✳✴BASMA✴✳
ROMANTIC LOVE STORY AND FAMILY 👪 SAGA..
PART 44
BY
TEE ZAREWA...
Bayan komawar basma makaranta ne da yawa daga en ajinsu sukai mata caaa akan lallaifa shawara suke bata akan tayi family planning dan baxata iya engineering tana goyo ciki ko kuma baby ba..
Aysha dai ko alif bata ce ba sbd sanin halin er gidanta..
Ai kuwa basma bata bata kunya ba dan a take tace..
A cikinku babu wadda bata da saurayi hakane?
Eh suka amsa..
Kuna bashi lokaci kuyi waya kuyi hira haka ne?
Eh suka ce
Ruth bake na gani jiya an sauke ba 2am?
Sunkuyar da kai tayi cikin kunya..
Kinada lokacin clubbing, bin smari, da kuma chatting ko?
Basma ce bata da lokacin miji..
Da naci last semester exams da sa hannunku ne?
To na rantse zan iya aje karatun akan mijina da yarinyata.. Har da unborn babiea dina..
Family first!
Ta fada ta barsu a tsaye kamar wasu marasa galihu..
***
Cikin sa'a basma bata sake samun ciki ba sai da dab da 2nd semester dinsu na level 4... Lokacin salma nada three years don har ta fara zuwa day care.. Dake yarinyar dana wayo ga kuma surutu.. Aiko ba bata lokaci haneef yace ko inna kawai ta dawo kaduna, sai asa salma a nan daycare dake cikin barrack..
Basma kuwa bata gaddama ba.. Ta dawo ita dayace a sch..
Wannan cikin kam me wahalarwa ne, dun yadda taso ta boyewa ya haneef saida ya gane.. Tsoro take kar ya hanata yin wasu assignment din da suke cikin karatunta.. Wanda ita kanta tasan zasu wahalar da ita..
Suna zaune ranar sunday a parlor, inna da salma kuma suna daki..
Basma kuwa pillow tayi da lap din haneef yana tayata tsifa suna hira..
Baby kamar fa wannan karan baby boy zamu samu..
Dariya tayi tace... Ashe fa sojojin ana koya musu likitanci..
Murmushi yayi yace inma baqa kika fdan naji.. Kuma zamu gani..
Dariya tadanyi tace ni dinwa in fadawa miji baqar magana..
Yace gashi nan.. Har wani ana koyawa sojoji likitanci?
Dariya tayi tace.. Wasa fa nakeyi ynxu kar kasa mamiena tasa kuka....
Kasan fa muna sch duk sanda ka mana video call kamar ta fasa min waya har wani zullo take tana papa..
Dariya yayi yace eh mana yarinya tasan babanta..
Baby dagamin cinya karta ja ruwa.. Kanki yayi nauyi..
A hba swry ai juyowa zanyi kamin dayan side din.. Nifa na tsani tsifa kuma kaine meson qananan kitson, kaga kai akai wa kwalliyar ai...
Lallai ma yarinyar nan.. Kedai a miki tsifa ba ruwanka da kafata ko?
Yunkurin miqewa tayi tace wayyk bayana..
Da sauri ya yace sorry baby wasa nake miki kwanta na qarasa..
Wani dadi taji aranta tana qara godewa Allah daya bata miji kamr haneef...
****
Ten years later...
Jagoran wannan project din itace engr. Basma ibarhim haris.., sbd haka muna fatan engineer zata fito domin karbar karramawa ta musamman,....
Mutane sun baza ido jira suke suga wata Yoruba ko igala.. Ga mamakin duk wani mahalukin dake wurin yarinyace wadda shekarunta basu fice 32 ba, me tsananin kyau, wadda hutu da jin ddi ya bayyana ajikinta..
Sanye take cikin abaya peach wadda ta amsa sunanta domin tsananin kyau da ke gareta.. Ta yane kanta da maroon gyale wanda ya rufe kirjinda, wuyanta da kuma kanta tsaf..
Yadda rigar ta saketane yasa duk kwakwar mutum bazai hango surarta ba.
Murmushi kawai su abba suke suna main parlor dinsu suna kallonta live a BBC.. Duk wasu manyan tashoshi na qasa Nigeria da wajen ta sun jono wannan taro..
Kwarai babban taro.. Kanfanin babban attajirin nan ne hobert sing wanda yai suna a kafatanin dunia..
Project dinda basma tai leading shine babban mafarkin hobert na tsawon shekaru..
Ba qaramin mamaki yaji ba samun shi a Africa, Nigeria kuma kano, agun bahaushiya... Usul...
Salma, abba karami, zahra da sadik sai murna suke ammansu a tv..
Salma dai ba'a magana don kaf kawayenta saida tasa suka kunna tv don suga ammanta..
Bayan basma ta bude taro da sllama tre da gaisuwa cikin tsaftataccen turancinta mai fita daki daki da yake nuna lallai ita er Africa ce..
Sannan ta fara gabatar da godiarta zuwa ga mijinta.. Brigadier general Haneef Abubakar Haris...
Tafi kawai kakeji da sowa ta mutane...
Wasu cewa suke ni na zata qanwarshi fa don kamar da sukeyi, wasu suce hala auren zumunci ne.. Abu dai kala kala...
Bayan dukkan wannan bayanai suka nemi ta zauna a seat din da aka tanadar mata..
Babu musu taje ta zauna, sojojin mijinta gudu biyu suka je suka tsaya a bayanta don tsaro..
Safna kuwa taci sa'a ranar off gareta tana zaune a gida.. Murna take kamr ta tashi sama..
Frnds dinta na asibiti take kira akan su kunna tv, suga er uwarta..
Aikuwa kowa sai sam barka en hassada kuwa kamar suyi bindiga...
Noor ma ba qaramin dadi taji ba...
Minal kuwa daki ta gudu da dau wayar mamanta ta kira mamie sanin cewa su salma suna gidan mamie..
Cikin sa'a kuwa salman ce agun ta daga.. Tace mama mamin tana...
Bata qarasa ba taji minal na cewa ke dalla nice.. Ynxu muke ganin ammanki a tv..
Dariya tayk sosai cikin farin ciki tace wallahi kuwa.. Muma muna ganinta.. Ita da papa ai sukaga je abujan..
Haka dai yaran sukai ta murnansu ta yara..
*
Abu kamar wasa hobert saida yasai project din basma 200,000 dollars... Wanda yake daidai da kusan 72million naira...
Haba ai kafin kace kwabo..
Zance ya ratsa dun wani lungu da saqo na nigeria..Instagram kamar zata fashe.. Followers kamar zasu kashe basma..
Neman tallafi ya yawaita..
Ba'a nan hobert ya tsaya ba ya nemi alfarmar basma ta yi aiki a company dinshi na gine gine dake America akan albashi mai tsoka
...Abinda yaba kowa mamaki shine a take tai rejecting?
Hobert yace why?
Tace FAMILY FIRST...
am sorry, Nigeria need me..
Wani hawayen farin ciki abba yaji suna zubomai..
Lallai basma ta cika mutum..
En uwa kuwa kowa saida yaji ta kara shiga ranshi, har sunaji da irinsu basma nada yawa to lallai ba family ba hatta qasa sai tayi alfahari dasu...
ALHAMDULILLAH
TEE LUV.