Ya fahad nifa na fiso musa kaya color daya, kawai kayi sky blue shadda, mammie tasai mana laces din dinner kuma ni blue din nafiso ko ya kace hayatie?
Fahad baida wani option duk ta dabaibayeshi.. This girl is silly... Murmushi yayi yace toh habibty sai kuma me?
Yauwa sai inason 50k sababbi sbd liki...
Ido ya zaro yace basma na yayi yawa sai dai 20k sabi kinji durling dina..
Gsky ya fahad a'a, haka zamuyi auren kake min mammako bayan nasan kana da kudin..Cikin mamki yace basma u r just 17 ya kike wasa da kudi?
Wlh in baba ya jiki sai yayi fada..
Sai dai in kai zaka fada masa ta fada tana turo baki..
No babe, karkice haka bhu 20k zan baki dai gske..
Toh shikenan yaya tnx....
Kallon basma yake yarinyar wani kyau take ji dashi photocopy din anty fatee, amma wayonta ya mata yawa.. Gaba daya ta kere su safna gashi dai sun girmeta, lallai badon yana da tsayi ba sai basma ta hada kafada dashi, ba abinda ke damunshi kamar rawar kanta, sam ba abinda ya dameta kome yazo kanta yi takeyi, amma inda ya godewa Allah basma bata da qarya domin hatta soyayyarta da suhail ya sani.. Itako tinda ta shiga SS2 taji tafi qarfin suhail.. Coz ta fishi tsayi.. Itako ta bade idonta da toka akan ba ita ba wanda tafi tsayi.. A cewarta salon ace yana yawo da babarshi.. Dama basma siririyace da sauki amma jikinta yabi tsayinta yadda ya fitar mata wa kyakkyawar siffa da shape..
Mamie fur ta hana basma yawo da leggings a gd sbd ganinta suke kamar diyar inyamurai..Babu wanda baisan soyayyar basma da fahad ba a cikin gidan nan, yo ita meya dameta har Abbanta take bawa lbrn yadda ya fahad ke kula da ita sai dai yai murmushi...
*******
Ya ilaahi.. Mamie fito kiga ladies dinnan cewar anty aisha da gaba daya en mata ukun suka birge, wannan ai in hadizan bata dage ba sai ku fita kyau..
Safna taci maroon nd silver lace straight fitted gown.. Ta masifar yin kyau, noor kuwa coffee ta saka dama duk ta fisu haske.. Kyau yana zuba.. Amazing , cute, bright and elegant smile din basma said it all.. Blue lace ta ska, duk inda kyau yake ta hadeshi... Duk inda ka waiga camera ne ke haskasu tin daga gida...Mamie tace ikon Allah ni ynzu idan bikin naku ya tashi ai sai ina tofa muku addua kar a lashe min ku, diba kiga kyau anan!
An fara tafiya gun dinner, fahad ya hade girar sma data qasa shi gsky basma bazata fita a haka ba..
Sakin baki basma tayi tana kallonshi tace gsky hayatie kana da damuwa, bikin anty autan ne za'ayi bazani a haka ba? Chab.. To ko Abba daya ganni be mgn sai kai..
Ransa ba qaramin baci yayi ba dan wlh yana masifar kishin basma nd ya tsani wannan taurin kan, ysn inta kafe tofa sae tayi..
........ Harya juya zai wuceta.. Ta dan riqo hannunshi.. Day sauri ya waigo coz this is odd, sai tai saurin sakin hannunshi, a hnkl ta furta,
hayatie am sorry, na ma fasa zuwa tinda baka so ta fada kamr me shirin hawaye.. ~Nace su basma ansan qauna.~Kura mata ido yayi a hnkl ya furta, basma ina sonki de yawa, ina jin tsoron kar na rasaki ne.. Bana son kowa ya kalle min ke.. Plz take care of my hrt basma. Bawai hanaki fita zanyi kona takuraki ba, kishinki ne yake min yawa, amma kinji habibty, karki je a hka akwai veil me kyau dana sai miki sai kisa ko kinga ke jikinki ba iri daya bane dasu noor.. U hv d bst shape.
Duk kunya ta gama cikata, kuma sai ta ji gsky ya fada mata..
Dalla fahad kai muke jira, kasa er cikin ka a gaba, kana bata mana lokaci.. Ita kuma tinda ta tsaya shirme saita nemi motar da zata kaita cewar haneef dashi dama bason zuwa yake ba...
A'a yi hkr yallabai ku tafi kawai zanzo da tawa amaryar..
Tsaki haneef yayi yashige mota suka qara wuta..
****
Basma kuwa fahad ya birgeta amma ya bata mata budget harga Allah burinta taje ta bada assignment, ta zama topic of the day a wajen... Anyway zamuga me zai faru ai...
#########
Anty sury kuwa bayan khalil, ta haifi, batool ansha yaqi akan sunan sbd kowa yasn sunan fatima taci amma manager ya bade idonshi da toka, bayan batool ynzu ilyas ne qarami, suna ce mishi baba sbd sunan mahaifinta ne...
Biki kuwa sun kankane komai su adole iyayen amarya suko su anty amina sauki ne a garesu... Ko a bakin zanin su.
.....................
Nooor in kinawa Allah ki kawo min ipad dinnan, duba kiga wanda ya tsaida basma... Bala'eee, dan Allah kawo na musu hoto cewar safna tana sheqa dryr mugunta
A dayan bangaren kuwa alh. Sani ne yake tsara basma wanda tinda ya fara magna take kallon tumbinsa da kunnensa, wadda tayi imani baya buqatar pillow wajen kwanciya sbd girmansu..
Sai da yaje aya tace ji mana mallam kalli can da hannu ta nuna mai ya haneef tace inzaka koma kamar waccan ko kamar waccan ta nuna fahad a cikin sati biyu wlh ka dawo zan aureka..
Yace haba baby inada kudi fa..
Dariya basma tasa tace in kana son qari akan naka kamin mgn....Ta barshi a tsaya duk kunya ta isheshi...
Tin kafin ta qaraso inda sis dinta suke ta gane mugun abu suke mata gashi ta hngo ipad din a hannunsu.. Da saurinta ta qarasa ta bige ipad din passsss kakeji ta fashe... Basma ce ta fara salati wai wlh ita mistakenly ta taba ta, safna kuwa tsn qarya ne dan ranta yai mugun baci, ya fahad kuwa dake gefe baisan meya faru ba amma for sure ysn babe dinsa ce at fault...
Noor gidan kuka a tk ta fara hawaye... Nan fa Alamin yai kicin kicin shi adole an taba mishi haskenshi... Kuma bazai iya cewa kowa komai ba kawai zuwa yayi yaja noor yana bata baki har tayi shiru, yayi promising zai sai mata sbwr ipad..
Tace ya al amin nifa bakin cikina daya hotunan grad dinmu duk suna ciki 😂... Yace karki damu za'a gyara kuma asai sabo...............
Ha'a wai ina basma ne? Kowa ya dawo gida ban ganta ba, nd wayarta a kashe... Mamie take cigiya
Qila tana tare da ya fahad cewar safna cikin halin ko in kula...
Noor tace wane ya fahad din, bayan tin agun bikin suke nemanta shi da ya al amin...Anty aisha ce ta shigo a gigice tace mun shiga uku, diba ku gani an ga takalminta wari daya a bakin hall din amma babu alamarta....
Teeluv
Vote and comment.