BAYAN WUYA
© ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION
® Basira Sabo Nadabo
Bismillahir-Rahmanir-Rahim
11•
Aliyu sai huci yakeyi kamar kubuwa ya juya ya fiskanci Inna Hajjo ya nunata da yatsa hane da cewa
"Duk laifinki ne Inna yau da tuntuni dana farkar dake da sabbin ɗabi'un da Ahmad da Sunusi suka ɓillo dashi cemin kikayi kina sane dasu, yanzu me shurun naki yaja mana in banda baƙin ciki kuma wallahi Inna sai nayi sanadin raba Ahmad da numfashin sa, koda kuwa nima za'a rabani da nawa numfashin bazan taɓa barin Ahmad yayi abinda yake so ba har yaje ya haɗa kai da ƴaƴan Ƙariba"
"Ali gadanga ƙusan yaƙi waye yace ba kai ba ɗan Hajjo lallai kacika jini na kuma na ƙara yadda jini na ne yake shawagi a cikin jikinka, amma maganar zama ajalin Ahmad kabar maganar kawai domin tsira da mutuncin ku gaba ɗaya kuma tunda har kace bazakayi karatun arnarci ba ai shikenan su da sukace zasuyi sai mubar su suyi abinda zasuyi, amma kusani na yafe Ahmad da Sunusi a cikin ƴaƴana"
Cewar Inna Hajjo cikin lallashi, Aishatu ce cikin shagwaɓa irinta sangartattun yaran nan tace"Ni wallahi banga abin ɓacin rai ana gurin ba tunda har sunce zasuyi toh ku rabu dasu mana, kuma kema Inna da laifin ki wallahi wai ina ruwanki da rayuwan su tunda rayuwar sune sai a barsu suyi abinda suke so kamar kowa, kai kuma Aliyu har kana wani cewa zaka kashe shi inhar ka kashe min yayyi wallahi kaima zansa a rama musu"
Tsawa ya daka mata amma ko gezau batayi ba balle ta nuna halamun tsoro a tattare da ita, Inna Hajjo ce tace"A'a kaga ta inda zamu samu matsala kenan don bazan lamunta wulakanta Aishatu ba saboda bata shiga tsabgar kowa, don haka kar kowa ya shige mata tsabgoginta"
"Wato Inna kinfi son Aishatu a kanmu muda muke kwato miki haƙƙoƙin ki da aka danne amma kece kike faɗa min haka, ai shikenan gaki ga Aishatu shiyasa take wahalar dake" cewar Aliyu
"Eh ruwan ka da rayuwa ta kaima kaci gaba da rayuwarka nima nayi tawa don haka kowa yayi rayuwarsa" da rashin kunya tayi maganar
"Yanzu Inna kina kallon abinda take min baki ce komai ba" cewar Aliyu cikin zafin rai
"Ai gaskiya ta faɗa kai ɗinne ka fiya samata ido akan yadda take gudanar da rayuwarta, Aishatu kiyi duk abinda kike so babu wanda ya isa ya hanaki ciki kuwa harda Iman" cewar Inna Hajjo
Umari ne zaune a karkashin bishiya shida Marzooq suna hirarra kinsu na samari, Marzooq ne ya kalla Umari haɗe da cewa"Wai nikam Umar meye a tsakanin ku da ƴan ɗakin Inna Hajjo? Kuma abinda yake bani mamaki shine kuna kallom irin aikin bautar da Inna Wuro takeyi duk yawan ku babu wanda ya gwada kwato mata ƴan cinta na ƴa mace, nifa don kar ace niba kowa ba inasa baki a lamuran gidan ku inba haka ba wallahi da tuntuni na dakatar da ita daga wannan ƙangin wahalan"
Fuskan shi kaɗai ya isa ya shaidar ma wanda yake tare dashi kalan tausayin da yakewa Inna Wuro, Ya Umari ne ya kalle shi sannan yace"Marzooq bazaka taɓa gane kuncin rayuwar da nake ciki bane amma da sannu zan sanar da kai komai game da gidan mu, sannan babu ruwan ka a cikin rayuwar Inna Wuro don mutuncin ta nake nema kuma bazan taɓa yafewa wanda yayi sanadiyar zubar kwallan Inna Wuro ba"
Da zafin rai yayi magana"Kayi hakuri nasan irin kunar zuccin da kake ɗanɗana yanzu a zuciyar ka, don nima na fuskanci wannan kaddarar rayuwar amma sai dai nawa ba irin naku bane"
Da ƙunar zuciya ya karasa maganar har saida kwalla ya gangaro masa akan kuncin sa, Ya Umari ne ya kalle shi haɗe da cewa"Kaima kana nufin ka fuskanci kalan azabar rayuwar da muke ciki? Ashe bamu kaɗai bane Allah baya so ada na ɗauka mune kaɗai Allah baya so, amma idan nayi duba da rayuwar Annabi (SAW) sai in lura da babban soyayyar dake tsakanin mu da Allah wannan ne kaɗai yake sanyaya min zuciya"
Da ajiyar zuciya ya ajiye maganar, daga nesa ya hango Hashimu ya nufo inda suke yana zuwa duk sukayi gaisa sannan ya zauna ya kalla Ya Umari haɗe da cewa"Abokina kai kuma daga cewa zaka dawo shine sai dai inta neman ka amma babu kai, yanzu ma Lamido ne yace ya gano min kai zaune nan shiyasa ka ganni"
"Kai dai bari kawai abokina ai abubuwa ne suka shamin kai amma yanzu nagama kuma dama ina da niyyar in natashi gurinka zanzo"
"Toh yanzu me ake ciki Imam ya yarda kuwa?"
Umari ya sauya fuska haɗe da sadda kanshi ƙasa, Hashimu ne yayi saurin cewa"Ni daman nasan za'ayi haka ba dole bane mutanen kauyen nan su yarda da makarantar boko, koda kuwa nasan Imam zai iya yarda amma bai zama dole mabiyansa su yarda ba shikenan bakomai"
Da sanyi jiki ya karashe maganar dariyar da Umar ya fashe dashi ne ya dakatar dashi daga tashin da zayyi, cikin dariya yace"Gaskiya Hashimu kai ɗan ƙasa ne nagari mai kishin ƙasar shi da mutanen da suke ciki, kai dai da wasa nake maka Imam ya yarda kuma kaɗan daga cikin mabiyansa suma sun amince da makarantar harma sunyi alkawarin sanya ƴaƴan su a ciki, nima daga gefena ƴan ɗakin mu suma sunce zasuyi karatun ciki kuwa harda mutuniyarka Inna Wuro"
Murna ne kwance a fuskan shi kuma jin Inna Wuro zata shiga yasa bakinsa ya kasa rufuwa da murna yace"Gaskiya bazan iya musalta irin farin cikin da nake ciki ba musamman da naji Inna Wuro zatayi karatun gaskiya abokina kai daban ne kuma ina kara godiya, yanzu ma daka ganni birni zani goggon muce take nema na akan ɓatan ɗan ogan mijinta kusan kwana asirin kenan ba'a ganshi ba, kuma abinda zai baka mamaki babban soja ne a garin nan domin ƙasa da wajen ƙasar nan suna alfahari dashi, toh shine zanje daga nan kuma sai a zo gina makarantar don gaskiya bazan so a ɓata lokaci ba koda da aji buyu ne za'a fara a hankali sai a karasa"
"Ikon Allah ɓatan ɗan mutun kamar ɓatan ɗan mariƙi gaskiya birnin nan suna da matsala har gwara mutun yayi zaman sa a kauye ya fiye masa wannan ruɗe-ruɗen kashe mutane da ɓatan su, kullun ka buɗe radio abinda ake faɗa kenan" cewar Ya Umari
"Umar ka cigaba da nema mana yara wanda zasu shiga wannan karatun ta zamani musamman matan wannan kauyen tamu, saboda karatun ƴaƴa mata shike maƙogwaron al'umma kuma inhar mace ta samu wannan ilimi na zamani dana muhammadiyya toh ina tabbatar maka da ita da jahilci sunyi hannun riga"
"Shiyasa na dage se Inna Wuro tayi wannan karatun don kwacen ƴan cinta da kanta, amma akwai abinda inna tuna yake tsinkar min da gaba shine Yabba ya ɗauki amanar Inna Wuro ya damka min a hannu kuma duk abinda yafaru da ita dani zaiyi kuka, wallahi Hashimu wannan maganar tana tsani cikin ruɗani kuma narasa dalilin hakan harma wani lokaci nakanji faɗuwar gaba" da rauni ya karashe maganar
"Be kamata ɗan wannan maganar ta ruɗaka ba ko kuma tasakaka cikin tashin hankali saboda babu abinda zai faru da Inna Wuro, sai dai shi Bakaam yayiwa karatun Boko bahaguwar fahimta ne shiyasa amma inna tabbata maka watarana zakuyi alfahari da karatun Inna Wuro, amma dole zaku fuskanci tangarɗa kuma dole tudu da gangaren dake hanya dole shima kuyi hakuri dashi a sannu saku wuce wannan hanyar" cewar Marzooq
"Wannan hakane kuma maganarka gaskiya ce sai dai ban waye kaba kuma ban taɓa ganinka a cikin garin nan namu ba Umar wannan kuma waye shi?, amma kuma kaman nataɓa ganin fuskar nan a wani guri sai dai na manta ko inane"
Yayiwa Marzooq kuri da ido, Marzooq kuma dajin abinda Hashimu ya faɗa saida yaji faɗuwar gaba yayi saurin sunkuyar da kanshi ƙasa, Ya Umari ne yace"Kai dai wallahi Hashimu baka rabuwa da abin dariya yo a inane kaganshi in banda cikin kauyen nan, sannan ai shiba baƙo bane ɗan gida ne shima a gidan mu yake kuma ɗan Imam ne kamar ni"
Ajiyar zuciya Marzooq ya sauke wanda yaja hankalin su gaba ɗaya duk suka jiyo suna kallon shi...ƳAR NADABO

YOU ARE READING
BAYAN WUYA (On Hold)
Historical Fiction"Inna Hajjo don Allah karki kashe ni wallahi ba laifina bane duwatsun ne sukaƙi kamawa kuma kince kar insa makamashi, don girman Adda Aisha karki duke ni na tuba Inna bazan ƙaraba wayyo Allah" Tana maganar tare da kare duk inda Inna Hajjo tak...