_Wasu sunce jajayen furanni daka fi sani da rose 🌹 tamabri ne na soyayya, wasu sunce kayan qawa ne da kayatarwa, wasu sunce ababen nishadi ne da kwantar da hnkl... Daga bakin duk wani ma'abocin farin ciki babu kalma mara dadi dangane da wannan fure.._
_Samunsu yakan bada wahala amma kyansu na daban ne, abin mamaki duk wannan kyau da suka mallaka idan suka sami bara gurbin kulawa, suka fada hannu marar kyau, wato mugun yanayi lawashin albasa sai ya fisu kyau da jan ra'ayi... Sai Sun kasance halitta me gajeran zango., shiyasa bature da balarabe basa wasa wajen tattalinsu da basu ruwa sai suyi tsawon rai su qara cika su qara bunqasa..._
_To ku dauka itama mace haka nan take, duk yadda mace take kamar fure ne, tana da komai da fure ya siffanta dashi ba kowacce bace take taka matsayi da daraja irinta 🌹 rose acikin fure, to idan ka sami daya, sai ka tattalata kada ka bari tai kukan yunwa ko kishin ruwa sbd in bata samu kulawa ba zata lalace!_
Nasihar daddy ce take dawo mishi lokacin daya furta yana son basma... Wasu zafafan hawayene suka zubo mishi.. Yana kuka yana fadin daddy i couldn't make it.. Basma was shattered, broken and weak all because of me! Why me? Mesa zan kasa kula da wannan furen me tsananin daraja da wuyar samu... Amma daddy basma ba raguwa bace, basma ba kamar sauran roses take ba, ita ta riga ta yi girma ta kafu.. Tana da foundation me kyau wanda baxai motsa taba, ita akomai ta daban ce, basma KAINUWA ce!, Dafe kanshi yayi cikin takaici da baqin ciki... He really want to see basma tonight!
****
B... A... B.... A nikuma? Ina fahad din? Bannn.. Yana stammering baba ya katseshi...
It's a command, if u like u can mess up!...
Jiki a mugun sanyaye haneef ya fito ya nufi part dinshi, yama rasa wanne tunani zai fara, meya raba fahad da basma?
Mesa baba yamai wannan babban albishir?
To tayaya zai tunkari basma da soyayya?
To wai meke shirin fruwa dashi ne... Gashi baida abokin hira cikin gidan nan bare ya sami details, mamie ba kulashi zatai ba, fahad kuma akanshi ne abu ya faru!
Ya salam!Ko kayan jikinshi bai samj kwarin cirewa ba bare yai wanka, da mugun yunwa ya shigo amma kaman anyi ruwa an dauke.. To wai wannan dama ya samu ko kuma akasin haka, ya fara tsoron karfa shigo shigo ba zurfi ake shirin mishi, sai ya sa rai kuma su shirya da fahad din, idan fada sukayi... The is completely confused zama yai gaba gado kawai ya dafe kanshi.. Dan kwakwalwarshi ta kasa processing komai..
Tunowa yayi yanayin daya riski basma da wani har tana mai dariya.. _nace haneef baka gani dakyau ba_
Wani mugun tsaki ya saki dan ya shaqa!
•••
Kee meya faru kika shigo kina haki kmar wadda tai tsere ko mayen ne? Safna ta fda tana dry..
Basma tace, kin ci bashi wlh, dan rashin mutunci hamxan zan zauna inawa haki?
Noor tace to waye?
Assalamu alaikum hajia basma gashi inji wannan me jar motar.. Asbe ta katse su..
Karba basma tayi ta bude ledar, ba tare data damu ba ta dauko pack din max daya ta ba asbe, tace kema ki bawa yara.. Karba tayi tana ta godia ta fita..
Tana fita suka bode kayan duk tarkacen kayan zaqi ne dangin chocolate da alewowi, sai cakes kala kala da pop corn na alfarma, zuma ce gaba daya jikinshi da madara, nan fa en matan suka sa murna kwadayi yaxo.. Ku dakata inji basma.. Bowl ta dauko ta debi ko wanne daga varieties din ta zuba tace this is for my lil mama.. Batool and lil papa khalil....
Murmushi en matan sukayi cikin jin ddi, mamie dake bakin daki take kallonsu wani farin ciki ne ya ratsata, haka yarinyar take, bata da dan ubanci, son qannen nata take ba ruwanta da uwarsu.. Abudaya ta sani, en uwanta ne..
Basma mutunce, bata da kyashi ko bakin hali.. Abu daya ne me daure kai cikin halinta, ba kowa ke iya fahimtar inda ta dosa ba, sbd soyayyar da takewa su batool bashi ke hanata yiwa uwarsu hau ba inta tabo ta.. Bata yadda a taka ta ba, batasan wulaqanci ba, dan bata yi kuma baxata dauka ba!
*_ita kyauta ko alheri danko ne baya faduwa qasa banxa, wlh duk wank marowaci baya cinma abinda yake burin cinmawa, duk wani me kyauta yanaa tare da samu, Allah ya bamu ikon kyautatawa da na qasa damu amin_*
Tana shirin fitowa mamie tai saurin juyawa dan bata son ta ganta.. Mamie takan leqo yaran nata akai akai ba tare dasun sani ba sbd kulawa da kuma lura.. Sam bata son ji ko ganin ba daidai ba dan gane da tarbiyyar yaran nata.. Ta tsaya tayin daka sbd sharrin zamani.. Yara uku ai bataga ta zama ba dole ta basu kulawa ta musamman!
••
Yeeeee anty basma nagode batool tana murna ta karbi bowl din.. Khaleel shima ya fito da gudu daga toilet yanason ganin meyasa batool murna haka... Laa zanchi nima..
Basma tace No khalil sai ka wanke hannu kaga daga toilet ka fito...
Ahayyye... To kai Ibrahim kaji kai akewa gorin tsafta.. Tsafta ta wuce mutum ya lallaba yai aure tin kafin yai bindiga.. To! dan gida ma da ake rawar kai akan shi yaja jiki ya gudu, waya sani ma koya samu abinda yake buqata ne ya qara gaba.. Babu tabbas fa idan arne bai kwashe duk wata gara da darajar da kowacce mace take tutiya dashi.. Kaico muazzamu baiyi dacen haihuwa ba! Dan gida ma ya gudu ballan tana bare..Dub dub dub qirjin basma ya buga dajin furucin anty sury akanta! Fahad? Fahad? Taya ya? Mutum mai tsantseni da kiyaye dokokin Allah... Taya ga zatai tunanin ya gama dani! Ko kuma ben!
Surayya! Ta fada cikin qaraji tare da sakin bowl din popcorn din ta fashe komai ya tarwatse...
Basma! Abba ya fada cikin bacin rai...
Waigowa tayi ranta yai mugun baci idonta ya cicciko da hawye zuciyarta na tafar fasa..
Ban baki wannan tarbiyyar ba, baki girman da zaki kira matata kanki tsaye ba kamad sa'arki, na haneki rashin kunya ko.. Ana fda min bana yadda yau daya idona ya nuna min, wato kin rainata! To ki jini basma ke fa yarta ce sbd ke yata ce.. Bai kuma magana ba ya nufi hnyar dakinshi...
Anty sury wani sanyin dadi taji kmr ta taka rawa dan murna.. Dan abban basma yaji shine ta daga murya take fadin..
Basma a kullum ki nake kamar batool amma duk sanda nai qoqarin nuna ke yata ce sai kin nuna min ban haifeki ba.. Kibi dunia a sannu, mahaifiyarki ta riga ta rasu ko tana raye bazata so taga kina kishi dani ba...
Wani mugun kallo basma ta jefeta dashi, a take gabanta ya fadi dan tasan taci bashi ne kuma sai ta biya!
Taku har kullum
Tee luv
Vote, comment nd recommend