BAYAN WUYA
© ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION
® Basira Sabo Nadabo
Bismillahir-Rahmanir-Rahim_
10•
Bakaam ne yake huci yace
"Haruna kana neman fin karfin mu don kawai kaga munayi maka shuru saboda muna gudun ɓacin ran Inna ce, inba haka ba da tuntuni ya karya ka tunda kake iskancinka na taɓa saka bakina? Ban taɓa ba saboda baka saka Inna a ciki amma inhar rashin kunyarka zai tashi akan Umar har zuwa kan Inna toh bazan laminta ba, kuma ina gabda ladabtar da kai da duk ɗanyen kan da kake jin kanka dashi don haka saika gyara harshenka akan Inna"
Ba Inna kaɗai ba hatta su Umar buɗe ido sukayi suna mamakin abinda yasa Bakaam buɗe bakin shi yayi magana har yau yayi mari, Inna sun kuyar da kanta tayi ita kanta tana mamakin ɗan nata da magana ma be dame shiba kuma duk abinda Haruna yakeyi baya taɓa ce dashi komai, Usman ne yace"Bakaam kayi hakuri kuma banji daɗin daka biyewa Haruna yau ba saboda dukkan mu nan mun san halin Haruna, sai dai kawai muyi hakuri dashi da duk wani halin da zaizo dashi kuma sannan inhar zamu dinga faɗa a tsakanin mu burin Inna Hajjo zai cika domim burin ta kenan ta raba kanmu kamar yadda take rabamu da ƴaƴan ta"
"Amma Usmanu saimu zuba mishi ido yayita iskancin da yake so don kawai yaga munayi masa shuru, muna masa kallon karamin yaro shiyasa ya samu damar yin duk abinda yake so"
Cewar Bakaam cikin ɓacin rai, Jamilu ne yace"Duk hakuri zamuyi da juna da kuma duk halin da muka tsinci kanmu a ciki, kuma sai muna kai zuciya nesa a tsakanin mu kodan zumuncin da Innan mu"
"Toh wallahi munjaɓata minrufata gite aminɗolarama _bazamu yarda muzuba masa ido muna kallon shiba_" Cewar Bakaam
"Nonnon munmuyata bemo _duk da haka de hakuri zamuyi da juna_"
Cewar Shamsuddeen, duk abinda sukeyi Inna batace dasu komai ba sai dai duk wanda yayi magana ta bishi da ido, Umar ne yayi gyaran murya haɗe da cewa"Nidai don Allah kuyi hakuri ni bama wannan ya kawo ni ba, zuwa nayi don wani magana mai mahimmanci amma maganar baza amsu a gurin kuba sai in kun bani hankalin ku"
"Ya Umar mun baka hankalin mu kuma muna sauraren ka"
Cewar Abubakar, Umari ne yayi murmushi haɗe da cewa"Dama akan maganar makarantar zamani ne nake son nashiga ko kuma zaku iya shiga domin tsira cikin duniya"
Tun daya fara maganar duk suka zuba masa ido suna hango wauta da jahilci irin na Umar, Bakaam ne yace"Umar kana hauka ne, wai yaushe kwakwalwar kanka suka samu matsala bamu sani ba? Wuta kake son ka kaimu da hannun ka don kawai kaga duk abinda kazo dashi muna na'am dashi, shine yanzu ma kazo kajamu zuwa wutan jahannama?"
"Ya Umar Makarantar ƴan wuta zaka kaimu? Bayan karatun da mukayi na addini wanda zai kaimu ga aljanna amma shine kai kake son kaimu ga jahannama, toh nidai babu inda zani kuma koda kayi karatun nidai bazanci kuɗin kaba domin kuɗin ƴan uwata ne" cewar Jamilu
"Ya Umar ni zan bika zuwa makarantar zamanin inhar kaima zaka dama na daɗe ina sha'awar wannan karatun musamman in naga Hashimu ya dawo daga birni, birgeni yakeyi"
"Kai Shamsuddeen kana hauka ne wutan jahannama zaka kai kanka don kawai ganin wani ya shiga? Toh bari kaji babu inda zaka, shi Ya Umar da yaga zai iya ai sai yayita zuwa amma bari kaji kai kam babu inda zaka"
Cewar Jamilu"Ya Umari nima zan bika zuwa makarantar inhar Imam zai yarda nayi toh nima zanyi karatun ko don rage aiyukan gidan nan" cewar Inna Wuro
"Idan har rage aiyukan gida kike so toh kifito da miji muyi miki aure amma inhar don wannan karatun ne kema kike son zuwa toh babu inda zaki, don da ranmu da lafiyar mu bazamu bari a koya miki karuwanci ba aje a lalata miki rayuwa ki jawo mana abin kunya" cewar Bakaam da faɗa yayi maganar

YOU ARE READING
BAYAN WUYA (On Hold)
Ficção Histórica"Inna Hajjo don Allah karki kashe ni wallahi ba laifina bane duwatsun ne sukaƙi kamawa kuma kince kar insa makamashi, don girman Adda Aisha karki duke ni na tuba Inna bazan ƙaraba wayyo Allah" Tana maganar tare da kare duk inda Inna Hajjo tak...