BAYAN WUYA
© ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION
® Basira Sabo Nadabo
Bismillahir-Rahmanir-Rahim
Ya Aishan mu Mom Innata da mutumin kirki wannan shafin naki ne don ke baki da halin Aishan Inna Hajjo wallah halinki na kwarai ne, domin uwa tagari ce ta haife mu kuma uwa tagari ce ta raine mu, Allahu ya jikan Innan mu yasa mutuwa hutuce a gare su damu baki ɗaya. Amin
5•
"Haba Inna abinda ake mana a gidan nan yayi yawa kuma gaskiya hakurin da mukeyi yanayin yawa, ki duba fa kece kawai akewa wannan rashin mutuncin a kauyen nan kuma duk ƴan kauyen nan sun sanan da haka, meya Inna bazaki bamu damar rama miki abinda ake miki ba?" cewar Shamsuddeen
"Saboda haɗin kanku nake so bana son tashin hankali a tsakanin ku da ƴan uwan ku, gaba ɗayan ku ina kara tunatar daku girma da mahimmancin zumunci a tsakanin ku kuma duk wanda a cikin ku ya yanke zumunci da ɗan uwansa Allah ya isa ban yafe masa ba, sannan gaba ɗayan ku a abu ɗaya nake ganin ku daku da ƴan ɗakin Adda Hajjo babu wani banbanci a tattare daku domin ciki ɗaya kuka fito, Umar da Usman ina kiranku da kuyi hakuri da ƴan uwanku kuma ina rokon ku da sunayen Allah tsarkaka da kuyi hakuri da ƴan uwanku dama duk abinda zasu muku, nasani suna tsokanar ku toh wannan kau da kan da kukeyi nake son ku karayi akan wanda kukeyi kar naji ko kuma nagani ɗaya daga cikin ku zai biye musu, nasan da sannu suma zasu gane abinda sukeyi ba dai-dai bane ko kun manta abinda Ɗan Gatan Allah yace ne? Cewa fa yayi ita fitina tana kwance ne kuma Allah ya tsinewa mai tada ta, toh kun gani kuma ni ko fushi bana so Allah yayi daku balle harya tsine muku"
Ta kalle su gaba ɗaya kowannen su ya durkusar da kai kasa cikin ladabi da nutsuwa murmushi tayi sannan ta kallah Abubakar tace"Abubakar Saddiƙu, Atiku masoyin Annabi wanda ya fara sadaukar da dukiyar shi da rayuwar shi don kawai Annabi (SAW) ya rayu, matso kusa dani masoyina"
Abubakar ya rarrafo zuwa gurinta yana murmushi don a duniya wannan kirarin da Inna Ƙariba take masa shi ke faranta masa rai har yaji inama yana da abu yayi sadaka dashi, dafa kanshi tayi murmushi ɗauke akan fuskanta tace"Nasan kai me hakuri ne akan komai kuma kai me sanyin haline wannan dalilin yasa nake sonka da dukkan rayuwana Abubakari na"
Umar dake murmushi ta kallah shi da Usmanu suma sun san inhar Innan su tana cikin farin ciki toh wannan kirarin take musu, Umar ne ya rarrafo zuwa gareta don yasan shine nagaba kanshi ta shafa haɗe da cewa"Kaga wanda ya sadaukar da karfi da lafiyar shi domin kare lafiyan Manzon Allah (S.A.W), kaga wanda Annabi yake sirri dashi sannun wanda kafirai ke tsoro kaga wanda shaiɗan yake tsoron haɗa hanya dashi, sannu Faruk ɗina Allah shine zai yi maku albarka kuma ina rokon Allah yasa kayi hali irin halin Sayyadina Umar (A.S)"
Ta juya gefen da Usman ke zaune ta kalle shi shima kallonta yakeyi yana dariya tace"Mai dukiya wanda ya gaji arziki kaine wanda ya sadaukar da dukiyarsa ga ba ɗaya don ɗaukaka kalmar Allah, kaga Usman ɗan Affan wanda ya bada dukiyar shi da lafiyan shi domin taimakawa Manzon Allah (SAW), ina rokon alfarmar Allah daya baka zuciya irin na Usman"
"Matso kusa dani Haruna na kaga masoyin Allah mai biyayya da kalmomin Allah sannu kanin Annabi Musa kalamullah, ina rokon Allah ya baka zuciya irin na Harun ɗana Haruna"
Shima sai murmushi yakeyi yana jin daɗin kirarin da Innar tasu take musu, Jamilu da Shamsuddeen ta kalla tace"Sannun ku hadiman addini sannun ku bayin Allah na kwarai sannanu ku manyan malaman musulunci, kaga Jamilu na kyakkyawa mai kyawun zuciya, sannu Shamsuddeen bawa ga addinin musulunci, ina roko haɗe da alfarmar Allah akan ya baku zuciyoyin waɗannan bayi nasa"
Inna Wuro ta kalla tayi murmushi haɗe da cewa

YOU ARE READING
BAYAN WUYA (On Hold)
Historical Fiction"Inna Hajjo don Allah karki kashe ni wallahi ba laifina bane duwatsun ne sukaƙi kamawa kuma kince kar insa makamashi, don girman Adda Aisha karki duke ni na tuba Inna bazan ƙaraba wayyo Allah" Tana maganar tare da kare duk inda Inna Hajjo tak...