BAYAN WUYA
© ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION
® Basira Sabo Nadabo
Bismillahir-Rahmanir-Rahim
9•
Gyaɗa kanshi yayi haɗe da cewa
"Nagode sosai Baba Allah ya bani ikon biyayya a gare ka duk da nasan muwiyacin abune ka sauke bakon da baka sani ba amma kai naji daɗin tarban daka min, sai naji inama tun asali a wannan kauyen mai karamci aka haifeni don in tashi da mutane masu zumunci da sanin darajan ɗan adam, nagode sosai Baba"
"Bakomai kuma babu godiya a tsakanin domin wannan halin daddatakon Annabi ya gina mu akai, sai dai mune muka watsar da abin har muke ganin musulmi ba ɗan uwan musulmi bane, kai Umar kaishi ɗaki ya kwanta in kuma Ƙariba ta dafa ruwan ɗumi ta bashi yayi wanka kuma ka bashi kaya ya saka kafin aci kasuwa nasa asiyo mashi nashi"
"Toh Imam"
Yayi saurin tashi domin cika umurnin Imam, Inna Wuro kuwa tunda bakon mutumin ya faɗa sunan shi tayi saurin barin gurin don gudun duka, amma duk kauce masa da takeyi sai data amshi rabonta na duka, suna shiga ya ganta zaune ta rakuɓe tana kuka Aliyu kuma yana tsaye a kanta da kokara a hannun shi
"Duk yadda akayi wannan shine Aliyun da yarinyar nan take faɗa"
Ya faɗa a ranshi kallon da Aliyu yake mishi ne yasa yayi saurin ɗauke kanshi a gurin su, Umar tunda ya kalla inda Inna Wuro take bai kara kallon gurin ba ɗakin Inna Ƙariba suka shiga ya gabatar mata da sabon bakon da sukayi kuma ɗan gida cikin girmama ɗan adam tace"Maraba lale ga ɗana yazo sannu da zuwa, sannu ko ɗan nan"
Ya durkusa har kasa yace"Inna ina kwana muntashi lafiya, mun sameku lafiya"
Yayi gaisuwar cikin wayewa kamar daman sun san juna dacen, ita kanta yadda ya sake da ita taji daɗin hakan tace"Lafiya lau ya iyayen naka suke?"
Fuskan shine ya sauya su kansu sun kula da hakan tayi saurin cewa"Ya sunan ɗan nawa?"
"Sunana Marzooq"
Cikin dariya tace"Wai sunan ka da wahalar faɗi yake nidai bazan iya faɗa ba kasan harshen filani sai hakuri"
Dariya shima yayi kana daga bisani Umar ya faɗawa Inna Ƙariba bukatar Iman aiki yayi sa'a akwai don ta ajiyewa Inna Wuro ne, in an gama dukanta tazo tayi wanka dashi
Aisha yarinya ce mara kamun kai da wulakanta rayuwarta da albazarancin kanta, tana da yanga bare in tazo gurin maza lokacin kaɗifirinta yake tashi don canza salon tafiya takeyi, kirjin nan banƙaro shi waje don dole sai ya fito, ƙugun nan kuwa girgizan da yake sha yasa shi sabawa ko normal tafiya takeyi a cikin gida saboda sabon da yayi da kanshi yake girgiza, Aisha irin yaran nan ne marasa kamun kai da bibiyar maza gashi duk in data shiga maza na sonta saboda sakar musu jikinta da takeyi wannan dalilin ne yasa duk faɗin kauyen babu mace mai farin jinin ta, kuma babu me kyaun ta a nata tunanin duk abinda Aisha takeyi da yawan mutanen kauyen nan suna sane dashi sai dai kowa ya zuba mata ido gudun kar'a faɗawa Imam ya kara sumewa, Inna Hajjo bata taɓa ganin laifin Aisha kuma a gurin ta duk abinda Aisha tayi dai-dai ne domin bata laifi me laifin kenan Inna Wuro, Aisha ce zaune da wani saurayi sai gyara rigar jikita takeyi kallon saurayin tayi haɗe da cewa"Saika biyani kuɗina don tafiya zanyi"
Shiko gogan sai wage baki yakeyi kamar gonar auduga yace"Kai Aisha aradu duk matan kauyen nan babu wacce ta kaiki kyawu da iya tafiya kuma wannan farin cikin da kika sani, kinci sa'a zan baki naira dubu ɗaya kuma gobe kizo dai-dai nan gurin kizo ki amshi kayan ado don ki dinga min ado a wannan kyakkyawan fuskar taki"
Dariyar jindaɗi tayi aiko da zata tashi ta kara bankaro kirjin sama haɗe da cewa"Shiyasa nake sonka kuma kana min kyautar girma kuma goben ka ƙara zuwa min da wannan film ɗin nata kallo a wayarka, kuma abinda yasa kaga nake sonka saboda kai kana da waya da film masu kyau a ciki"
"Aisha indai wannan ne baki da matsala indai zaki barni nayi yadda muka ga sukeyi toh kema watarana zan siyo miki waya kuma insa ɗan birni yasa miki film a ciki"
Yayi maganar idon shi akan kirjinta ita kuma da taji maganar waya sai kara juyu takeyi a gaban shi, haka suka cigaba da hirarrakin su irin nasu na wayayyu
Yau satin Marzooq biyu a gidan Imam kuma a ɗan kwanakin da yayi ya fahimci halinda mutanen gidan suke ciki, da aikin bautar da Inna Wuro takeyi dama irin wulakancin da Inna Ƙariba take fuskan ta daga Inna Hajjo har ƴaƴanta, sai dai wani abu guda ɗaya Marzooq ya ɗinke da Inna Hajjo don itace take shirya mishi makircin da yakeyi a cikin gidan kuma da bakin ta take karanta mishi karya da gaskiyan da yake faruwa a cikin gidan yauma kamar kullun Marzooq ɗinne zaune a ɗakin Inna Hajjo suna hira tace"Ai bari kaji bakon Malam ita wannan Ƙaribar munafukar mata ce tun shigowarta duk lamuran Malam suka tsaya hatta ɗan ihsanin da makwaftan kauyukan nan suke mana, amma shi Malam ɗin ya gaza fahimtar hakan saima ni daya ɗauki tsanar duniya ya ɗaura min, shine ni kuma naje gurin boka ya shiga tsakanin ta da Malam shiyasa kaga duk abinda nake mata Malam baya hanani, kuma kasan wani abu bakon Malam?"
Yayi saurin girgiza kai haɗe da cewa"Sai kin faɗa Inna Hajjo"
"Kasan me yasa Aishatu tafi Inna Wuro farin jini?""Dama kyau ai Aishatu wutar kyau ce kuma kyawun ta bakowa bane yake gani saimu masoyanta, sannan da an ganta an ganki don kema ba bayaba indai kyau ne gashi ta iya tafiya gata da iya kwalliya, dole samari dama basu budurwar zuciya su sota domin ita ɗin abar so ce amma kinje kina haɗata da waccen jakar kwakwalwarta babu abinda ya sani sai aikin bauta, aini ba karamin birgeni kikeyi ba da kike bautar da uwar da ƴar kuma ki kwana lafiya Inna Hajjo"
Tunda Marzooq ya fara kuranta Aishatu annurin fuskarta suka bayyana sai murmushi takeyi, guɗa tayi haɗe da cewa"Ai barewa bata taɓa gudu ba ɗanta kuma yazo yana rarrafawa wannan bazai taɓa yuwuwa ba dole abinda nayi shi Aishatu takeyi, kai zanma iyace maka abinda ni nayi a lokacin ƴan matanci na Aishatu batayi kwata a ciki ba, kuma kyawu ai gadon sa tayi gurina don nima ai gurin kyau ba baya bace a lokacin samarin kauyen nan dama makwaftakar mu babu gurin wacce suke zuwa saini Hajjo"
"Amma shine kika ƙare da auren Imam haba amma dai an cuceki Inna Hajjo da ba'a barki kin auri saurayin da kike so ba kuma nasan bazaki rasa attajiran samari ba, da yanzu kina nan kema a birni kin waye yadda kike da kyau ɗin nan inda a birni kike da duk a birnin nan babu maganar wacce akeyi sai naki domin keɗin ta dabance Inna Hajjo"
Matse idonta tafayi haɗe da fyace majina tace"Kai dai bari kawai bakon Malam wanda ya tuna bara baiji daɗin bana ba, a wannan lokacin akwai wani attajirin saurayina daya nuna zai aureni sai Baba na yace ya bawa Malam ni, ba karamin kuka nayi ba kuma shima a birni yake"
Marzooq ya cigaba da fan fata ita kuma sai biye mishi takeyi har zuwa wani lokaci da yaji shigowan su Umar yayi saurin fitowa a ɗakin kaman tsohon munafuki, Ya Usman ne ya lura dashi amma sai bece komai ba saboda yana ankare da shakuwar da Marzooq yayi da Inna Hajjo, ɗakin Inna Ƙariba suka shiga suka taradda Haruna sai kunbure-kunbure yakeyi babu wanda yabi ta kansa don suda suka shigo tare sun san kwanar zancen, Inna Ƙariba ce ta kalle shi haɗe da cewa"Kai kuma da waye Haruna tun ɗazu kashigo ɗakin nan amma bakace dani komai ba, meke damun ka Haruna?"
Ya Shamsuddeen ne yace"Rabu dashi Inna tunda shi yace rashin kunya ne akanshi mu kuma zamu sauke mishi wannan rashin kunyar don babu wanda yaga yana raina na gaba dashi, sai shine mara kunyar cikin mu"
"Haruna ban san yaushe zaka girma ba kullun indai akan Inna Hajjo ce kai baka ganin girman kowa, baka ganin darajan kowa da mutuncin kowa kuma kai baka ganin mu da gashi a kai, koh Haruna?"
Cewar Ya Jamilu, Haruna kara ɓata fuska yayi haɗe da cewa"Nifa gaskiya ana shiga hakkin Inna Hajjo kullun mata bata damuwa daku ama ku kullun cikin zaginta kukeyi tare da ƴaƴanta, bayan kowa ma yana da nashi laifin amma saiku take naku ku hango nasu kuma matan nan tana sonku kune bakwa sonta sannan kuke mata kallon muguwar matar uba, kuma ita a ƴaƴa ta ɗauke ku ba ƴaƴan miji ba harda Innan mu kuke zama kuna zagin ta haba don Allah wannan ai dace b......"
Naushi aka kaiwa bakin shi a take bakin ya fidda jini gefen bakin ya kunbura yayi suntun, ni kaina dana kalla wanda yayi naushin sai da abin ya bani tsoro ƴar baby nokia ta da nake ɗauko muku rahoto ta faɗi kasa battery ɗin ta cire, wayar ta ɗauke dole saina tsaya nayi caji domin cigaba da kawo muku rahotoƳAR NADABO

YOU ARE READING
BAYAN WUYA (On Hold)
Tarihi Kurgu"Inna Hajjo don Allah karki kashe ni wallahi ba laifina bane duwatsun ne sukaƙi kamawa kuma kince kar insa makamashi, don girman Adda Aisha karki duke ni na tuba Inna bazan ƙaraba wayyo Allah" Tana maganar tare da kare duk inda Inna Hajjo tak...