CHAPTER TWO

335 67 13
                                    

👑 *AAERAT* 👑
(The princess of Binaaf)

Written by *Seemby luff* 😘
*WATTPAD* - Itz_Seembyluff

Don't forget to click the star at the bottom of your screens. Follow, share and comment
Thank you 💖

*************
Page 02

Murmushi Aaerat tayi sannan ta shige gaba ita kuma Heenah na binta a baya har suka fice daga master bedroom d'in. Maids dake tsaitsaye a parlor'n suka fara rusunawa suna yi masu barka da fitowa, wata y'ar matsakaicin shekaru da bazasu wuce na Aaerat da Heenah bah ta taho da gudu gudu ta tsaya dai-dai gabansu, hannunta d'auke da wani tray wannan a samanshi wani need sequenced alkyabba ne mai kyau, with a smile adorning her face ta duka tana fad'in

" Barka da fitowa gimbiyata, kinyi matukar kyau tamkar hasken wata dake yaye duhun dare, idanunki na fitar da kyalli kamar taurarin da suke kewaye da wata suna k'ara wa sararin samaniya kyau. Allah yayi miki tsawon rai gimbiyata, Allah yayi miki mulkin masarautan Binaaf"

Numfashi Aaerat taja tana girgiza kanta, kamar bata son yin magana sai kuma tace

" Ke dai Jameelah akwaiki da surutun tsiya, sau nawa zan fad'a miki ki daina yimin wad'annan kirarin, nifa banaso ku cusa min girman kai and from all indications kunaso ku boosting min ego na, what you guys need to understand is that I'm perfect the way I am"

Dariya Jameelah tayi tana ta faman nodding kanta as if tana jin abunda take fad'a, tace

" Ga alkyabbanki nan ya gimbiyata, ki sanya sannan ki cika kamalarki a idon bakonki, hakan zai karawa Binaaf da mahaifinki martaba a idonshi "

Bata tsaya jin meye Aaerat zata fad'a bah ta yaye gyalen data rufa a hankali ta ije, tray'n ta mik'awa wacce ke tsaye gefenta sannan ta d'ago alkyabban ta warware, a nutse ta saka mata ta kuma gyara mata zamanshi dai-dai a kanta, a hankali ta matsa baya tana yashe baki tace

" Yanzu kin fito cikakkiyar gimbiya"

Cikin bakin ciki da b'acin rai Heenah take hararan Jameelah, wato ita d'in statue ne a wurin da baza'a yi mata nata kirarin bah, ai koda ita ba d'iyar sarki bace mahaifinta ne Galadiman Binaaf, she's supposed to be given equal respect with Aaerat.

Jan hannun Aaerat tayi tana murmushin yak'e tace
" Saboda Allah ki daina kula wannan yarinyar, she'll just waste your time and you have someone waiting for you, you know how impatient he is in kikayi la'akari da yadda ake fad'a, don't keep him waiting " ta k'are maganar tana yatsina fuska tana kallon Jameelah

Dafa kafad'ar Jameelah Aaerat tayi tace da ita

" D'akina na buk'atar gyara Jameelah, make sure an gyara min kafin in dawo " ta k'are maganar tana yi mata murmushi

Itama Jameelah murmushin ta mayar mata kafin tace

" An gama ranki ya dad'e, a dawo lafiya " Juyawa tayi kan Heenah ta wurga mata harara ta juya tayi tafiyarta, a zuciyarta tana cewa

" Mutum sai shegen girman kan tsiya, mts!"

**************

A k'ofar mak'ek'en guest parlor'n taja ta tsaya, zuciyarta na beating kamar zai fasa k'irjinta ya fito, it's the first time they are meeting and she can't help but think of how cruel he is, kusan kullum sai taji labarin rashin mutuncin da yake yiwa jama'ar masarautansu, tana cikin tunanin taji Heenah tayi tapping shoulder d'inta, gently ta juyo ta kalleta da fargaban dake kwance cikin idanunta.

Girgiza mata kai Heenah tayi tana so ta bata k'arfin gwiwa, hannunta ta d'ago ta d'aura mata a saitin kirjinta tace

" Listen to the pulsation of your heart princess, it's beating swift yeah? "

AAERAT (The princess of Binaaf) Where stories live. Discover now