CHAPTER SEVEN

123 21 1
                                    

A sanyaye ta mik'e ta tada iqaman sallan isha'i, bayan ta idar ta ninke prayer mat d'in ta mayar mazaununshi, da hijaab d'in jikinta ta
wuce parlor zuwa dining area saboda yunwan da take ji don rabonta da taci abinci tun breakfast da tayi, bata ma jin zata iya cin abincin
amma jin cikinta na juyawa yasa zata ci koda kad'an neh, p-soup ta d'eba cikin saucer kad'an ta ajiye gabanta, kamar ma contemplating
take taci abincin ko a'a, ta d'au tsawon lokaci a haka kafin ta d'iba a spoon ta kai baki, a hankali ta lumshe ido diving in the taste, sosai tasha
p-soup din don ba karamin dad'inshi taji bah, they've made it just the way she likes it, tissue ta d'auko tana wiping bakinta sannan ta tura kujeran
baya ta tashi a hankali ta wuce bedroom feeling very sleepy, bataji zata iya waya da Heena ma yau like they always do every night before going to bed.
gado ta hau tare da kashe bedside lamp ta ja duvet ta rufe jikinta da sannan ta lumshe ido trying to feel the moment har bacci ya d'auketa.
       it was a very beautiful morning with the sunshine shining on the curtains and kissing her face, da murmushi ta tashi ta y'ar miqanta mai kyau, babu tantama
kamar dai ta mance duk anunda ya faru jiya ta tashi ready for the dayfarin ciki neh fal zuciyarta saboda yau friday neh and by sunday zata wuce school, saukowa
tayi daga gadon tan sanya takalmi ta wuce bathroom, wanka ta fara yi kafin ta wanke bakinta ta fito, a gaban mirror ta zauna tayi switching hair dryer ta fara drying
kanta, a nutse tayi oiling bayan ta gama tayi packing abunta cikin ribbon mai kyau ta shafa mai, duk abubuwan da takeyi cikin farin ciki da annashuwa ta wuce closet
ta bud'e, tsayawa tayi da alamar tana nazarin me zata saka, wayarta dake kan gado ne ya fara ringing, a hankali ta juyo tana kallon wayan knowing Heenah ce zata iya
kiranta war haka, ignoring call d'in tayinta cigaba da kallon d'umbin kayan dake closet d'in, wani peach ankara neh ya d'auki idonta, sai da ta saki murmushinta mai
kyau kafin ta ciroshi daga inda yake sannan ta ciro matching veil sannan ta koma gaban mirror, powder ta d'auko tana shafawa ta sake jin wayarta na ringing for the second time,
y'ar tsaki taja a zuciyarta tace "this girl wouldn't just let me be" ta kare maganan pouting her lips just like a cute little baby, kin daukan  wayan tayi nan ma tayi concentrating
kan fuskarta, mascara tasa bayan ta gama shafa powder tasa wani peach lipstick da charpet, ita d'aya take ta fari da ido a mirror tana sake godewa ubangijinta for the gift of life
tashi tayi bayan ta karasa light make-up d'inta tana wakar brown skin girl, ta sa kayanta kenan wayarta ya sake fara ringing, da ihu tace "HEEENAHHH!"  kafin fad'a kan gadon ta d'auko
wayan ta kai kunnenta, ko sallama batayi ba tana ta harara kamar Heenan na gabanta tace "Heena wai meye na b'ata maki neh? why won't you leave me be neh wai, yo've been calling tun d'azu
without a break, must i pick your call? ko ke kika siya min wayan neh?" ta kare maganan tana dariya kasa-kasa, a d'ayan b'angaren Heenah ta kumbura kamar zata fashe don haushin rashin picking call d'inta
da Aaerat tayi and on top of that tana sake mata haka, "wai ke dan Allah meye haka neh, been calling you tun d'azu amma kika yi banza da kiran tsabar rashin mutuncin da kike ji dashi da safen nan koh, bama laifin ki bane
ai ni ce na damu dake har nake kiranki but i've learnt my lessons and from my mistake now and today will be the last day 'll ever call you" Heena ta kare maganan tana kiciniyar kashe wayarta, da sauri Aaerat tace "c'mon girlfriend, i was just
joking and you are already upset?, ke ba da gangan naki picking calls d'inki ba fah, i was taking my bath and you don't expect me to go to the bathroom with my phone do you?" shiru Heena tayi bata ce komai ba, hakan yasa Aaerat
ta gane cewa fushi take da gaske, murya can kasa tace "please baby girl, i'm sorry... you know my day can never be happy when you are upset with me, c'mon forgive your poor friend and let everything go away please" ta kare maganar kamar
zatayi kuka, wani numfashi Heena ta sauke on the other side da kamar bazata ce komai  bah sai kuma tace "staying at home a whole day day is very tiring my princess, you know we'll be leaving or school by sunday, let's go shopping please"
murmushi Aaerat tayi tace "Oh thanks for forgiving me, i know you won't say it don shegen girman kai bazai barki ki  bah,  anyways, let's go shopping sweetheart" da sauri Heenah tace " yanzu zan shigo coz i'm all ready, make sure you are done
before i arrive" Aerat na dariya tace "yes ma!" sannan tayi hanging up.
    Ba'a d'au 20 minutes ba Heenah tazo, Aaerat na ganinta ta fara dariya tace "ayawo kawai" wurgar da jaka da gyale Heenah tayi ta fad'a kan gado tana hararanta tace "whatever, ni dai kiyi sauri coz we have a lot to do out there" dariya kawai Aaerat
take mata tana cigaba da abunda takeyi, kallonta kawai Heenah keyi ganin she looks at ease and very happy today unlike the rest of the days she'll spend shedding tears and being unnecessarily  sad. Tashi Heenah tayi tazo har gabanta scanning her expression slowly for a moment
kafin tace "heyy, whats up with you? you seem so happy today, ko dai wani abun ne da ban sani ba ya faru?" dariya kawai Aaerat ke mata ta kare d'aura d'ankwalinta sannan ta tafi wurin shoe rack d'inta da d'auko wani peach color heel tasa, ignoring Heenah
tayi knowing very well that she needs an answer yadda take mata wani irin kallo mai d'auke da ayar tambaya, kofar parlor ta nufa ta k'ira maid dake duty safiyar, jiki na b'ari ta karaso ta durkushe wajen tana "barka da fitowa ranki ya dad'e" "kiramin Jameelah" kawai
Aaerat ta fad'a ta juya ta koma ciki, ba'a d'auki lokaci bah Jameelah ta shigo, tana ganin Heenah tayi saurin gaisheta ta d'auke kai, ita kuma Heenah ko kulata batayi bah, tura baki Jameelah tayi ta wuce wajen uwargijiyarta, zata durkusa Aaerat tayi saurin cewa
"no, there's no need for that, kiyi tsayuwarki" Jameelah tayi murmushi tare da sauke kanta kasa, juyawa Aaerat ta fara yi gaban Jameelah tana murmushi tana fari da idanu tace " how do i look Meelah?" ganin Jameelah bata d'ago ba yasa tayi saurin gane cewa bata gane
abunda take fad'a bah, girgiza kai tayi kafin tace "ko nayi kyau kuwa Jameelah?" sai a lokacin Jameelah ta d'ago kanta tana murmushi har yanzu tace "ai dama ke mai kyau ce gimbiyata, komai kika saka yana miki kyau yasa ki zamto kamar hasken farin wata" sosai Aaerat
taji dad'in comment d'inta sannan tayi dismissing d'inta. A qage Heenah ta taso ta isa wajenta tace "nifa kin sani a duhu my princess, tell me what you are up to please" ta k'are maganar kamar mai magiya, sai sannan Aaerat tayi deciding ta kulata tace "d'auko mayafinki mu tafi, i just have a feeling
that i'll set someone's soul on fire today...." tana gama fad'in haka tayi wucewarta, babu yadda Heenah ta iya, dole ta d'auki mayafi da jakarta tabi bayan Aaerat.

THIS CHAPTER IS FOR YOU AMRAH UTHMAN SALI {TUTUS} BABY GIRL, I LOVE YOU TO THE MILLIONTH ROOT OF INFINITY...

@Seembyluff❤

AAERAT (The princess of Binaaf) Where stories live. Discover now