Noor tace wlh sbd nasan da lbr nace mu fara zuwa naibawa wajen safna.. Ke kinga yadda safna akai fresh sai zuba qauna suke ya fahad ba sauki fa..
Dariya basma tai tace, kinji munafurci gun safna ko? Kafin auren nan kamar tai hauka ita she is not ready for marriage..
Dariya noor tasa tace wlh dai, kuwa dai safna anji kunya..
Basma tace ina zuwa..
Aslm alaikum..
Tashin ta yayi daidai da shigowar mazajen..,
A takaice basma ta amsa ta nufi daki ta barsu anan..
_yanzu fa basma sai ta cire abayan nan ta fito haka ko? Tana ganin al-amin ai dan uwanta ne_
Da sauri haneef ya miqe yabi baynta byn gajeran tunanin dayayi..
Drawer ta bude ta debo sweets da chocolates dayawa.. Juyowar da zatai da sauri ya bugi hannunta duka swt din ta watse..
Ranta ba qaramin baci yayi ba, batai zaton zai biyota ba, to uban me zai mata? Wani guntun tsaki ta saki iya lips dinta..
Matsowa yayi sosai.. Me lips dinki yayi ynxu?
Ya haneef dan Allah ka bari, noor tana jirana sweets din duk sun watse...
Shima sai yaji meyasa ako da yaushe yakewa basma kallon mara hnkl, sai yaji me yasa yake ganin kamar bata da nutsuwa..
A ranshi yace, ranki ya baci ne dan bige miki sweets to da ace kuma kinsan meya kawo ni fa?
Goshinshi yadan dafe cike da takaicin moves dinshi..
Basma kuwa aje mayafin abayar tayi ta bar hular kanta don gyalen damunta yake cikin gida, kitchen ta nufa ta dauko bowl ta kwashe alewowinta..
Ya haneef kuwa parlor ya koma fuska a sake suka gaisa da noor da aminu kamar yadda yake ce mishi..
Suna dan hira basma ta shigo da swts din tana fara'a kmar ba ita haneef ya batawa ba ynxu..
Ya al-amin mutan port.. Wlh ina son garin nan, muma ai zamu leqa musu ko ya haneef..
Kallonta haneef yayi yace eh ki mana tarin kudi ko autan mamie..
Dariya sosai sukayi, al-amin a ranshi yace lallai su haneef harda cracking joke lallai aure yayi ddi..
Al-amin yace matar yaya ynxu wannan kyautar aita noor ce, ni ina tawa? Kinsan dai bazan sa swt a gaba inasha ba..
Dariya tayi tace tuba nake, ai dole na sallameka yayana qanina..
Dariya suka danyi, haneef ma yadan yi murmushi
Yana jin ddi yaga basma tana fara'a tana hira.. So yake shima ta dinga maqaleshi tana mai lbrai da hirarraki masu dadi.. Amma sam bata liqe mai sai ta tashi yin basajan ta.. Dazu data kwanta kafadarshi jiyai dama ta dawwama a haka..
Bayan dan hira da sallama, basma ta daukowa al-amin wani turare mekyau tace gashinan yai tayiwa aminiyarta kamshi.. Suna dry sukai sallama, har motar su ta fita tana admiring dinsu..
Ita meyasa nata mijin is not loving and caring? Kowa da kalar tashi qaddarar taba kanta amsa... Jitai jikinta yai sanyi....
Masallaci ya haneef ya fita, itama ta miqe tai sallah, kafin ya dawo ta shiga kitchen tana preparing chinese rice da shredded beef.. Ga Bananas ta debo zatai smoothie...
Yana shigowa ya tabbatar basma tana kitchen dan yadda kamshi ya cika gidan..
Anya ita ce ta iya girki haka?