Roman VI

886 72 12
                                    

🔘 *KULLU NAFSIN* 🔘

      💥 *Fiction Story* 💥

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }

         🎐 '''G•W•A'''🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼


*_By Miss Xerks_*🌺
*_Wattpad@ OUM-RAMADHAN1433._*

*_Dedicated to my  Masoyiya_*
*_Ummu Nabil💖_*

⚜ _Duk wani mai baƙin ciki rayuwarsa zata dawwama cikin lalura👌_.⚜

~Aѕ-ѕαlαm:thє pєrfєctíσn αnd gívєr σf thє pєαcє.~

'''①8/8/②0①9••⏰21:30pm'''

~Wattpad @ GaskiyaWritersAsso.~

_єdítєd👁‍🗨._

                     *Ꮢ-VI*

__________📖gaba ɗaya yinin wannan rana haka Nabil ya kasance cikinta a sukurkuce, tin safe daya shiga ɗaki bai buɗe ƙofa ba sai after magriba dan ko masallaci bai je ba.

shi damuwarsa ba auren bane, wa kuma yanzu za'a sake bashi matsayin mallakinsa?, shin sai yaushe ne zai sami ƴancin kansa ya kawo matar da yake so su shimfiɗa asalin rayuwar aure da ita shima yasha zumar da ake samu acikin wannan rayuwa.?

baya da amsar tinaninsa hakan yasa ya miƙe ya shiga toilet ya sakarma kansa shower.

Aisha ma haka ta ƙaraci buge-bugen ƙofan room ɗinsa ta haƙura ,sai dai hankalinta tashe yake duba da halin da mijinta ya shiga na damuwar da bata sani ba.

shiru ta zauna tana ta saƙe-saƙe cikin ranta, ta kawo wancan ta kawo wannan, ƙarshe dai ta miƙe ta ɗau waya dan ta kira Papa taji ko yasan mi ya faru tinda daga wajensa ya dawo.

ta ɗau waya zata kira sai kuma taga ba dacewan hakan, dan haka ta haƙura ta zauna ta rafka tagumi tana adu'an Allah yasa koma mine ne ma ya zama mai sauƙin war-warewa.

har isha'i tana zaune nan parlo gyan-gyaɗi ma ya fara ɗibanta, sam bata san da fitarsa ba saboda ta ƙofan baya ya fita sai yanzu daya shigo ta main parlo.

gyan-gyaɗin data ke ne ya katse lokacin da hayaƙin wutar ƙamshin tiraransa ta gama cika ɗakin, da sauri ta miƙe tasha gabansa tare da rungumesa tana ɗan kukan shagwaɓa.

bai motsa ba ko yinƙurin yin wani abu kawai yay tsaye a sojansa, ta ɗago da kai idanunta cike da hawaye tana shafo fuskarsa.

"Handsome ɗina wai miya faru? ,mine ya saka min kai acikin damuwa?, kasan bani son abinda zai taɓa min walwalanka ko kaɗan, ko nice na maka abinda bakaji daɗi ba a tarban da naka maka ɗazun?".

duk cikin rauni da tashin hankali gami da shagwaɓe fuska take ta maganar.

shiru baice mata ƙala ba sai bin idanuwanta da kallo da yake cike da tausayawa duk da tsanarta data gama cika zuciyarsa.

baya son Aisha ko kaɗan kuma bai san ta yanda zai fara ba tinda shi so ba'a tilasta masa, amma to ya zaiyi dole ya zauna da ita tinda zancen mahaifiyarsa a koda yaushe shine matarsa ce farin cikin ta.

to amma kuma haƙƙin  ta daya ke ɗauka kullum pa, shi yana ƙoƙarin jurewa amma shin ita ya take da tata sha'awar da yake gani ƙururu acikin idanuwanta duk sanda tsau-tsayi yasa ya kalla idonta.

"mi ka gani a wayanka wanda ya saka cikin damuwa? dan na lura da hakan tin daga lokacin daka karanta saƙon daya shigo cikinta".

murfayen idonsa ya haɗe wuri ɗaya na ƴan second sannan ya buɗa tare da jan hannunta zuwa kan kujera.

KULLU NAFSIN Completed.Où les histoires vivent. Découvrez maintenant