CHAPTER FIVE

507 79 48
                                    

AAERAT

Vote, comment, follow and share💖

************************
Page 05

    Sai da ta idar da sallar Isha d'inta sannan ta mik'e jiki a sanyaye zuwa bathroom, ta kai 30 minutes tana shower kafin ta fito. Bayan ta kammala shafa mai ta tafi zuwa gaban closet d'inta, a nutse taja k'ofan ta tsaya dai-dai b'angaren night wears d'inta, wani mint green ta ciro da wandonsa dogo ta saka, sai kuma ta d'auki babban hijabinta ta zuwa da niyyan zuwa gaida Ummanta.

   Sosai zuciyarta ya buga lokacin da Umman ta fad'o mata rai, ta san tabbas yau zata sha hate speech da maganganu marasa dad'in ji tunda tun safe basu had'u bah.

Zama tayi bakin gadonta wanting to calm herself down, she knows she has to be brave and strong for her father and the entire kingdom, a kullum idan ta had'u da Umma sai ta b'ata mata rai, sai ta fad'a mata maganar da zai sa zuciyarta ta karaya.

Ji tayi an tapping shoulder d'inta, a hankali ta juya taga Jameelah tana smiling, duk da itama kanta bata san ko zata iya mayar mata da murmushinta bah but she felt the warm smile on her face, haka kawai presence na Jameelah ke soothing d'inta, her gentleness da sanin yakamatanta, sam she doesn't behave as an illiterate and she's one

" Gimbiyata, Nasan cewa kina cikin wani hali a y'an kwanakin nan, na sani da mahaifiyarki na raye abun zai zo miki da sauki, mahaifinki ne kad'ai ke goya miki baya a cikin gidannan kuma Kinsan ba lallai baneh ko da yaushe ya tsaya maki. Shi sarki neh, miliyoyin jama'ar Binaaf duk a karkashinshi suke, a gefe guda ga Sarauniya Firdausi wanda a kullum burinta ta karyar miki zuciya"

"Huh" ta d'an ja numfashi tukunna taci gaba

" Idan har kin d'aukeni kawa kamar yadda kika ce, zan baki shawara Gimbiyata "

Ta karashe maganar tana kallon Aaerat, a hankali ta nodding mata kai kawai bata ce komai bah, hakan ya bawa Jameelah daman cigaba domin an bata dama

" Kada ko d'aya daga cikin abubuwan da suke faru su sa ki kara Gimbiyata, dama dole ne rayuwar mutum bazai tab'a tafiya dai-dai ba tare da k'alubale bah. Inaso ki zama jaruma, ki yarda da ubangijinki kuma kada ki gaza wajen kai masa kukanki, shi yasan dalilin da yasa aka haihoki cikin wannan masarautan, shi yasan dalilin da yasa ya bawa mahaifinki ke, watakila akwai wani babban Al'amari da zai faru nan gaba, kada ki tab'a karaya kinji "

Da sauri ta shiga gyad'a kanta bata tsayawa yayinda hawaye suka fara zarya a fuskarta, like a baby ta shige jikin Jameelah burying her face in her neck

Itama Jameelah idanunta sun kawo hawaye amma sai tayi saurin gogesu kada Aaerat ta gani, she wants to be her source of strength and seeing her tears will only break her again. A hankali itama tayi wrapping hannayenta a jikinta tana bubbuga bayanta, sun kai kusan 4 minutes a haka kafin daga bisani Jameelah tayi breaking hug d'in tana cewa

" Bar kuka yanzu"

D'agowa Aaerat tayi tana murmushi tace

"Thank you Jameelah, thank you"

Sannan ta mik'e zuwa b'angaren Ummanta, Jameelah na biye da ita.

******************************

   Suna isa b'angaren Sarauniya Firdausi Aaerat taja ta tsaya, duk lokacin da tazo nan sai ranta ya mugun b'aci, ace wai mutum da gidan ubansa sai ya nemi anyi masa iso zuwa wani wuri?

Sarauniya Firdausi mace ce mai matukar son mulki da nuna isa, tana son nuna izza kuma she likes looking down upon people. Kusan komai with the exception of bathing yi mata ake yi.

Aaerat bata ce komai bah kamar kullum, Jameelah ce tace da wasu hadimai biyu dake zaune nan bakin k'ofa

" Ayi manah iso da Sarauniya Firdausi, d'iyar sarki kuma magajiyar kujeran sarautar Binaaf ke son gaisheta"

AAERAT (The princess of Binaaf) Where stories live. Discover now