CHAPTER 12

135 12 5
                                    

SET TO COME BACK HOME
CAMBODIA 2019
Fitowanshi a wurin wanka kenan a gurguje saboda wayarshi dake ta kara babu kakkautawa, still curious to know who has been calling him without a break though yasan wanda yake masa irin wannan kiran
da towel d'aure a kugunshi ya fito ya nufi side drawer inda wayarshi ke ajiye ya d'aga a nutse, "Haba Mas'oud, wai me yasa halinka baya canzawa neh, if you call me twice and i didn't pick up it means i'm not with the phone
and i'll definitely see your missed calls when i return, kullum fad'ana da kai fa kenan amma har yanzu ka kasa gane hakan, i still wonder what type of human you are" ya kare maganar yana b'ata fuska kamar Mas'oud d'in
na gabanshi, shekaru da dama suka san juna kuma tun daga wannan lokacin jininsu ya had'u duk da ba wata abokantaka sosai baneh a tsakaninsu amma kusan halayyarsu na saukin kai da son taimakon jama'a a lolacin da suke
bukata yazo d'aya, sai dai akwai abu d'aya da baya so game da Mas'oud wanda shine halinsa na idan ya fara kiran wayarka to fah ba zai tsaya bah har sai ka d'aga koda kuwa sau dubu neh zai kirah, a d'ayan b'angaren Mas'oud
yace "You already know by now that it's my nature and i can't stop just becase you tell me to, i'm just calling to tell you i'll be going somewhere in a bit so you better come get your shave coz i don't think i'll be back anytime soon" yana
kaiwa nan ya katse wayar don baya son jin mita, girgiza kai yayi sannan ya ajiye wayar ya koma gaban mirror ya shiga shiryawa, ba'a d'au lokaci bah ya kammala abunda yake a gaban mirror sannan ya koma closet ya bud'e tare da
d'an ja da baya yana tunanin wani kayan zai saka duk da cewa closet d'in a cike yake da kaya makil, kusan kullum d'abi'ar kenan, sai yayi tunani sosai kan kayan da zai saka kafin daga bisani ya yanke shawaran wanda zai saka d'in
ya d'au tsawon lokaci a haka kafin daga karshe ya juya b'angaren English wears ya fara fiddo shirt sannan ya fiddo rigar da zatayi matching da shirt d'in yazo ya saka. Fridge ya nufa ya fiddo chilled water ya b'alle marfin sannan ya
kurb'a yana rufe idanunsa, sai da yaji he's satisfied tukunna ya ajiye sannan ya d'auki car key d'inshi da wayarshi ya sauko downstairs.

Mahaifiyarsa na zauneh kan d'aya daga cikin sofan dake zagaye da parlorn sannan kuma a favorite spot d'inta tana kallon wani program a TV ya sauko a hankali ya rungumeta ta baya yana sumbatar gefen fuskarta yace "Barka da
hutawa Aunty Ummah" hakan yasa ta girgiza kai bata ce masa komai bah sai da ya saketa don kansa ya zagayo ya zauna a sofan dake kallon tata, remote ta d'auka ta rage volume na TV'n ta kallosa da serious face tace "Wai Iqbaal yaushe
zaka girma neh ka daina wannan shashancin naka, how many times do i have to tell you that you are no more a kid, god'e-god'e da kai ka isa aure amma ka rinka rungumata kana sumbata kamar wani karamin yaro sannan ni kuma ka mayar
dani kamar kakarka, i'm your mother Iqbaal, stop doing all this and grow up baby, please" abun ma sai ya bashi dariya, saukowa yayi daga sofan ya durkushe gabanta sannan ya kamo hannayenta duk biyu yha d'ago yana kallonta yace "You just
said it Mum, you just called me a baby and that only means i'm still a baby, haba Aunty Ummah yanzu fa ba zamin da baneh da kuke jin kunyan duk wad'annan ababen, this is a modern world" da sauri ta tari numfashinsa da cewa "Yes, it's a modern
world amma bai kamata mu manta al'adarmu ba ai, karka manta da wannan" sumbatar hannayen nata yayi sannan ya koma ya zauna yace "Naji toh abunda kika ce, dama inaso in fad'a miki wani magana mai muhimmanci neh, sannan inaso ki gane
cewa sai da na tsaya nayi nazari da tunani kafin na yanke wannan hukuncin, i just want you to respect my decision duba da cewa baki tab'a hanani aikata wani abu naki in hanu bah, all my life i've always been an obedient son and never did i think of
disobeying you, i hope you'll understand me this time" gyara zama Aunty Ummah tayi don bata tab'a ganinshi this serious bah, ajiyar zuciya mai kara tayi kafin tace "Insha Allah i'll understand you son, maganganun da ka fad'a duk gaskiya neh kuma ina
kara godewa ubangijina da ya bani d'a kamarka mai tausayi da biyayya a gareni, fatana kawai shine Allah ya albarkaci rayuwarka ya kuma biya maka dukkan bukatunka, i'll support whatever decision it is that you took no matter how it'll hurt me don nasan
bazaka tab'a yanke hukuncin da ba shi kenan bah, Allah yayi mana jagora" duk su biyun suka amsa da "Ameen" shiru neh ya d'an biyo baya na wasu mintuna yayin da kowannensu da abunda yake sakawa a cikin ranshi, lallai maganganun Aunty Ummah sun
matukar tab'ashi sanin cewa abunda take tsoro ne yake shirin aikatawa amma babu yadda ya iya, he can't keep running away from his responsibilities, he has to face them and fight if need be, d'agowa yayi ya kalleta da kyau yana kuma nazarinta kafin yace
"i think it's time Mum" sai da taji zuciyarta ya buga da jin furucinsa, those this mean her worst fear is about to be a reality? a hankali tace "Ya Allah ka bani karfin jure duk abunda zai sanar dani" dakewa tayi kamar bata d'ago abunda yake nufi bah tace "I
don't understand, me kake nufi da IT'S TIME?" ji yake maganganun sun tsaya a wuyanshi sun kasa zuwa kan leb'b'ansa bare kuma ya kai ga furtasu, sai da yayi da gaske yace "I'M SET TO GO BACK HOME" rufe idanu Aunty Ummah tayi taa maimaita
"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'oon" tabbas abunda take tsoro neh yake shirin faruwa, she has raised him with so much love without think that a day like this will come, ranar da sai so ya fuskanci wanene shi kuma yaji yana son exploring wannan feeling d'in, wasu
tsiraran hawaye neh suka sauko kan kumatunta ta ma rasa abun fad'a, sake durkushewa yayi gabanta a karo na biyu cikin tashin hankali yace " Aunty Ummah don Allah kada kiyi kokarin hanani thogh i know this must be hard for you to accept, it's also hard for me
to take the biggest decision in my life amma it's time i face who i am and the responsibilities that awaits me i nstead of hiding here like a coward, ni namiji neh Ummah, har yaushe zan cigaba da zama a nan tare da ke ba tare da masaniyar yaya duniyar ma take bah
you are my mother and i love you more than my own self, idan ma kina tsoron kadfa in koma sannan in manta dake neh toh hakan bazai tab'a faruwa bah, ke kika maidani mutum har na kawo inda nake a yanzu, mantaki ba daban yake da manta kaina baneh, you'll always
be in my heart and thoughts for as long as i'm alive" ya kwantar da kanshi a kan kafafunta yana hawaye shima, a hankali ta d'aura hannunta saman kanshi tana shafa sumarshi a hankali tace " Ni ba tsorona ka tafi ka barni ko ka manta dani baneh, tunanin yaya rayuwarka
zata kasance a inda baka saba bah sannan tare da mutanen da suka nuna rashin kauna a tare damu, kada su zo su cutar da kai saboda bazan tab'a juran hakan bah, kai kad'ai nake gani inji dad'i a cikin raina, i just wonder what my world will be like without you in it" babu abunda
suka isa suyi min Ummah, Babana yana sona and that reason is enough for me to be with him, with them, to face who i am as a man, babu abunda zai sameni kinji Ummata, insha Allah" d'ado da fuskarshi tayi tare da cupping a cikin tafukan hannayenta tana kallonsa tace " shikenan
Allah ubangiji ya kaika lafiya, ya tsareka daga duk wani mummunan abun da zasu yi maka, my blessings and prayers will always be with you" daga haka suka rungume juna suna jimamin rabuwan da zasuyi saboda basu tab'a rayuwa a wuri daban daban bah, cikin hanzari Iqbaal yayi
breaking hug d'in dalilin wayarshi daya fara ringing, ko tantama babu yasan Mas'oud neh da rashin hakurin tsiyan nan, mik'ewa yayi yana cusa wayar a aljihu yace da Aunty Ummah zashi haski, nan tayi mishi a dawo lafia sannan ya fice tana kallonsa har sai da ya b'ace da ganinta, goge
hawayen da ya sake sauko mata tayi sannan tace "I'm gonna miss you son".

BAIRAAN
Bayi neh kusan guda hudu durkushe gaban Sarauniya Fateemah, biyu na mata tausan kafarta yayinda sauran biyu ke mata firfita, a gefenta kuma Yrareema Saleem neh zauneh ya d'aura kafarsa d'aya kan d'aya yana kallon wad'annan bayin yana lasar leb'e, musamman ma d'aya daga
cikin wad'anda suke firfitan da suka bashi basa, yarinyar kam akwai dirin jan hankali ga tudun dake bayanta, a ranshinyace wannan ita ce next target d'inshi kuma lalle sai ya sauke kwad'ayinshi, yana cikin tunanin hakan neh yaji ana "Gyara kintsi, mai martaba Sarkin Bairaan zai shigo
wajen sarauniyarsa, gaba salamun baya salamun, gyara kintsi......" cikin hanzari har suna tuntub'e bayin suka mik'e tare da dukar da kansu kasa sannan suka juya zuwa waje, har a wannan lokacin Saleem bai d'auke idanunsa a kanta bah musamman yadda mazaunanta ke motsawa yanzu
da take tafiya, suna fita mai martaba ya shigo d'akin ya zaunah, cike da sarauta da yanga sarauniya Fateema dake kishingide tace "Barka da shigowa mai martaba sarkina, ko menene ya kawoka nan war haka?" hannu ya kai ya d'auki tuffah dake ajiye kan tray ya kai baki, sai da ya d'an ci tukunna
ya kalleta yace "Nazo neh in sanar dake zuwan d'anki, i want you to make all necessary arrangements for his arrivals" ba ita bah har Saleem sai da gabansa ya fad'i duk da basu tabbatar da wanda zai zo din bah, kusan a tare suka ce "wani d'an kenan", cikin idanunta ya kalla yace "IQBAAL"
nan take zufa ya fara karyo mata, lallailokaci yayi da zata tashi tsaye,bata tab'a tsammanin hakan a dai dai wannan lokacin bah, ita da ta d'auka Saleem neh kad'ai magajin kujeran mahaifinsa, ta ma manta he isn't the only heir to the throne of Bairaan, a b'amgaren Saleem kuma hankalinshi yayi matukar
tashi, a wani b'angare na zuciyarshi kuwa cewa yake "lokaci yayi, lallai lokaci yayi" yayin da d'ayan b'angaren yace "lokacin menene?" a bayyane kuma ya furta "FIGHT FOR THE THRONE"...

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jun 22, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

AAERAT (The princess of Binaaf) Where stories live. Discover now