Roman I

3.6K 185 20
                                    

🔘 *KULLU NAFSIN••* 🔘

      💥 *Fiction Story* 💥

*_By Miss Xerks_*🌺
*_Wattpad@ OUM-RAMADAN1433._*

*_Dedicated to my  Masoyiya Ummu Nabil💖_*

   🇳🇬®
*_ABORIGINAL WRITERS ASSOCIATION📚✍_*.
[❄Dance above the surface of the world. Let your thoughts lift you into creativity that is not hampered by opinion.]

_⚜{All’s well that ends well.}_⚜

*~In the name of Allah, the Entirely Merciful, the Especially Merciful.~*

'''①⓪/7/②⓪①9••⏰19:00ρm'''

                *Ꮢ-I*

_______📖"ehenn.... kuma dan ubanki yauma idan kinje makarantar ki zauna kamar yanda kika saba, kar Allah ya baki ikon dawowa ki kwana a hostel kiga yanda zanyi dake agidan nan wlh"

ta ɗago ta goge guntun hawayen daya sakko mata, durƙusawa tayi ta ɗauki jakarta sannan tabuɗa bakin da baya shiru tace,

"babu wanda ya isa yayi yanda yake so akaina sai yanda Allah ya tsara wlh"

"kut...ni kike faɗawa haka Nabila......"

ta katseta da faɗar,

"ai bawai na faɗa maki dan rashin kunya bane... no na faɗa maki yanda asalin zancen yake ne, babu wani bawa daya isa yay wa mutum abinda Allah bai shirya ba"

fuu tai gate, bata jira mai gadi ya buɗe mata ba tayi waje ranta duk a jagule.

waya tayiwa Maimunatu tace su haɗe a school ɗin kawai.

bata ɗau lokaci ba ta tari napep ta hau ya sauketa a gyaɗi-gyaɗi daga nan ta sake hawan motan da zai kaita KUST Wudil.

kusan awanta 2 a library  sannan ta fito, zip ɗin jaka ta zage ta ɗauko wayarta ƙirar iphone ta danna kiran Maimunatu.

bugu da bai wuce uku ba ta ɗaga, daga can ɓangaren Maimunatu tace,

"Lovely kina ina ne? tin ɗazun fa inata kiranki not recherble"

"na shiga libry amma gani na fito zanje bank mu haɗe a hanya"

a hanya suka haɗu nan suka ƙarasa bank, kuɗi Nabila ta cira suka juyo suka wuce terrace resturant.

bayan sun gama cin abinci suka ɗan taɓa hira daga bisani kuma suka miƙe zuwa enginerng depertment wurin ƙawarsu Munira.

Munira na zaune da wasu frnds ɗinta maza suna karatu ta hangi su Maimunatu, tasan Nabila ba lalle ne ta ƙaraso ba hakan yasa ita ta miƙe ta ƙarasa wurin nasu.

"oyoyo my stars" abinda tace tana rungumesu.

"enyen oyoyo... ƴan mata duk bokonce naga tasa kin ƙara duhu ne"

Nabila ta faɗi cike da tsokana idonta na kallon can wani gefe guda, ɗabi'arta ce magana ahaka ta faɗi abu amma tayi kaman bada kai take ba.

Munira tai ƴar dariya tace, "kedai Allah ya rabamu da boko lafiya....amma fa tana jaakamu da yawa ba ƙarya"

Maimunatu tai murmushi tace, "umm wai sunan ma bamu zurfafa ba ƴan read and pass ne mu"

"kedai bari kawai, Allah² nake ayi a wuce wurin yasin masters sai dai nayi a ɗakin mijina"

cewar Munira.

kallo mai kama da harara Nabila tai masu tace, "zancen kenan kullum...aure miji😏...ku bari ku kai matakin da kunfi ƙarfin raini da walaƙancin ɗa namiji tukunna ku fara zancen samari"

KULLU NAFSIN Completed.Where stories live. Discover now