🔘 *KULLU NAFSIN* 🔘
*1441H/2019M.*💥 *FICTION STORY.* 💥
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•🏇🏼_**BY MISS XERKS✍🏼.*
*WATTPAD@ OUM-RAMADHAN1433.**DEDICATED TO UMMU NABIL.*
*IN THE HONOUR OF:-*
*{ANTY NICE & BINTA G. DAUDAWA.}**[SPECIAL GIFT TO MAMAN JIDDA & MRS KHALEED.]*
~Wattpad @ GaskiyaWritersAsso.~
*~AL-LATIF:-THE KIND.~*
*Ꮢ-XXXII*
*32**__________📖* hannu yasa aljihunsa ya ɗauko wayarsa ya miƙa mata.
ta amsa tayi dialling numban Anty tajita a kashe, haka wayar Mommy ma a kashe,kota Kakus ma data kira duk a kashe ta jisu.
numban Maimuna ta danna, ita kuma sai dai ai tace mata not available wanda ta kira sama da sau goma, har numban Daddy ma not available, zata fara kuka cikin tausasan kalamai ya lallasheta.
"kar hankalinki ya tashi kinji, nan garin akwai matsala na network sose, so yanzu zan bar maki wayan a hannunki ko cikin dare sai ki kira by the time ma ƙilan sauran wayoyin sun buɗe".
ya bar mata wayan a wurinta ya miƙe ,ya kai bakin ƙofa tace dashi, "dan Allah ya sunanka?".
"Ramadhan".
"na gode Ramadhan da taimako na da kayi,Allah ya biyaka da alkhairinsa".ya amsa da ,"ameen". kana yasa kai ya fita.
har biyun dare tana ta gwada numbobin data haddace akanta amma babu wadda tayi sa'a ta samu ta shiga, anan ƙasa inda take ta ɓingile bacci ya ɗauketa.
da asuba kaman yanda yace da ita suka shiga da ita O Room, Face Mask ɗin da Nabil ya sanya yasa sam bata ganesa ba har yay mata aiki ya gama.
alhamdl cikin nasara da sa'a akai aikin aka gama.
kwananta biyu a asibitin kana Ramadhan yace to ta shirya ya kaita gida, daɗi fal ranta tinda ya faɗi mata bakinta yaƙi rufuwa,koda ya shigo yay ta tsokananta wai dama tana murmushi har haka.
hannu tasa ta rufe fuskarta tana ƴar dariya, kaɗan-kaɗan haka take jin gabanta yana faɗuwa.
"ki hanzarta ko kar mu rasa flight, in kin gama Nurse Bilkisu ta rakoki office ɗin CEO oak".
"tam shikenan".
tace dashi tana ci gaba da rolling mayafinta dan kwana biyun har sun saba da Ramadhan, tace masa Bro yace mata Sis.tana gamawa ta fito cike da ɗokinta yau zata koma gida, duk tsawon wannan lokaci ba ƙaramin dana sani take da barinta gida ba.
dalilin karayarta yanzu kam a hankali take ɗingisawa,Nurse bilkisu ce ta rakata har office ɗin kana ta juyo, Ramadhan na tsaye suna magana da Nabil ta shiga.
jin sallamarta Ramadhan ya jiyo yana mata nuni da kusa dashi.
ta ɗan rissina tace da Nabil, "ina yini Dr".ci gaba yayi da rubutun da yake ajikin wani file bai amsa mata ba,Ramadhan yace dashi, "Brother ana gaida ka".
still kansa na ƙasa yace, "lafiya". yaci gaba da rubutunsa.
"kina ta murna zaki gida ko".
Ramadhan yace da ita cike da zolaya.
ŞİMDİ OKUDUĞUN
KULLU NAFSIN Completed.
Tarihi KurguDukkanin mai rai mamaci ne...kuma haƙiƙa mutuwa bata taɓa barin wani dan wani yaji daɗi...ku biyoni dan jin yanda wannan labari nawa zai kasance wanda yazo da sabon salon da ba'a fiya yinsa ba.