CHAPTER THREE

338 54 11
                                    

👑 *AAERAT* 👑
(The princess of Binaaf)

Written by: *Seemby luff*😘
Wattpad: *Itz_Seembyluff*

Don't forget to vote, follow, comment and share💖
*********************
Page 03

   Head held high take takunta cikin izza da kasaita saidai zuciyarta bai daina bugawa bah, ita kanta tasan maganganun data fad'awa Yariman Bairaan sunyi tsauri duk da shi ya sanya tayi masa abunda tayi, tunanin meye makomar abunda ta aikata take don tasan tabbas mahaifinta sai yaji wannan zancen. Kai tsaye side d'inta ta wuce, babu wanda ta amsawa barka da dawowan da ake mata kamar yadda ta saba, she was completely lost in her thoughts, bedroom d'inta ta wuce tare da cire alkyabban ta jefashi kan couch, gado ta koma ta kwanta da bayanta tana kallon ceiling.

Ganin shigewarta d'aki yasa Jameelah bin bayanta tana tunanin what could have happened daya canza mata mood d'inta, da sallama ta karisa cikin d'akin sannan ta tsaya kusa da gadon tace

"Lafiya kuwa gimbiyata? Waye ya b'atawa d'iyar sarki Abdullahi, jikar sarki Muhammad rai? Ban saba ganinki a irin wannan yanayin bah gimbiyata, ko zaka iya fad'a min matsalarki? Naji cewa idan mutum ya tattauna matsalarshi da wani, toh yakan samu sassaucin damuwarshi "

Dafe kai Aaerat tayi ta tashi zauneh, a hankali ta juya ta kalli Jameelah ta d'an yi mata murmushi, kamar batason magana tace

"I need a glass of water please"

Da yake kusan kullum sai ta fad'i haka yasa Jameelah ta gane cewa ruwa take nema, she needs not to repeat herself in hausa again. Hurriedly ta k'arasa wurin bedroom fridge dake edge d'in d'akin ta bud'e, bottle water ta ciro sannan ta mayar ta rufe. A saman mini dinning table ta d'auko glass cup ta tsiyayi ruwan a ciki ta mika mata.

  A nutse take shan ruwan har ta gama dukka ta mik'awa Jameelah cup d'in, k'in tafiya tayi tana jiran Aaerat ta fad'a mata damuwarta, a karo na biyu Aaerat ta sake d'agowa ta kalleta sannan ta nuna mata gefenta a kan gadon tace

"Zaunah"

Babu musu ta zauna kamar yadda aka umurceta, sai da Aaerat ta ja dogon numfashi tukunna tace

"Jameelah bansan yadda zan sanya mahaifina fasa auren nan bah, Gosh! The guy is a moron, I so much hate him wallahi "

Ido kawai Jameelah ke binta dashi don ba jin abunda take fad'a take yi bah.

********************

Gabad'aya jikinshi is shivering to the anger that's strewing out of him, bai tab'a tsammanin akwai ranar dazai zo da wata mace zata kalli k'wayar idonshi sannan ta fad'a mishi magana bah, deep down inside of him he loves her ego, he loves how brave she was to have looked him in the eye ta fad'a mishi abunda ta fad'a, amma idan ya tuna hakan sai yaji bakin ciki a cikin ranshi. A zuciye ya juya ya fice daga parlor'n yayinda guard d'inshi ke binshi a baya zuwa mota

Da ganinshi yasa wanda ke tsaye kusa da motan yayi saurin bud'e masa k'ofa ya shige, before the blink of an eye convoy d'inshi suka tashi.

Tun d'azun he was trying to calm himself down amma abun yaci tura, abun kept ringing in his head again and again, wayarshi ya d'aga ya shiga dialling number'n abokinshi. Ringing biyu sannan aka d'aga a na ukun

_Allah yayi maka yawan rai Yarima Saleem, mai tafiya akan kud'i kuma maganarka ma kud'i neh, the one only one who's ego destroys anyone else's,Allah dai ya kar giwa muci nama...._"

Zai cigaba Prince Saleem yayi saurin katseshi, yace

"Al'ameen, my ego has been overthrown today, wallahi ban tab'a jin bacin rai kamar yadda nake ji a yanzu bah, I feel so embarrassed " yana maganar bakinshi na kumfa

Sounding very confused Al'ameen yace

_Tsaya dai prince, kana nufin wancar yarinyar ta ci maka mutunci kenan? Shin ko bata san kai waye bane? The only prince who looks every inch of the royalty he is" ya k'are maganar da mamaki

"Bari kai dai, you need to see how she talked to me, kamar ni ba kowan kowa bah, wallahi wallahi wallahi sai tayi data sanin abunda tayi min, I'll make her pay for it har sai ta durkusa a gabana tana neman tafiya, that I promise you" cewar Saleem, yana gama fad'in haka ya katse wayar

3 hour drive ne daga Binaaf zuwa Bairaan, hakan yasa Saleem regretting rashin zuwansu da jet na mahaifinshi, ji yake kamar bazasu isa Bairaan bah.

Ji yayi kamar 10hrs sukayi before finally arriving at the palace gate, wangale mak'ek'en gate d'in akayi yayinda masu busa algaita suka d'au himma,sauti mai dad'in saurare suke busawa wanda ya janyo hankalin duk wani leaving being dake palace d'in

Wani matashin da bazai wuce 25 bah ya fito ya tsaya a tsakiyar palace d'in yace

"Every activity should halt, the future king of Bairaan has arrived "

In da sabo kam sun saba, kowani fitan Yarima Saleem da dawowanshi sai anyi wannan sanarwan, nan take kowa ya tsaya a inda yake babu wanda ke motsawa, duk sun saka ido suna jiran fitowanshi. Sau tari idan yazo baya bari a kaishi har bakin fada kafin ya sauka a mota, he prefers ya taka kan red carpet da ake shimfid'a masa yana baza kasaita da d'agun kai, yayinda ma'aikatan gidan da sauran mutane zasu ke rusunawa suna gaisheshi, hakan na matukar sashi nishad'i.

Yau ma kamar kullum, chan nesa motarshi ta tsaya, cikin ji da kai da nuna isa ya fito daga motarshi yana yiwa jama'a kallon raini da rashin mutunci, nan take kowa ya zube da kai a kasa kamar had'in baki, babu wanda ya isa ya d'ago ido ya kalleshi saboda sanin consequence na hakan

"Takawarka lafiya Yarima Saleem, d'a d'aya tamkar da goma, magajin izza da sarautar Bairaan " cewar wancan matashin

Da jin haka yasa Saleem jin ego d'inshi na boosting, sai dai bazai iya murmushi kamar kullum bah saboda ranshi a bace yake sosai. Har ya kusa shigewa ciki yaji wata dattijuwa ta zube a bayanshi tana kiran sunanshi cikin hawaye, ko a jikinshi don shi kukan mutum da magiyarshi bai tab'a yin tasiri a zuciyarshi bah, he really enjoys making people feel forlorn, har zai shige sai kuma ya juyo, he's sure he'll enjoy this one

Kuka take yi kamar ranta zai fita, gefenta wata yarinya ce da bazata wuce 12yrs bah, sosai tayi k'okarin saita kanta tukunna tace

"Don Allah ka taimakeni kamar yadda Allah ya taimakeka Yarima, na yardar ma zuciyata cewa d'iyata zata zama wani abu nan gaba, sai dai akwai abunda ya tsaya tsakaninta da cimma burinta, ta gama makarantar firamare kuma malaminta ya tabbatar cewa idan har aka kula da karatunta zata samu d'aukaka nan gaba, don Allah Yarima ka taimaka ka yardar mana ta cigaba da karatunta"

A fusace Yarima Saleem ya matso yasa kafa ya tunkud'eta, wuka dake makale jikin bango ya zaro da gaskenshi zai fille mata kai, ji yayi an rik'eshi ta baya, juyowa da zaiyi yaga Al'ameen ne yana girgiza masa kai, a sanyaye yace dashi

"Don't do it Saleem, learn to control your anger"

Da k'arfin ya k'wace hannunshi daga rikon da Al'ameen yayi masa, kafarshi yasa ya take matar tare da pointing wukar saitin mak'ogoronta,yace

"A Ina ma kika samu kwarin gwiwar fuskantata da wannan maganar, this rule was made since the beginning of the Bairaan dynasty that an haramta wa mata zuwa makaranta saboda baya da amfani. Ku mata ba komai bane illa hidimai, amfaninku kawai shine to satisfy our sexual desires, cook and produce babies for us then bow down to our feets and worship us. Y'arki bazatayi makaranta bah, daga yau ki fara kawota tayi aiki tare dake, shine rayuwar da yafi chanchanta daku da duk sauran mata, don't ever show me this ugly face of yours else, I'll behead you kuma na kashe banza, now get out of my sight"

Da sauri Al'ameen yace su tashi su tafi kafin Saleem ya canza ra'ayinshi ya cire masu kai, sosai matan ke kuka ta kama hannun d'iyarta suka wuce.

*********************

Hope you are enjoying the story?
Vote, follow, comment and then share with your friends
Your votes and comments strews the magic in my pen💖💖

© *SEEMBY LUFF*😘

AAERAT (The princess of Binaaf) Where stories live. Discover now