CHAPTER NINE: THE TREATY

152 19 5
                                    

      Kaya masu yawa suka siya a mall d'in, sai da Aaerat ta jira Heenah ta karashe nata shopping d'in tukunna ta tafi counter ta bayar da credit card d'inta don making payment, sannan masu aikin wajen suka kai masu kayan zuwa mota, Aaerat kam ta gaji sosai y'ar shopping a waje d'aya da sukayi, zama tayi cikin motan tana jiran Heenah da tun d'azu ta tsaya cikin mall d'in tana yin abunda Allah kad'ai ya sani, can sai gata ta fito tana ta wani karairaya,  hakan yasa Aaerat ta kura mata ido daga inda take tana mamakin halayyanta, har ta karaso Aaerat bata d'auke idanunta a kanta bah, bud' e motar tayi ta shiga tana sauke numfashi ta juya tana kallon Aaerat tace " Billahi i'm damn tired girlfriend amma nasan we have a lot more to do so,  can you please drop us at a nearby eatry? i'm so so hungry Allah" Aaerat da ta gaji, ji take kamar ta rufe idanunta ta ga kanta a gida ta juyo tana kallon Heenah na d'an wani lokaci tace "and what is that 'lot more to do' yo are talking about? Heenah idan kika ga na tsaya ko ina to gida neh, fine you are hungry but we'll go eat at home" kamar Heenah zata yi kuka tace " haba manah, kin manta zamu gyaran gashi neh?" Aaerat bata kalleta ba ta fara kokarin tada motar kamar ba zata ce komai ba tace " sai aka gaya miki dole sai munyi duk abubuwan nan yau koh? i'm so exhausted and i'm not going anywhere from here" Heenah zata yi maagana Aaerat tayi saurin cewa "i'm not going back on my words Heenah, karki manta i'm my father's daughter, bana magana biyu, kiyi nhakuri kawai" tana gama fad'in haka ta tada motar suka bar wajen. Har suka isa gida babu wani hiran da suka yi, kowa da tunanin da yake yi a zuci, Heenah na gefe tana ta faman b'ata fuska tana ta kumbure kumbure yayinda bata ko ishi Aaerat kallo bah, parking lot direct ta wuce tayi parking motar sannan ta fito ta d'an jingina da jikin motan, kusan palace guard uku suka karasa duk a tare cikinsu har da head-guard suka zube gabanta suna mata sannu da dawowa, da fara'arta ta dubi head-guard d'in tace "can you please take this stuffs to my chambers" ta kare maganar kamar tambayarsa take, jiki na b'ari yace "sure my princess, Allah ya baki yawan rai" mika masa car key d'in tayi tace "thank you" sannan ta wuce, sai a sannan Heenah ta bud'e motar ta fito itama tana ta faman shan qamshi, gaisheta suka higa yi itama ta wani ignoring d'insu kamar ma ba'ayi halittan mutane wajen bah ta bi bayan Aaerat, cikin isa head-guard d'in ya zagaya ya bud'e boot d'in motar sannan ya umurci sauran biyun da su kwashe kayan zuwa ciki.

THE TREATY [YARJEJENIYA]
BAIRAAN
      D'and'azon jama'a neh tare a tsakiyar fadan sarki Muhammad Aabideen, daga gani carbinet members d'inshi neh cikin shiga ta alfarma na gani na fad'a, motoci neh parked in a straight line sun kai kusan talatin suna jira, sun kai kusan mintuna ashirin suna tsaye daga karshe wani d'an dattijo ya fito da d'an gudunshi ya tsaya daga bakin entrance yayi making announcement na fitowan sarki, masu sarewa ne suka fara aikin busawa a yayin da mai kirari yake ta kirara sarki, har ya kai bakin mota, then follows the prince of Bairan; the elder son of the king of Bairaan, the sole heir to the throne of Bairaan, the handsome and charismatic prince that makes ladies jaws fall on the floor.  A hankali yake takunsa kamar mai tausayin kasa, kaya ta alfarma neh sanye jikinsa daga kan alkyabbansa zuwa takalmin dake sanye kafarsa, head held high yake tafiya yana kallon taron mutanen ba a bakin komai bah, nothing matters to him right at that instant kamar treaty da zasu je signing a masarauntan Binaaf, he can't wait to get over with this,  he can't wait ya koyawa wancan y'ar rainin wayon gimbiyarsu hankali, murmushi yayi yana kitsa abubuwa dayawa a mind d'inshi har ya karasa wurin mota, da sauri aka bud'e masa kofan motar ya shiga sannan aka rufe, sai a sannan yayi murmushi mai kara yace " it'd be only few months for you to be mine princess, only few months and i'll get to teach you the lesson of your life, sai na nuna miki cewa kinyi babban kuskuren d'aga min murya da kikayi a ranar farko, sai na nuna miki cewa b'an d'auki mace a bakin komai ba sai abar hutawa and that no woman on this earth is worth my respect, i'll make you realize that the whole of the Binaaf dynesty and the Binaaf clan means nothing to me... Just come to me wife, i have a lot in store just for you" bayan ya shiga motan neh kowa ya shiga nashi suka kama hanyar Binaaf.

AAERAT (The princess of Binaaf) Where stories live. Discover now