Page 2•

138 6 1
                                    

BAYAN WUYA

© ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION

® Basira Sabo Nadabo

Bismillahir-Rahmanir-Rahim

2•

Ɗauke shi da mari akayi wanda sanadiyyar wannan marin har saida bakin shi ya garwaye da jini, dafe gurin marin yayi idonshi yana zubar da kwalla yace

"Ya Usmanu me nayi maka harda zaka mare ni?"
       A zuciye Ya Usmanu yace

"Haruna bar ganin anayi maka uzurin yaranta toh bazan laminci rashin kunyar da kake mana a cikin gidan nan ba don kawai kana karamin yaro kum...."

"Usmanu!" Inna Ƙariba ta kirashi da rawan murya ta cigaba da cewa "Usmanu agaban idona kake dukan ɗana saboda yayi rashin hankali tarbiyyar da kullun nake muku kenan Usmanu?"
    Usmanu yayi saurin zuwa gaban Inna Ƙariba ya durkusa ya sunkuyar da kai kunya duk ya lulluɓe shi amma duk da haka bai bar saukar da zuciya ba, ajiyar zuciyar da yakeyi duk wanda yake ɗakin yanajin saukar zuciyarsa yace

"Inna kiyiwa girman Allah da Manzonsa kiyi min rai na tuba nabi Allah kuma nayi miki alkawari bazan sake kwatanta irin wannan aiki da zuciya ba, Inna kiyi hakuri aradu ban sakewa"
     Inna Ƙariba shafa kanshi tayi sannan ta kalla Haruna da yake tsaye yana kuka tace

"Zonan mai sunan margayi"
        _sunan da take kiranshi dashi kenan saboda a ranar data haifi Haruna a ranar kanin uwar mijinta wato Fa'iza ya rasu da ranar suna ya zagayo sai akayi masa madadi da sunan wannan dalilin ne yasa Inna Ƙariba take masa alkunya da mai sunan margayi kuma kusan duk Filanin asali ansan shi da kunya kuma duk taurin kai irin na Haruna ya tsoron fushin Inna Ƙariba don intayi fushi saukowarta ba abu bane mai saukibane, shiyasa wasu kance Umar da Usmanu zuciyarta suka ɗauko. Wannan kenan_

Zuwa yayi gabanta ya durkusa yana kuka yace
     "Inna kimin aikin gafara natuba nabi Allah da Manzonsa nabiki Inna"

"Mai sunan margayi ka kyauta tun ƙasa bai rufe idona ba ka nuna min kaima ka isa ina ga kuma bana raye halayyar da zaka dinga yiwa yayyinka kenan ko? Rashin kunyar ya tsallake Usmanu ya koma kan Umaru bama Umaru ba har kan Yabbanku ko mai sunan margayi? Ka kyauta Allah ya shirye ka"
  
"Inna don Allah kiyi hakuri karkiyi fushi dashi in kikayi fushi dashi tamkar damu duka ƴaƴanki kikayi fushi dasu don Allah Inna kiyi hakuri"
     Cewar Jamilu da tunda suka zauna gaban Innan su sai yanzu yayi magana, Shamsuddeen ne yayi caraf yace

"E Inna kiyi hakuri abinda Ya Jamilu ya faɗa gaskiya ne domin ba iyakan Haruna fushin zai sauka ba har damu sauran ƴaƴanki muma Allah zayyi fushi damu, don Allah Inna kiyi hakuri da halin Haruna"
      Abubakar da Inna Wuro ne suka rarrafo zuwa gaban Inna sukace

"Innan mu kiyi hakuri don Allah kuma kinga kece kike cewa mu dinga hakuri da junan mu kuma duk mai hakuri bazai taɓa taɓewa ba"
       Inna Wuro tace

"Shiyasa duk abinda akemin cikin gidan nan bana cewa komai Inna kuma kina kallo duk yawan gidan nan nice mai dafa musu abinci kullun kuma na wanke kwanukan da sukaci abinci, sannan Inna kina kallo nice nake wanke kayan Ya Ishaku dana Ya Aliyu da Ya Lukmanu Ya Ahmad da Ya Sunusi ne kaɗai basa bani kayansu nake wankewa kuma ban taɓa jin nagaji ba saboda kina ƙarfafa min gwiwa da irin wahalhalun da Sahabban Annabi (SAW) suka sha amma daga karshe sunji daɗi" tayi saurin share hawayen da suka gangaro mata ta cigaba da cewa
     "Inna duba hannaye na duk sunyi ja sunyi ciwo saboda wanki da wahalar da nake sha Inna ina fatan watarana nima na tsinci ribar hakurin da nakeyi a gaba kamar yadda kike yawan faɗan mana, Inna don Allah kiyi hakuri da duk halin da Ya Haruna yakeyi nasan watarana shima zai gane cewa abinda yakeyi ba dai-dai bane kinji"
     Tunda Inna Wuro ta amshi maganar Inna dama sauran yayyinta jikinsu yayi sanyi domin sun san kalan wahalar da take sha a gidan kuma babu halin magana domin Inna tace bata yafewa duk wanda yasa baki a cikin lamuran gidan ba inhar ya shafi ɗakin Inna Hajjo, share hawayen tayi sannan tace

BAYAN WUYA (On Hold)Where stories live. Discover now