BAYAN WUYA
© ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION
® Basira Sabo Nadabo
Bismillahir-Rahmanir-Rahim
13•
Bakin tane yahau rawa tana yarfar da hannu cikin tsoro tace
"Inna Hajjo don Allah kiyi min rai wallahi ba laifina bane duwatsun ne sukaƙi kamawa, don Allah Inna Hajjo karki buge ni"
Ita kuwa Inna Hajjo sai huro hanci takeyi tayiwa Inna Wuro kuri da ido wai gawar da zatayi tayi ido huɗu da wani murɗaɗɗan ko-kara, kamar kiftawar ido kawai Inna Wuro taji saukan duka a tsakiyar kanta, har saida goshinta ya fashe yana fidda jini wani gigitaccen ihu ta sake duk saida mutanen gidan suka farka daga bacci kaman haɗin baki gaba ɗaya suka fito a lokaci ɗaya, ita kuwa Inna Hajjo tana tsaye kanta sai jibganta takeyi kaman an aiko ta da gudu Umar ya nufi inda suke don ganin rashin motsin da Inna Wuro takeyi ne, a zuciye ya hankaɗe Inna Hajjo gefe ya ɗauki Inna Wuro sai ɗakin Imam yana zuwa ya kwantar da ita a gaban Imam haɗe da durkusawa yana kuka mai cin rai, ita kuwa baiwar Allah Inna Wuro har yanzu tana sume domin ko yatsar hannun ta baya motsi ga bugun zuciyarta yana sauka da sauri, ganin kuka bashi bane mafita kuma har yanzu Imam bece dashi komai ba yasa yayi saurin fita waje ya ɗibo ruwa mai sanyi a randa yana zuwa ya sheƙa mata, amma duk da haka bata farka ba wani ruwan ya kuma ɗibowa ya sheƙa mata har yanzu dai tana nan yadda take bai damu da jiƙa Imam da yakeyi ba shidai kawai Inna Wuro ta dawo hayyacin ta, wannan karan tulu ya ɗauko cike da ruwa yana fara zuba mata tayi ajiyar zuciya kana cikin razana da firgici tace"Inna Hajjo don Allah karki kashe ni wallahi ba laifi na bane duwatsun ne sukaƙi kamawa kuma kince kar insa makamashi, don girman Adda Aisha karki duke ni na tuba Inna bazan ƙaraba wayyo Allah na"
Tana maganar tare da kare duk inda Inna Hajjo take dukanta musamman kanta Ya Umari ne ya tallabo ta haɗe da jingina ta a jikin shi, shima kukan yakeyi ɗago jajayen idanun shi yayi ya kalla Imam da shima idon shi duk sun rune sau canja launi, sunkuyar da kanshi yayi haɗe da cewa"Kabani izinin ramawa Inna Wuro dukan da aka mata" cikin kuka yayi maganar
"Bazan baka izini ka duki matata ba kuma ban yafe maka ba idan har kayi mata kallon banza" yayi maganar cikin ƙunar rai
"Lallai ya tabbata bakai bane mahaifin mu kuma naƙara yadda da maganar da matarka take faɗa a kanmu muba ƴaƴan sunna bane sannan Imam bashi bane mahaifin mu" a zucciye yayi magana
"Umar ƙarna ƙara jin wannan mummunar kalmar tafito daga bakin ka" wannan karon gargaɗi yayi masa
"Torh ya zama dole kanunawa duniya kaine mahaifin mu kuma mu ƴaƴan sunna ne kuma ka gargaɗi matarka karta ƙarasa hannu ta duki kanwata daga ita har ƴaƴanta" babu tsoro ko shakka a zuciyar shi
"Umar idanka ƙara magana akan matata zan mugun saɓa maka"
"Torh yazama dole inje in nemo mahaifina koda kuwa rigarsa ne Imam tun muna yara kake nuna ko in kula akan Innar mu, yanzu kuma abin ya koma kan Inna Wuro wacce taci sunar mahaifiyar ka amma baka taɓa ɗaga ido ka tsawatar akan abinda ake mata ba, torh wallahi yanzu an kureni naji niba ɗan gidan bane amma kasani daga rana irinta yau bazaka ƙara sakani ko Inna Wuro a idonka ba kuma wallahi bazaka ƙara gan........"
Saukan marin da yaji ne ya hanashi ƙarasa abinda yayi niyyar faɗa dafe kuncin sa yayi haɗe da juyowa ya kalli wanda ya mare shi, Inna Ƙariba ce durkushe tana kuka maicin rai ƙoƙarin kamata yayi amma ta goce saboda ganin yadda take layi shima wani kukan ya kuma fashewa dashi Inna Wuro ma kukan takeyi, cikin kuka tace"Don Allah kayi shuru Umar!"
Duk cikin kuka take magana shima Umar cikin kuka yace"Inna ina neman gafarar ki amma wannan karan bazan taɓa shuru a cigaba da muzguna mana ba kullun da kuka kike tashi a bacci kuma da kukan kike bacci, amma kice nayi shuru Inna dole yau asan abinyi kodai Imam yafaɗa da bakin shi muba ƴaƴan shi bane ko dai kuma ya sake ki domin kafata kafarki zabu bar gidan nan, bazaki ƙara zama a gidan da ake birne ki da sauran rayuwar ki b......"
Wani marin ta ƙara zuba mishi sannan cikin ƙaraji tace"Kayi shuru! kayi shuru!! Nace Umar ashe bazaka taimaka musu gurin birne niba Umar ashe ban isa ince kayi shuru kayi ba Umar? Shikenan tunda su basu kashe ni ba wannan baƙar zuciyar taka shine zai zama silar rayuwata"
Duk abinda suke faɗa Imam yana zaune baice dasu uffan ba kuma bai hana Inna Ƙariba kuka ba kamar yadda ya saba, sai dai ƙasan zuciyar shi yana jin raɗaɗi da ƙunar abinda ya hanashi hanata kuka sannan wani ɓarin zuciyar shi yana ingiza shi da yayi mata sakin da ɗanta yake nema.....
A bangaren Inna Hajjo kuwa sai murna takeyi domin abinda take bukata kenan kuma har yanzu bataji Imam yace komai ba akan kukan da Inna Ƙariba takeyi, sai dai wani zuciyar ta tana gargaɗinta dakarta bar Inna Wuro tabi su saboda aiyukan gida amma inhar tabar Inna Wuro torh tabbas Inna Ƙariba ma zata zauna a gidan wanda kuma hakan bazata taɓa barin hakan ya faru bane, suma su Ya Usman suna kofar ɗakin Imam kuma duk abinda yake faruwa sunaji su kansu suna mamakin canjin da Imam yayi"Yau ga Innan mu durkushe a gaban Imam tana neman taimakon shi amma ya kasayin komai kuma dole yau yayi komai koda kuwa hakan shine zaisa ya tsine mana, wallahi bazamu zuba ido a cigaba dayin irin wannan ɗanyen aikin ba"
Cewar Bakaam cikin ƙunar zucci"Bazan taɓa hanaku abinda kuke so ba amma kusani gaba ɗayan ku bazan taɓa sakin matata ba sai dai kuma bazan taɓa zuba muku ido kuyi duk abinda kuke so ba, idan har kuna ganin fita neman mahaifinku shine a gaban ku na baku dama daga nan har binnin sin kuma bazan taɓa gushewa dasa muku albarka ba, amma kusani ni Imam bazan laminci wulakanta matata ko kuma ƴaƴana ba don haka duk me shirin fita duniya kofa a buɗe take daga kan Ƙariba har Inna Wuro ban hana kowa fita duniya ba kuje Allah yana tare daku"
Yana kaiwa nan yafi waje, Inna kuwa kukanta ne ya tsananta shekewar data farayi ne Umar yayi saurin sakin Inna Wuro yayi kan Inna Ƙariba, amma ina kafin ya isa inda take harta faɗi jini yana fita a bakinta ihun da yayi ne ya jawo hankalin sauran yaran suma suna ganin abinda ya faru duk suka rikice da kuka gashi jinin bai daina fitowa ba, Imam yana jin ihun su amma ko jiyowa da baya bayyi ba balle yaga abinda yake faruwa haka yasa kai yabar gidan yana fita yayi majilisar da masu ɗaukan karatun shi suke zama, suna ganin shi suka miƙe suna gaishe shi shima da dakin fuska ya amsa musu sannan yayi gyaren murya haɗe da cewa"Acikin ku waye yake da ra'ayin auren ƴata Inna Wuro?"
Duk sukayi shuru suna kallon shi, gyaran murya ya kumayi sannan yace"Acikin ku waye yake da ra'ayin auren ƴata Inna Wuro?"
Kallon juna suka farayi kana dattijon cikin su yace"Haba Imam yada girman ka kuma ka dubi tsufar mu ka kawo mana tallar ƴarka wacce batafi muyi jakanya da itaba amma mune kake cewa mu aure ta, nidai kam bazan iya auren taba amma ban sani ba ko sauran ƴan uwana zasu iya auren ta"
Yana kaiwa nan ya tashi a gurin zuciyar shi cike da tausayin Inna Wuro,"Aisha ya kamata kayi tallan aurar da ita amma ba kamilalliyar mace ba nasan kana sane da abinda takeyi a cikin garin nan amma baka taɓa cewa komai ba, sai wannan adilar zaka aurar da ita a wukance ba" cewar wani dattijo shiko ɗayan cewa yayi
"Shiyasa akace ku aurar da ƴaƴan ku tuntuni kuka ƙi wai saita ƙara hankali, ai ga hankalin ta ƙara amma kuma ya zame maka masifa kila ma abin kunya ta ɗauko shine gudun ɓacin suna kake son aurar da ita, torh nikam badani za'ayi irin wannan abin kunyar ba"
Haka Imam ya ƙarashi yawon neman mawa Inna Wuro mijin aure amma duk wanda akayi masa tayin ta sai yace abin kunya tayi ake son liƙa masa ita, da dai yaga abin ƙara ɓata masa suna yakeyi gashi ranshi ya fara ɓaci duk girma da mutuncin sa amma mutanen kauyen nan suke yaɓa mishi magana da bakin ciki ya koma gida, yana shiga gidan abinda ya gani yayi mugun razanar dashi haka ya tsaya a daskare a inda yake kamar an shuka shi........Hmmmmm Anya kuwa amma dai nayi shuru readers ne kaɗai zasuce komai
ƳAR NADABO

YOU ARE READING
BAYAN WUYA (On Hold)
Historical Fiction"Inna Hajjo don Allah karki kashe ni wallahi ba laifina bane duwatsun ne sukaƙi kamawa kuma kince kar insa makamashi, don girman Adda Aisha karki duke ni na tuba Inna bazan ƙaraba wayyo Allah" Tana maganar tare da kare duk inda Inna Hajjo tak...