Zaman goggo a asibiti bashi ya hana kama khaltum ba..
Tome kuwa zai hana a kamata? Bayan kowa yasani, goggo dai is paralyzed babu wanda zai hana qaddararta riskarta..
Ai dama ramin mugunta akace ka ginashi gajere ko kuma kai ka afka ciki....
Gashi dai ba laifin basma bare na ahalinta, amma barin jikin goggo ya shanye. Ta zama a kwantar kuma a tayar....
A wannan lokacin bata da wani gatan.. Yaron data shogwaba ta lalata ya zame mata dan kuka, yau yana cell gobe yana prison...
Sata, kwace, fashi, shaye shaye, bin mata sun zame masa sahibai a rayuwar duniya..
Ba mutuwar rayuwarshi bane abin tausayi abinda zai riska bayan ya kasance matacce shine abin tunani..
Me gata ya haifar masu?
Yara ne da tun tali tali aka bude musu ido da qiyayyar yayunsu, aka nuna musu yayunsu macuta ne azzalumai?
To ynxu yaya qarshen zalunci ya kasance?
Ko babu komai hadiza ta shiryu... Garin fiska biyu sai kuma ta gano abinda zuciyarta baxata iya yinsa ba..
Anasu zaton kamar yadda uwarsu ta dorasu akai, fatima da ahalinta azzalumai ne marasa adalci...
Ta shige jikinsu don ta yaqesu.. Saidai kashh..Kyawawan dabi'un data riska bazata iya juyawa musu baya ba, mutane masu karamci da yakana..
Tayaya zata san wannan halin sannan a hade baki da ita a cutar dasu?
Dalili kenan da hadiza ta fahimci a wannan bangare uwarta da en uwan uwar suke!
*
Earlier..Safna tayi kuka kamr ranta zai fita.. Bata taba zaton qoqarin basma yakai haka..
Yarinya karama, ta hada kawaici, kara, dakiya, hakuri da juriya.. Amma babu abinda mutane suka fi gani tare da ita face rashin hnkl da kuma rashin kunya?
A tunaninta duk mutumin daya hada kyawawan halaye haka baya buqatar muzanci daga mutane har haka?
Cikin kuka take ta maimaita why basma? Matar da zata iya miki haka wlh is capable of killing you, amma kince abarta duniya ta isheta..
murmushin qarfin hali basma tayi tace haba saffy, kinga mijinta ya daketa, yaranta su zage ta, aljihunta babu ko sisi, yayarta is now paralyzed, duba kiga asirinta ya tonu... Bakya ganin takaici, kunci da kuma tsoro a idonta
wannan kadai ya isheta, ganina cikin farin ciki kadai ya isheta, me zan mata? Barta kawai
Wani irin shiru dakin yayi sai qarar AC dake tashi..
basma bakya tunanin karta qara yunkurin cutar dake
Cewar al-amin cikin dakiya da qarfin hali.. Don kowa jikinshi yayi sanyi a dakin..murmushi tayi tace, karta fasa, yadda Allah ya kubutar dani a baya SHI zai cigaba da kareni.. Ni ban rayu da ummah ba amma na samu mamie, khalthum taje ta rayu da yaranta don baza su samu kamr mamie ba
Anty sury fashewa tayi da wani azababben kuka.. Rungume basma tayi tana cewa don Allah don Annabi ki yafe min wlh ban taba zaton haka zuciyarki keda tsarki ba..
Murmushi basma tayi ta janye daga riqon anty sury tace.. Duniya tafi baga ruwa jima, duk yadda kika dauketa umma qarama am haka zata zo miki...
Mamie cikin kuka tace basma bansan wace irin baiwa gareki ba tin kina qanqanuwarki kike da hakuri da kawaici, nakan kasa tantance miye alaqar taurin kanki da kuma sauqin kanki, hakurinki da kuma ramuwarki, kawaicinki da yawan tankawarki.. Basma Allah ya miki albarka..