BAYAN WUYA
© ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION
® Basira Sabo Nadabo
Bismillahir-Rahmanir-Rahim
7•
Jikinta ne ya fara rawa saboda tsananin tsoron da takeyi durkusawa tayi tana yarfar da hannu amma ko kallonta bayyi ba ya cigaba da zuba mata kokaran nan har sai daya ɓalle kuma ya gaji don kanshi sannan ya barta haɗe da cewa
"Duk ranar da Inna ta tayi magana kika bata amsa wanda zan miki sai yafi wannan kuma inga uban da zai rama miki, shegiya mai siffar karuwai kina tafiya kina yanga wake mai kyau ko? Toh aradu ina gabda lalata wannan fuskar taki mai kama dana uwarki"
Cewar Ya Aliyu cikin zafin rai ya juya yayi tafiyarsa"Kamin dai-dai ɗana kuma kacika ɗa kuma jini na, naji daɗin tare ma ƴar uwarka faɗa da kayi wannan shine ke nuna min jinin Aishatu na yawo a jikin ka kuma uba ɗaya ne ya haife ku, ke kuma ki tashi ki karasa mana ɗumamen da zamuci don Aishatu ta farajin yunwa"
Da sauri ta tashi ta cigaba da aikin da takeyi jikinta duk yayi shatin bulala, Inna Ƙariba ma sai kuka takeyi a ɗaki kuma duk ƴaƴanta suma suna ɗakin su suna jin duk abinda yake faruwa amma saboda biyayya da abinda Innar su tace yasa babu wanda ya fita yace da Aliyu uffan, Umar ne zaune a gaban Imam idanun shi duk sunyi ja zuciyar shi yana mishi zafi sai kuka yakeyi na rashin fitar da Imam ya hanashi, dafa kafaɗun shi Imam yayi haɗe da cewa"Ina sane da duk wani nau'ikan bautan da Inna Wuro takeyi a cikin gidan nan amma Umar ina son kusani gaba ɗayan ku wallahi Allah bazai taɓa barin Inna Wuro ta wulakanta ba, nasan zakuce ina sane da duk abinda ake mata amma bance komai ba Umar Inna Wuro ɗiya ce ga Hajjo saboda irin kawaici namu na filani sannan yau inda Hajjo zata ɗauki wuƙa ta yanka Inna Wuro wallahi bazance mata komai ba don itama ƴarta ce, kuyi hakuri kuma ina ƙara baku hakuri da duk abinda za'ayi muku yanzu da nan gaba nasan duk mai hakuri bazai taɓa taɓewa ba ku cigaba da kai kukan ku gurin Allah kamar yadda nima nake tayaku watarana zai zama tarihi, in babu mutuwa akwai aure wanda yake raba mutun da mutun ya kaishi guri mai nisa inda ma baza'a ganta a mata abinda akeyi yanzu ba, kuma ina sane da halin da Ƙariɓa ƴar albarka take ciki da kau da kai dakai hankali nesa saboda ta haɗa kanku wallahi duk watarana zai zama tarihi kaji ko Baba na"
Umar ya gyaɗa kanshi haɗe da cewa"Naji kuma In Shaa Allahu zamu cigaba da hakurin da kuke ɗaura mu akai kuma In Shaa Allahu bazamu baku kunya ba"
Murmushi Imam yayi saboda yasan Umar bai da wuyar hawa kuma bai da wuyar saukowa, kallon shi ya karayi sannan yace"Jiya da daddare kace min zamuyi magana amma saboda karatun dare ban samu mun zauna da kai ba, yanzu faɗa min meke damun ka kuma ina rokon Allah ya bani ikon warware maka wannan matsalar"
Jikin shine yayi sanyi amma zuciyar shi tana karfafa mishi gwiwar Imam zai amsa bakon zancen da yazo dashi, karfin da zuciyar shi tayi ne yasa shi yin magana cikin karfin hali yace"Imam dama wani bakon lamari ne aka same ni dashi kuma akace na faɗa maka saboda kaine wanda suka dogara dashi bayan Allah da Manzon sa (SAW), amma kuma zuciya ta tana min rauni saboda nasan bazaka iya musu abinda kake so ba tunda kaima bason wannan al'amarin kakeyi ba, shiyasa jikina yayi sanyi zuciya ta tayi rauni haɗe da sakin gwiwar bazaka min abinda nazo dashi ba"
Ya karashe maganar da sanyin murya, shi kanshi Imam tunda yaga Umar haka yasan ba karamin abu bane kallon Umar yayi haɗe da cewa"Umar nima a gurin Allah nake nema nidai kawai na kasance shugaba a wannan kauyen tamu kuma bawai duk nafi ƴan kauyen bane, a'ah babu wanda yafi wani sai wanda ya fishi tsoron Allah kawai dai nine sarki kuma nine babban malami a kauyen nan, kuma hakan bashi zaisa na kasa sauke nauyin dake kaina ba kota gurin cigabar al'umma kota gyaran kauye kaga Umar faɗi bukatar ka kai tsaye inhar naga ya kaucewa addinin musulunci toh kasani bazan yarda da wannan bukatar taka ba"
Wani karfi da karfin zuciya ya samu ta dalilin wannan bayanan na Imam, sadda kansa kasa yayi haɗe da cewa

YOU ARE READING
BAYAN WUYA (On Hold)
Historical Fiction"Inna Hajjo don Allah karki kashe ni wallahi ba laifina bane duwatsun ne sukaƙi kamawa kuma kince kar insa makamashi, don girman Adda Aisha karki duke ni na tuba Inna bazan ƙaraba wayyo Allah" Tana maganar tare da kare duk inda Inna Hajjo tak...