Don't forget to press the star ⭐ at the bottom of your screens 💖
Vote, comment, follow and share with your F&F*************************
Page 04Kusan a tare suka jera zuwa ciki da Al'ameen, yana sane cewa yakamata ya sanar da mahaifinshi outcome of his visit to Binaaf, amma yana da buk'atar ya d'an huta tukunna. Side d'inshi suka wuce suka zube akan couch, shiru ne ya ziyarci d'akin na kusan mintuna biyar kafin daga bisani Al'ameen yayi breaking silence d'in da cewa
" My prince, wai meye yarinyar nan tayi maka ne naga gabad'aya ka fita hayyacinka? Is she that strong headed? " ya kammala da tambaya yana kallon Saleem d'in
Shiru yayi mishi bai ce komai bah kuma bai da niyyan cewa komai d'in, huci kawai yake tayi yana inhaling da exhaling iska loudly, ganin cewa bai da niyyan cewa komai ya sa Al'ameen sake cewa
"Man, I asked you a question, baka fad'amin abunda ya faru a Binaaf bah"
Kamar forcing d'inshi ake yayi magana, ya juya yana kallon Al'ameen da jajayen idanunshi yace
"Ameen you needed to see how that stupid princess spoke to me looking me direct in the eye, Wallahi wallahi ko a mafarkina ban taba ganin macen da tazo gabana ta gayamin maganganu masu d'aci bah bare kuma a zahirance, she wasn't even scared a bit"
Tashi yayi tare da zagaye hannunshi ta bayanshi yana tafiya to and fro a cikin d'akin, ya cigaba tare da warware hannayenshi yana demonstration dashi
"Tana da wani kwarin gwiwa a tattare da ita wanda na rasa inda ta sameshi, she has this ego that made her look sophisticated, can you believe tace min wai ITA SARAUTA CE? " ya tambaya tare da juyawa yana kallon Al'ameen
Al'ameen bai ce dashi komai bah, he's just looking at him silently and waiting for him to continue, sanin cewa tambayar tasa baya buk'atar amsa, yasan cewa yana sanar dashi neh
"Ni Saleem Aabideen zata gayawa sarautah Ameen? She won't like me the next time we meet wallahi, sai na tabbatar na koya mata hankali da ita da matsoracin mahaifinta mai goya mata baya, I promise " ya k'are maganar folding his hands into fists
Mik'ewa Al'ameen yayi tare da yin tattaki zuwa wurin Saleem, manly ya dafa kafad'arshi tare da sighing
"Huh" kafin yace
"Whatever it is, nasan cewa zaka iya gyarawa, you just need to be a bit soft towards her in dai kana son abunda kake nema, su mata k'aramin k'wak'walwa ne dasu, they need to be cuddled and pampered.... "
"To hell with what you think Ameen, babu macen da ta isa in rarrasheta wallahi, babu ita kuma bana tunanin za'a yita ma nan gaba, idan waccar kucakar ta turani zuwa bango sai na k'ona gabad'aya masarautansu, I'll set them all ablaze Ameen"
Ya kalli Al'ameen yana gyad'a masa kai in assurance sannan ya sake cewa
"Wallahi I will"
"Calm down man" cewar Al'ameen, tashi yayi yaje fridge ya ciro ruwan gora ya mik'a masa.
*************************
*Aaerat*
Kwance take kan gadonta ta baza gashi akan pillow, hannayenta dukka biyu ta d'aurasu bisa tummy'nta, idanunta a bud'e suke tana kallon sama, babu wani walwala a fuskarta saboda da alama tana tunani ne kuma akwai damuwa cikin ranta.
Sallamar Heenah ne yasa ta juyar da kanta direction na k'ofa sannan ta amsa a hankali.
Kamar yadda ta saba, flinging jakarta tayi zuwa kujera ta k'araso bakin gadon ta zaunah tana unlocking wayarta"Hi bae " tace ba tare da ta juya ta kalleta bah
Shiru Aaerat tayi mata bata amsa mata bah, ita dai taga ta zaunah amma batasan abunda take fad'i bah

YOU ARE READING
AAERAT (The princess of Binaaf)
Mystery / ThrillerAAERAT is the story of a Binaaf princess, who's forced to marry the enemy of her father for the safety of her Kingdom ... In a kingdom where women are treated as the inferiors, where women are the victims of domestic violence, where women are depriv...