Roman 49

802 85 29
                                    

*🔘KULLU NAFSIN🔘*
      *1441H/2020M.*

     *💥FICTION STORY.💥*

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

            '''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•🏇🏼_*

*BY MISS XERKS✍🏼.*
🅖🅦🅐 ᏟᎬᎾ.
*WATTPAD@ OUM-RAMADHAN1433.*

*DEDICATED TO UMMU NABIL.*

*IN THE HONOUR OF:-*
*{ANTY NICE & BINTA G. DAUDAWA.}*

*WATTPAD:-* GaskiyaWritersAsso.

*G-MAIL:-* gaskiyawritersassociation@gmail.com.

*TWITER:-* https://twitter.com/GaskiyaWriters?s=09.

                     
15readmore/1391Words.

                     *Ꮢ-IXL*
                         *49*

*__________📖* "Kayi haƙuri, amma kasan ko muso ko kar muso dole mu rabu da juna, bana son abinda zai haifar mana da rashin samun kwanciyar hankali daga ni har kai shi yasa nace ka fita a rayuwa ta.....
Yanzu dai ba wannan ba, ya sauƙin jikin naka?".

"Babu sauƙi".
Ya bata amsar a taƙaice kuma cikin fushi.

"mi yasa zaka ce haka?, aiko babu haka ake cewa alhamdulillahi da sauƙi".

"to mai kike so nace maki banda haka, tunda baki damu dani ba, ko waɗanda basa sona suna zuwa duba ni amma banda ke, na mutu ko na rayu wannan duk ba damuwar ki bane".

"kayi haƙuri idan na sami chance zan zo, amma ni kam dai ka daina faɗin cewar bana son ka, kar ka manta fa kai mijin Yayata ne wacce banda tamkar ta".

Magana ce take yinta a sanyaye idanunwan ta a cike da hawaye.

Bai kuma ce mata komi ba yayi shiru har sai data katse shirun nasa da cewar,

"sai anjima, dama sun fito zasu tafi ne, bari na basu wayar kar na tsaida su dare nayi, ka kula da kan ka kaji".

Ƙala baice mata ba kusan minti uku tana jiran cewar sa, haka ta haƙura ta kashe wayar ta miƙawa Munir.

Cike da jin haushin sa ta shigo ɗaki, tsaki tayi ta jefar da mayafin ta kamin ta zauna kan gadon, lallai ma wannan mutumin, mai yake nufi da ita, nufin sa ita bata jin irin raɗaɗin da yake ji ne?, ko kuma tana ganin abinda Allah ya haramta zata take don farincikin sa?, ko kuma zata zaɓi farincikin sa akan na mahaifin ta?, "mtswww". Matsalar data haifar ma a tsakanin iyayen ta kaɗai ya ishe ta, dalilin wannan abun yanzu ko magana Daddy da Mommy basa yi, bare kuma Daddy da Kakus dako gaisuwar sa sama-sama take amsawa, Ta kuma jan tsuka "rayuwar duk babu daɗi".

Dama tana fashin sallah don haka tai kwanciyar ta, ba abinda ya faɗo mata sai gargaɗin da Aisha ta kuma mata na jiya a text, muddin bata bar mata miji ba to tana mata rantsuwa da wanda ya busa mata rai sai ta kashe ta sai taga bayan ta, Nabil nata ne ita ɗaya.

Haushin kanta taji da bata mayar mata da martani ba, koda yake idan ta biye ta zasu kwashi ba daɗi duk da cewar bata cikin hayyacin ta yanzu, ƙoƙarin ta warware wannan cakwakiyar, aikin banza mijin ma da take taƙama da shi ai ba sonta yake ba, kuma auran sa sai dai idan ita tace ta fasa, amma wallah ta bari ta kaita bango babu fashi don babu wanda ya isa ya rabata da Nabil, yanda take tunƙaho tana da Daddy haka itama tana da Kakus, ba don tana son kwanciyar hankali ba yanzu sai ta birkicewa Kakus taga ta ƙarya kumfar bakin da take akan zata kasheta tunda ita mahaukaciya ce.

KULLU NAFSIN Completed.Where stories live. Discover now