Roman 14 [XIV]

728 64 9
                                    

🔘 *KULLU NAFSIN* 🔘

💥 *Fiction Story* 💥

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }

'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼


*_By Miss Xerks_*🌺
*_Wattpad@ OUM-RAMADHAN1433._*

*_Dedicated to my Masoyiya_*
*_Ummu Nabil💖_*


~Al-вααríч:-thє mαkєr.~

'''⓪5/11/②0①9••⏰20:00pm'''

~Wattpad @ GaskiyaWritersAsso.~

*Ꮢ-XIV*

*__________📖* tsayuwar parking ɗinsa a matanadin motoci Aisha tazo ta tarbesa tare da tambayansa ko akwai abinda zata ɗaukar masa.

ciki-ciki ya amsa mata da, "babu, ko ce miki nai nayi bulaguro"

"um-um"
ta amsasa, yay gaba ya barta tsaye tai saurin binsa tare da kamo hannunsa.

"Handsome dan Allah ka saki fuskanka dan darajan yarusilillahi, kaga Momma fa tazo tana ciki, bana son abinda zai jawo tama faɗa"

ya ɗan kalleta ya basar, hannu yasa cikin aljihunsa ya ɗebo wayoyinsa ya damƙa mata a hannu.

ta amsa sukai jera tare suna tafiya har cikin parlo.

kujeran kusa da Momma ya zauna, sannu da zuwa yay mata tare da gaisheta.

"lafiya" tace dashi tana kamo kunnensa ta murɗe.

"kai yanzu haka akeyi tsakani da Allah, yarinya ba lafiya ka tashi ka fita ka barta ita ɗaya acikin gida, inace ba yau sunday bane, ko kaine uban ƴan aiki na duniya aika huta"

ɗagowa yay ya duba Aisha dake kallonsa tana wasa da hannu, tasan sam bai gane kan zancen ba dan haka tai saurin bada amsar, "Momma maganin yaje sayowa ai"

shidai Nabil ya ƙagu Momma ta saka masa kunne dan murɗewar data masa da zafi, tana ce masa, "wai haka ne?"

yay saurin ɗaga mata kai, "ehh ehh Momma hakane"

dariya su Jiddah da Hamida suka sanya ganin yanda ya amsa da sauri yana janye hannun Momma a kunnen.

Momma ta jima gidan dan sai kusan magriba Ramadhan yazo ya ɗaukesu, ta jaddadawa duk su biyun kan su kula sose dan shi ƙaramin ciki ba'a wasa dashi, kuma duk wasu aikace-aikace Aisha ta daina zata ma Yafindo waya a samo me aiki acan ruga.

bayan sun dawo ciki daga rakiyan su Momma ya dakatar da Aisha yana binta da banzan kallon tuhuma kamin ya buɗa baki yace da ita,

"wa yay maki ciki? kona ce cikin wane ajikinki?"

yanayin tambayar tasa ba ƙaramin dukan kanta yayi ba, baki na rawa tace dashi, "kaman ya waya yi min ciki, ina da wani miji bayan kaine?"

"kusan hakan, tinda ni wata mu'amala bata taɓa haɗani dake ba sai jiya, to taya za'azo min da zancen rainin wayon cewan kina da ciki wanda har ya bayyanar da kansa aka gane"

ƙwalla tap a idonta tace, "kana zargina kenan akan bin wasu mazan?"

"ba zarginki nake ba, gaskiyar zancen kenan, idan kin haife ki miƙa ma ubansa shi domin baza'a min rainon shege acikin gida ba.... thank God bana jin komi agame dake bare hakan ya dameni"

KULLU NAFSIN Completed.Where stories live. Discover now