🔘 *KULLU NAFSIN* 🔘
*1441H/2020M.*💥 *FICTION STORY.* 💥
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•🏇🏼_**BY MISS XERKS✍🏼.*
*WATTPAD@ OUM-RAMADHAN1433.**DEDICATED TO UMMU NABIL.*
*IN THE HONOUR OF:-*
*{ANTY NICE & BINTA G. DAUDAWA.}**[SPECIAL GIFT TO MAMAN JIDDA & MRS KHALEED.]*
~Wattpad @ GaskiyaWritersAsso.~
*~AL-HALIM:THE INDULGENT.~*
'''DEDICATED TO SARDAUNA MY CIWON KAI, BA DON HALIN KA BA.'''
*Ꮢ-XLII*
*42**__________📖* murmushi yayi wanda ya fidda sauti, hannun nata ya kama ya sauke daga saman fuskar, idon ta na kallon ƙasa take jin wani irin sanyi na ratsa zuciyar ta.
shi ko fuskarta kawai yake bi da kallo kaman yau ya taɓa ganin ta, katse shi tayi da zame hannun ta cikin nasa tace da shi,
"kayi haƙuri kar ka cinye mani ɗan guntun kyan nawa".
"hmmm".
shi ne abinda ya faɗi yana murza idanun sa bayan ya miƙe daga duƙen da yake."ka zauna mana".
"um-um ki dai sauko ƙasa mu zauna tare, zan fi jin daɗin hirar da ke".
murmusawa tayi ta ta shi ta ɗauko carpet ta war-ware shi ta shimfiɗa.
zama yayi ita kuma ta nufa tray ta ɗauko kayan tarbar da ta tanadar masa.ruwan faro ta buɗa ta zuba cikin cup ta ijje gaban sa tare da faɗin,
"barka da zuwa ya hanya?".
yana kallon ta yace, "alhamdulillahi".
sannan ya ɗauka cup na ruwan ya sha.
warm coolers ɗin abincin ta janyo zata zuba masa, ido ya waro waje yace,
"Nabila duk wannan abincin a ina?".
"a cikin ka mana".
ta faɗi tana zuba farfesun kayan cikin a wani madai-daicin bowl.duk abinda ta dafa sai data zuba, shi ko kallon ta kawai ya keyi, ko aina zai sanya su oho ta dage tana ta zubawa, hannun ta riƙa yace,
"Mah Heart Beat plsss ki bar sa haka,walla ni kusan ma a ƙoshe nike, kuma koda ba haka ba wannan abincin kam ai yay ma ciki na yawa".
galala ta kalle sa tace, "what ka ke nufi da a ƙoshe ka ke?".
"munci abinci a jirgi....".
"koma aina kaci wannan dabanne, in kuma abincin dana dafa da hannu na ne baza ka ci ba tau sai naji?".
ta ƙarasa tambayar tata a shagwaɓan ce.
saurin kaɗa kai yayi tare da ce mata, "no ba haka bane, zuba zanci nayi taci har sai ke da kan ki kin ɗauke plate ɗin".
sai data saki murmushi kana ta ƙarasa war-ware samosa ɗin da tayi folding nata a paper.
duka ta ijje a gaban sa haɗe da cewa, "to bismillah".
YOU ARE READING
KULLU NAFSIN Completed.
Historical FictionDukkanin mai rai mamaci ne...kuma haƙiƙa mutuwa bata taɓa barin wani dan wani yaji daɗi...ku biyoni dan jin yanda wannan labari nawa zai kasance wanda yazo da sabon salon da ba'a fiya yinsa ba.