20

1.9K 156 2
                                    

Sanye yake cikin qananan kaya baqar riga ce designer a gaban ta an rubata _the RABEL_ da golden color, da baqin jeans wanda yayi daidai da tsarin rigarshi, yayi kyau fiye da yadda ake zato, ramar da yayi ta sanya fatarshi qara haske da kyan gani, gashin kanshi yayi lub lub sai sheki yakeyi, qamshin turaren wisal ke tashi a hnkl...  Skin color dinshi me kyau irin ta black americans da suka sami hutu da jin dadi..  Da qarfi kirjinsu ya buga a tare...

Duk saita tsinci kanta da rikicewa sakamakon sallamarshi tayi daidai da bararrajewar da tayi a parlor tana shan rake.. 

Farar riga ce jikinta me qaramin hannu, gaban riga zane ne barkatai na multi colors..  Sai green short skirt wanda da kadan ya wuce gwiwarta...

Da dane gyale kawai zata janyo ta rufe kanta, amma ynxu kam baxata iya zama a haka ba..

Duk sai taji kunyar yadda ya sameta..  Qirjinta bai daina bugawa ba yadda hakan ya janyo mata mugun discomfort a parlon..

Yi yayi kamar bai ganta ba duk da ba qaramin bugu qirjinshi yake yi ba..
Mamie ina kwana ya fada a sanyaye.. 
With blank expression ta amsa mishi..  Da sauri basma ta miqe zata bar parlon..  Har ta kai bakin matattakalar benen taji ya ce BASMA...

BUGUN kirjinta qaruwa yayi, chak ta tsaya, ta kasa hawa ta kuma kasa juyowa..

Mamie kuwa tashi tai ta nufi part din mama.. 

Basma..  Zo ya furta cikin dakiya da nuna shifa baida matsala..

Itama dakewa tayi ta dawo, gyalen dake kanta ta ware ta yafa daga kanta zuwa qirjinta..   Seat ta samu ta zauna, kofa ta xubawa ido ta hade rai kmr babu abinda ke damunta.. 

Qare mata kallo yayi ya danyi wani murmushi, dry ma ta bashi yadda ta hade girar sama da qasa..  Wato zatai rashin kunyar data saba..  Hm

A hnkl ya furta choice opposition babu gaisuwa?

Da sauri ta waigo dan kalamar da ya kirata dashi ya nuna bayayinta, wanda ita anata zaton sonta yake shiyasa su baba suke qoqarin saukaka mai wahala..  A ranta tace chabdi jam! Gsky da kura...

Yaya ina kwana, ta fada kamar wadda akaiwa dole...

Bai amsa ba, kallon yadda tai maganar yayi, kamar kar tai shiri..  The way her mouth is moving make him feel little bit naughty..

Dagowa tayi kamar zatai fashe tace..
Sakamakon gaisuwar kenan?

Nifa in kasan haka ne ya kawo ka, gwara ka tsaya iya yayana bana son wani zancen so..

Ta fda tana fighting zuciyarta dan gabanta ba qaramin faduwa yai ba.. 

Ido ya zuba mata har ta gama..
Ido ya lumshe yace.. 

Ke kina sona ne?

Kafin ya bude ido ta bar gun..  Dan wani takaici daya taso mata..  Har ta isa daki bata daina jero tsaki ba...

Yana bude ido yaga wayam..  Da qarfi kirjin shi ya buga, a hnkl ya furta, shike nan bata sona!  Dafe kai yayi cike da takaici ya na tunanin mafuta...

*****

Da yammacin ranar haneef da fahad suka nufi dagin baba inda suka bashi lbrn duk abinda ya faru har takaiga rabuwar basma da fahad...

Baba dan takaici speechless ya zama, ya kira mamie da mama, abba da kuma daddy nan parlonshi.. 
Ya sanya fahad maimatawa..  A take kuwa ya warware lbr..  Mama kasa riqe kukanta tayi..  Itama mamie duk ta rude...  Kmr wadda saqon mutuwar dan nasu ya riska...

Baba ne yai gyaran murya, inda dora da cewa

Fahad yayi kuskuren boye wannan lbr da kuma danyen hukuncin daya yanke akan basma ba bisa sharawa ba, ai cuta ba mutuwa bace, sbd hk shi baima yadda da wani banxan gwaji ba mara lasisi, sbd hka, a daren nan zasu tafi asibiti domin gwaji...

Su daddy kuwa duk tausayin fahad ne ya rufesu...  Shima haneef duk jikinshi yai sanyi da lamarin...

Ba'a bata lokaci ba, suka tafi asibiti basu samu ganin oncologist ba, dole suka jira sai washe gari tinda ba emergency bane..

****

Asslamu alaikum...

Wslm, basma

Naam abbana ina kwana,

Lfy lau, yasu safna,

duk suna daki...

Anty sury ce ta shigo cikin kissa tace.. Laa basma kin shigo kenan, kin gama mana fishi daga fadar gsky kuma duk sai na kasa gane kanki...

Basma ta gane ta fada ne duk dan ta tunzurata.. Sai tai murmushi tace a'a umma qarama, ai sanin nayi kuskure ne na dawo, bai kamata ba ya taiwa uwarta fushi, bama idan uwar ta gari ce mewa yarinyarta fatan alkhair, kin san uwaye na gari basa gorantawa yaransu aure ko yaudara sbd sunje islamia sun san qaddarace, wasu ma sai sun kusa talatin sukeyin auren kuma sbd samun gu irin na dan adam sai su bude baki su gorantawa dan cikinsu aure..  Gsky umma qarama akwai gyara a duniyr nan, mata sun manta cewa, _diya mace bata gorantawa er uwarta abu uku; aure, haihuwa da mutuwar aure!_..

Anty sury kuwa ta shaqa dan batai zaton jin haka daga bakin basma ba, tsab ta maida mata da magana cikin lumana!.. 

Abban basma yi yai kamar baya jinsu amma sarai ya fara gano akalar zancen..

Basma ce ta kalleshi tace Abbana kayi hkr nayi laifi dana kama sunan umma qarama.. Da fatan dai aranka kanajin kayi sa'ar haihuwata a erka ta fari, diyar fatima , umma babba...

Da sauri ya dago danshima ta faraa bashi mamaki, duk sanda aka ambaci fatima sai yaji wannan yanayin, kallon basma yayi sai yaga tana mai gizo da fateenshi..  Da hannu bibbiyu ya tallafo fuskarta ya yi kissing goshinta yace sosai ina alfahari da diyar fatee.. Allah ya miki albarka..

Anty sury cikin qaraji da bacin rai tace, ai wannan rashin mutunci ne da rashin sanin muhinmanci, in banda wulaqanci zaka wani sanya yarinya agaba kana wani tuna matacciya...

Basma ce tai murmushi tace haba umma qarama, ai matacce shine wanda yake raye amma rayuwarsa bata amfana mai komi ba, babu wanda yake ta tashi, umma tana cikin kabari amma sonta yana raye cikin zukatan rayayyu, abin tausayi, har matattu ma kishin ruhinta suke.. Umma ki ba abbana shayi yasha, kema kisha kadan naga hnkl ya tashi... 

Bata kalli expression din kowa ba tace..  Umma qarama ki shafa min kan qannenan in sun dawo dg sch. Kafin na kawo musu akewar rana..  Ta mike tai waje, ta bar sury da baki a hngame...

Teeluv

Vote, comment nd recommend.

With love ❤️

BASMA (COMPLETED ) Where stories live. Discover now