BAYAN WUYA
© ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION
® Basira Sabo Nadabo
Bismillahir-Rahmanir-Rahim
Ya Sadiya Maman Siyama kema ga naki don naga kinfi Jienieh son littafin nan don ita tana ɓan garen Aishatu ɗiyar Inna Hajjo, ke kuma kina son Inna Wuro amma ni kuma gaskiya ban cika son..... No be talk dat one oo Na Ya Sadiya talk am lol
6•
Ajiyar zuciya ya sauke domin shima yana girmama girman zancen don yasan abune mai wuya mutanen kauyen nan su yarda da abinda zaizo dashi, amma ya daure yayi ta maza cikin sanyin jiki yace
"Umar dama nayiwa goggo na magana ne akan buɗe makarantar boko a cikin kauyen nan, kuma ni gaskiya ban san ta yadda zan fara maganar ba a cikin kauyen nan saboda bani da uba, Baba na ya mutu tun ina yaro kuma kaima kasani a gidan ku nakeyin komai Innar ku kuma itace take bani abinci sannan ta ɗaukeni tamkar ɗan data haifa, Umar bani da wanda zan faɗawa wannan maganar sai kai kuma ina son ganin muma kauyen mu ya gyaru yaci gaba kamar yadda sauran kauyukan suma sukaci gaba"
Umar ya daɗe a tsugune yana nazarin bakon al'amarin da Hashimu yazo dashi tabbas yasan wannan al'amarin, da wuya ƴan kauyen nan suyi na'am dashi sai dai ya rigada yayi alkawari kuma dole ne ya cika wannan alkawarin daya ɗauka, sauke gauron numfashi yayi haɗe da cewa"Hashimu kasan yadda kauyen nan yake wannan al'amari ne me girma kuma da wuyan fassarawa Hashimu, amma bakomai akwai Allah tunda har nayi maka alkawarin biya maka bukatun ka toh tabbas zan cika maka wannan alkawarin sannan kasani dole sai munyi hakuri da duk yanayin da zamu fuskanta, Hashimu zanje na samu Imam duk yadda mukayi dashi zan faɗa maka kuma na tabbata zai yarda sannan In Shaa Allahu inhar ya yarda toh na tabbata koda duk ƴan kauyen nan basu yarda ba toh tabbas wasu daga cikin su zasu yarda don haka ka kwantar da halinka"
Saboda murna Hashimu yayi saurin rungumar Umar, haka suka cigaba da hirarrakin su shi dai Shamsuddeen ɗan kallo ya zama domin ko uffan bece ba har suka gama hirar tasu na aminan abokai na hakiƙa.
Inna Wuro ce zaune cikin hunturu duk tayi buɗu-buɗu da kura sai kokarin hura wuta takeyi amma iccen bata kama ba, gashi Inna Hajjo tace kar tasa leda ko wani abinda zai taimaka mata wutar ta kama gashi sanyi yana damun ta, Aisha ce tafito bakinta duk yawun bacci sai miƙa takeyi da sauri ta koma ɗaki saboda sanyin daya doketa ta kwalawa Inna Wuro kira, da gudu tabar aikin da takeyi ta ruga zuwa kiran da Aisha take mata kallon kasa da sama tayi mata haɗe da cewa"Ke don uwarki haka ake amsa kira idan nagaba dake ya kiraki haka zakizo kiyi masa tsaye tuda gashi nima kinzo kin min tsaye a kai kamar wata dodonniyar gona, toh ai saiki hau kaina ki tsaya shine zan san kema kin isa kuma kin cika ishashshi boɗaɗɗiya" da sauri Inna Wuro ta durkusa kan kafarta tace
"Don Allah Adda Aisha kiyi hakuri me kike so nayi miki?"
Jikinta har wani rawa ya keyi saboda tsoro da gudun abinda Inna Hajjo zata mata inhar tafito ta taradda Aisha tana faɗa da sanyin safiyar nan, toh jikinta ne zai faɗa mata kuskuren da tayi har gwara kar wutan ya kama tayi ta wahalar wurawa akan ran Aisha ya ɓaci, kallon kaskanci tayi mata haɗe da cewa"Shegiya mummuna shiyasa ai har yanzu babu karen da yayo sallama cikin gidan nan saboda ni ce ƴar so kuma mai farin jini me kyau da kyan sura, amma kefa dube ki fa dake da namiji baku da banbanci sai dai kila inji tausayin ki ince banbanci kaɗan ne, saboda ke kina amsa sunan mace su sannan kina nan a jinsin mata kuma suma suna nan a jinsin maza wannan dalilin ne kaɗai zaisa naji tausayin ki in kiraki da sunan mace amma kuma kisani a matan ma rakosu ke kikayi, nice kaɗai mace a duk faɗin kauyen nan don ni ce kalar macen da maza suke yayi sannan ni ce hasken dake haskaka gaban goshin ko wani namiji dake amsa sunan shi namiji a kauyen nan namu ta Jaada, ni wallahi na rasa inda kika samo wannan bakin jinin don Imam duk da tsufar shi har yanzu mata suna kawo masa tallar kansu, kuma Innata sai dai bata shiga gidan biki ba a kalla sai ta dawo da kawaye sama da biyar saboda farin jinin dake yawo a jikinta"
Ta karayi mata kallon wulakanci haɗe da cewa"Au nafa manta ashe daga uwa aka samo saboda an tsotsa baƙin nono kinga kuwa dole ayo gadon bakin jini kamar uwani, amma nifa kalleni daga sama har kasa na tsotso farin jini a farar nonon uwata kinga kuwa dole nayi farin jini ina fatan kin gane ko?"
Tayi saurin amsawa da kai, murmushi tayi najin daɗin muzgunawar data mata tace"Shikenan tunda kema kin fahimta halin munafuka kuma annamimiyar uwarki da take yiwa Imam da Innata, yanzu abinda nake so kimin shine ruwa neke so zanyi alwala kuma yanzu nake so"
Inna Wuro tayi saurin juyawa domin ta ɗibo ruwan, Aisha tayi sauri ce mata"Ke dakata a ina zaki ɗibo min ruwan da zanyi alwalan?"
"Cikin randa dama zan ɗibo miki" da sauri tayi maganar
"Au ashe" tayi dariya har tana tafawa sannan tace
"Wato kema so kikeyi ki kashe ni kamar yadda uwarki a kullun take son kashe Inna ta ko? Toh a hir ɗinki kuma ruwan rafi nake so bana randa ba saboda shine zafi daɗin alwalar sannan yanzu nake son ruwan kuma yanzu nace"
Ta karashe maganar da tsawa har saida Inna Wuro ta tsorata, saurin ɗaukan tulu tayi ta nufi rafi ga uban sanyi ko wani ɗan gata yana cikin ɗaki a dukun kune da abin rifa saboda sanyin da ake busawa, hakanan ta nufi rafin babu ko mayafi sai ɗan ɓingil-ɓigil ɗin kaya jikin ta duk ya tamushe kafarta kamar akanta aka sauke hunturun, bakin ta sai haɗuwa yakeyi da ɗan uwan shi saboda karkarwar sanyi da yakeyi ko data isa rafin babu kowa sai wani mutun daga cen nesa yana zaune ya dunkule guri ɗaya tunda tayi mishi kallo sau ɗaya bata kara kai fuskanta inda yake ba, ruwan tayi kokarin ɗiba tanasa kafarta cikin ruwan tayi saurin janyewa saboda sanyi don har gwara ruwan randar ma, ɗiba tayi har zata wuce ta juya gurin wannan mutumin har yanzu yana nan inda yake shima tunda ya kalleta sau ɗaya bai kara kallon inda take ba, tayi saurin barin gurin ta koma gida tun daga kofar gida takejin faɗan Inna Hajjo da hanzari ta shiga gidan saboda tasan mai kwatarta sai Allah, ko gama sauke ruwan batayi ba Inna Hajjo ta janyo ta ruwan duk ya zube mata a jiki amma duk wannan abinda da ake mata bata bar tulun ya faɗi ba domin in ya faɗi shima wani hukunci ne me zaman kanshi, gefen da Aisha take ta kalla haɗe da cewa"Adda Aisha ga ruwan na ɗibo a ina zan sauke?"
Inna Hajjo jin ta kira Aisha tayi saurin sakin Inna Wuro tace"Au ashe Aishatu kika tafi ɗibowa ruwa, eh kam kin kyauta don babu abinda zaisa naga Aishatu cikin wannan uban zanyin da ake busawa, kin kyauta Inna Wuro saboda tunanin ki da hangen nesa yasa watarana nake ɗaga miki kafa in kika min wani wautar"
Ita dai Inna Wuro batace komai ba saima ajiye ruwan da tayi ta koma gurin wura wutan da takeyi, cikin hukuncin Allah tana buga dutsen ya kama tayi kokarin kara masa ƙirare don karya mutu, Aisha ce tayi ihu da yasa Inna Hajjo saurin fitowa a ɗaki tare da faɗin"Aishatu meya same ki keda waye, wani uban da uwar ne ya taɓa min ke da safen nan?" duk a tare take jero mata waɗannan tambayoyin saboda Umar ya gifta ta wurin, itako goganniyar sai wani kuka takeyi ita a dole ga shagwaɓaɓɓiya goge hawayen daya zubo mata haɗe da cewa
"Ni Inna wannan ruwan yayi sanyi kuma duk jikina yana min sanyi bazan iya alwalan da ruwan sanyi ba" da shagwaɓa tayi magana
"Yi hakuri Aishatu na bar alwalan ɗan anjima in gari ya rage sanyin sai kiyi ai babu takura a addinin musulunci kinji ko Aishatu"
"Toh amma Inna Hajjo saboda wannan sanyin ne kika hana adda Aisha taɓa ruwan sanyi, ni kuma a cikin sanyin nake tunda duƙu-duƙu kuma har naje rafi na ɗibo mata ruwan da zatayi alwala don dai tayi sallah, ke kuma Inna kince kar tayi sai anjima kuma gani nayi inhar ya kai anjima toh sai dai ta bautawa rana badai Allah ba saboda a lokacin rana ya fito"
Ba Inna Hajjo ba hatta duk jama'ar dake cikin gidan yau suna cike da al'ajabin martanin da Inna Wuro ta maidawa Inna Hajjo, Inna Ƙariba dai tsoron tane ya ƙara yawa domin tasan babu makawa sai adda Hajjo ta duke ta kuma daman tun fitan Inna Wuro take zaune tausayin ƴarta ya cika mata zuciya har fitarta ɗibo ruwa da dawowarta, yanzu kuma gashi ta maidawa adda Hajjo martani, itama Inna Hajjo jinin jinin kinta ne ya daske shiyasa itama ta daske tana kallon Inna Wuro cikin al'ajabi, Inna Wuro kam tana gama faɗan albarkacin bakinta ta cigaba da aikin da takeyi bata kara juyowa ba sai saukan kokara da taji a jikinta da sauri ta jiyo tana kallon wanda ya duketa ai suna haɗa ido taji wani fitsari yana neman sauko mataƳAR NADABO
YOU ARE READING
BAYAN WUYA (On Hold)
Ficción histórica"Inna Hajjo don Allah karki kashe ni wallahi ba laifina bane duwatsun ne sukaƙi kamawa kuma kince kar insa makamashi, don girman Adda Aisha karki duke ni na tuba Inna bazan ƙaraba wayyo Allah" Tana maganar tare da kare duk inda Inna Hajjo tak...