gani anan harda zai ɗaga min hankali ko kuma ya dame ni, abu kamar slippers"
Yaja tsaki duk a zuciyar shi yayi maganar a fili kuwa cewa yayi"Haba Inna Hajjo kinfi kowa sanin yadda nake da ƴaƴan ɗakin waccen munafukar kuma kin sani ɓoye jiki nakeyi inzo gare ki saboda halacci da karamci irin naki"
Da hararen gefen ido ya karashe maganar, ita kuwa Inna Hajjo dajin anya beta sai washe dafaffun hakwaranta takeyi sannan tace"Kai dai bari kawai ɗan birni ni kaina nasan nafi waccen baƙar munafukar kyau da kyan diri kuma ko a gurin Malam nasan nafita mukami a zuciyar shi, yanzu dai nasan dole akwai abinda ka kuntso da kake rawar bakin kakkaɓarsa" Itama hararar tayi masa, dariya yayi haɗe da cewa
"Yanzu Inna Hajjo da ranki da lafiyarki kika bari wannan maganar tafita har kunnen maƙiyan ki wanda basa son cigabanki da kuma na ƴaƴanki" Ya karashe maganar da riƙe haɓa na jimami, kusa da Marzooq ta dawo ta ɗaura hannunta kan cinyar Marzooq sannan tace
"Bani nasha ɗan birni me kajiyo a kaina da kuma ƴaƴana?"
"A bakin uban ƴan zuciya da zafin rai naji wai Aliyu yayi alkawarin ɗaukan ran Ahmad kuma kema kince kin yafesu kuma kin bawa Ƙariba ƴaƴanki kyauta, sannan abinda yafi ɗaga min hankali ya dagula min lissafi shine Umar shima yayi alkawarin ɗaukan rayuwan Ali muddun ya ɗauki na Ahmad, ni kuma ganin yadda nake dake yasa nayi saurin zuwa gareki don kiyiwa tufkar hanci kinde san yadda Umar yake da zuciya sannan kuma Aliyu shine sanyin idonki, shine dai kamar kinyi kaki don kama kinga ai bazanso a kashe miki shiba" Wani dogon salati taja haɗe da tattafa hannaye cike da mamaki
"Yanzu wani munafiki ɗan shegiyar ne ya faɗawa Umari wannan maganar? Waima wani ɗan iskan ne yafitar da wannan maganar? Oh ni Hajjo wai yaushe zan dinga sirri a ɗakina ne kuma ya zauna a cikin ɗakin ba tare da wani shegen ya fitar da maganar ba?, lallai zanyi saurinyiwa tufkar hanci amma kai ɗan birni a ina kagano min Ahamad da Sunusi?" Mamaki fal kwance akan fuskanta
"Waye yasan inda suke tunda kema da kika haifesu kin koresu ni aina zan gansu? Ai kece zaki fita ki nemo su amma bani ba, wallahi Hajjo kema wani lokacin bana gane kanki ke uwa ce ko kuma mai rainon ƴaƴa"
"Kirani da kowanne amma zanyi maganin Umari ba dai dani yakeyi ba zan ganar dashi mugun maɗaci" Da baƙin ciki tayi maganar
"Me kuma zakiyi mishi Hajjo?"
"Kaidai ka tsaya kagani kuma da hannun ka nake son kabashi duk abinda zanyi masa tunda naga kuna shiri sosai"
Tunda asuba take aiki ɗaya ga sanyi gashi babu kayan kirki a jikinta sai kaɗuwar sanyi takeyi hakwaranta sai haɗuwa yakeyi da ɗan uwan sa, amma haka baiwar Allahn nan take wanke kayan Aishatu dana Aliyu sannan da ruwan randa Inna Hajjo ta bata umurnin amfani dashi, hannayenta duk sun ƙandare saboda sanyi ko wanke kayan da kyau batayi gashi Inna Hajjo tayi mata gargaɗin kafin su tashi a baccin safe take son ganin kayan akan katanga, Imam ne ya shigo gida dai-dai lokacin Inna Wuro ta fashe da kuka cikin kukan take cewa"Wayyo Allah na wayyo rayuwata ni yaushe zanji daɗi kamar sauran yara? Yaushe ne nima zan ɗanɗani gatan da sauran yara kamar ni suke ɗanɗana? Anya ni ƴar gidan nan ne kamar yadda Inna ta take faɗa min, kodai maganar Inna Hajjo ne gaskiya muba ƴaƴan Imam bane shiyasa Imam yana kallon abinda ake mana bai taɓa magana ba, shikenan ni a haka zan ƙarasa rayuwata babu ranar da zanji daɗi kamar kowa, Inna ta cikin ƙangin wahalar rayuwa nima gani a ciki sai yaushe ne zamuji daɗin rayuwa mu rabu da muzgunawar matar uba?"
Haka tacigaba da faɗin abinda yake ranta sai dai bata san duk abinda take faɗa a kunnen Imam bane shi kanshi Imam maganganun Inna Wuro ya daki zuciyar shi har sai daya dafa ƙahon zuciyar shi saboda zafin da yaji"Dole in nunawa ƴaƴana gata ko zan samu rahamar Allah Inna Wuro daga yau kinbar yin kukan rashin gata, aurar dake zanyi kema kije kiji daɗin rayuwa kamar kowa amma bakomai BAYAN WUYA sai daɗi da sannu zakuji daɗin da kuke ganin yayi muku nisa Inna Wuro"
Harya shiga ɗaki Inna Wuro bataji wucewar shiba tana gama wankin kayan tahau hura wuta gashi raɓa duk ya sauka akan iccen, yaki kamawa kuma babu makamashin da zata hura dashi hannun ta har rawa yakeyi saboda yadda gari yayi haske gashi duwatsun hura wutan suki kamawa, daga bayanta taji an doko salati da sauri ta juya tare da buɗe ido cikin razana.......ƳAR NADABO

YOU ARE READING
BAYAN WUYA (On Hold)
Fiksi Sejarah"Inna Hajjo don Allah karki kashe ni wallahi ba laifina bane duwatsun ne sukaƙi kamawa kuma kince kar insa makamashi, don girman Adda Aisha karki duke ni na tuba Inna bazan ƙaraba wayyo Allah" Tana maganar tare da kare duk inda Inna Hajjo tak...