THE ALLIANCE
Ranshi yayi makura wurin b'aci, har yau ya kasa gano inda ta samo wannan izza da zarran da take dashi a yanzu, ta gama ruguza masa jiji da kansa da tarihin da ya kafa cewa babu macen da ta isa ta d'aga ido ta kalleshi balle har ta fad'a masa maganar da ranta ya gadama
he needs to act fast domin ya sauke mata wannan rashin kunyar da take ji dashi sannan ya tsayar da ita a iya matsayinta na cewa ita mace ce kuma shi bai d'aiki mace a bakin komai bah, tafiya yake zuwa mota amma yana jin kafarshi na masa nauyi yayinda kanshi ke juyawa, lalle Aaerat
tana neman sashi ya rasa izzarsa wanda idan haka ta kasance zai iya mutuwa, he values his ego more than anything in the world and its clear to him that she is set to destroy it. Da kyar ya iya karasawa wurin motan, bai ma jira an bud'e masa marfin motan kamar yadda aka saba ba ya bud'e abunsa
kuma hakan shine na farko a tarihin rayuwarsa ya bud'e marfin mota da kansa, suna ganin haka kowa ya shiga tasa motar suka fice kamar zasu tashi sama. Tafiya suke da gudun gaske amma gani yake kamar basa ma tafiyan, he really needs to talk to his father right away don ayi komai a gama, burinsa
a yanzu bai wuce yaga ta zama mallakinsa bah, ta hakan ne kawai zai iya koya mata hankali sannan ya ruguza mata tsarin rayuwarta, tabbas sai ta kasance tamkar baiwa a Bairaan, sai yasa ta goge masa takalma da harshenta, he will make sure he reduces her to nothing until she begs for mercy at his feet
every blessed day, da wannan tunane-tunane a ranshi suka isa Bairaan.
Mota bata gama tsayawa bah ya banke marfin ya fita cike da b'acin rai, kai tsaye carbinet na mahaifinsa ya wuce sanin cewa zai samesa a chan yanzu, cike da gadara ya shige duk da maganar da masu gadin kofar suke masa kan cewa mai martaba yana tattaunawa ne a ciki, magana kawai suke masa cos no
one dares to stop him, yadda ya mayar da kofar ya rufe ne ya janyo hankalin kowa suka juya suna kallonsa har ya karasa gaban mahaifinsa ya tsaya yana huci, shima mai martaban kallonsa yake cike da tambayoyi a cikin zuciyarsa, a gefe guda kuma abun ya fara damunsa matuka because his sons behavior is really
getting out of hands, yana cikin wannan tunanin neh Prince Saleem ya yanke masa tunani yayinda ya tsinkayo muryansa yana fad'in "Father, we need to talk" Galadima neh ya mik'e yana masa wani kallo yace "kamar yadda kake gani muna tsaka da tattauna abu mai muhimmanci neh, i know whatever you want to discuss
with your father can wait, it's only a matter of some minutes and........." "And who are you to yell me how and when i will talk to my father huh? i said i want to talk to him right now so i expect you all to get out of here get it" "Leave us" cewar mai martaba, a fusace Galadima ya juya yana kallonsa sannan bakinsa ya motsa kamar dai
yana so ya fad'i wani abun, "NOW" mai martaba ya sake fad'a a karo na biyu, babu yadda suka iya iya dole suka mike zuwa waje, a zuciyoyinsu kuma suna Allah wadai da hali irin na Saleem da kuma goyon bayaa da yake samu daga mahaifinsa, tabbas sai dai suyi Allah wadai a zuciyarsu amma babu wadda ya isa ya bari tazo kan fatar
bakinsa. D'ago kai mahaifinsa yayi a karo na biyu ya kallesa sannan yace "wani maganan neh haka mai muhimmanci da bazai iya jira in karasa tattaunawa da nake yi bah? those people are my carbinet members, they have a say in every decision i take in this kingdom, don't you think they deserve a little bit of respect from you? they......"
"Ba abunda ya kawoni kenan bah" ya tari numfashin mahaifin nasa "i want this alliance to be finalized within two days, na kosa in kawo d'iyar marasa mutuncin chan gidannan, na kosa in nuna mata cewa ubanta ma ba komai baneh balle ita, i need to be over with this madness God damn it, i'm loosing my mind billah" ya kare maganar tare
da dafe kansadake barazanar fashewa, nazarinsa mahaifinsa ya shiga yi na y'an wasu lokuta kafin daga bisani yace "naji duk abunda kace amma, babu yadda za'ayi a kammala komai cikin kwana biyu kamar yadda ka bukata domin kuwa muna da al'adunmu a Bairaan kamar yadda suma na tabbata suna da nasu al'adun a Binaaf kuma
Sarki Saifullah bai yi kama da wadda zai kyale al'adar masarautansa ya tafi haka bah, shi mutane suke kalla don haka he must lead by example sannan kuma, bana tunanin zamu iya tankwasashi zuwa ga aikata duk abunda muke bukata, baka ganin we've asked for too much from him already? the person in question is his daughter, one he loves
with the whole of his life, shawaran da zan baka shine ka sake hakuri mu bi komai a hankali har a samu a kammala" Ba haka Saleem yaso bah amma sanin cewa gaskiya mahaifinsa yake fad'a yasa shi mikewa ya fice yana cizar leb'e, yanzu sai ya sake jiran wata d'aya zuwa biyu kenan? lallai he needs a lot of patience to deal with this fact.

YOU ARE READING
AAERAT (The princess of Binaaf)
Mystery / ThrillerAAERAT is the story of a Binaaf princess, who's forced to marry the enemy of her father for the safety of her Kingdom ... In a kingdom where women are treated as the inferiors, where women are the victims of domestic violence, where women are depriv...