🔘 *KULLU NAFSIN••* 🔘
💥 *Fiction Story* 💥
*_By Miss Xerks_*🌺
*_Wattpad@ OUM-RAMADAN1433._**_Dedicated to my Masoyiya_*
*_Ummu Nabil💖_*🇳🇬®
*_ABORIGINAL WRITERS ASSOCIATION📚✍_*.
[❄Dance above the surface of the world. Let your thoughts lift you into creativity that is not hampered by opinion.]_⚜{dσnt вítє thє hαnd thαt fєєdѕ чσu.}_⚜
~Ar-rαhєєm: thє σwnєr σf mєrcч thαt єncσmpαѕѕєѕ híѕ crєαtíσn.~
'''①9/7/②⓪①9••⏰15:40pm'''
*JAMA'AT KAREEM 2OLL MUSLIM UMMAH🕌.*
''' Եհҽ Թɑցҽ íՏ ժҽժíϲɑԵҽժ Եօ վօմ ʍɑʍɑղ յíժժɑԵմӀ-Ƙհɑíɾ & ɑƒƒɑղ.'''
_nσt єdítєd⭕._
*Ꮢ-III*
_______📖Alhji Muhammad Shamsuddeen Shattima shine minister of budget and national planing na nigeria, matarsa ɗaya Hajia Hafsat ita kuma babbar lecturer ce a Bayero university sai yaransu huɗu da suka haifa.
Nabil, Ramadan,Jiddatul-khair sai autarsu Hamida, ƴan uwane da suka taso cikin so da ƙaunar junansu.haka ma mahaifansu na matuƙar ji dasu babu abinda suka nema suka rasa.
anama Hajiya Hafsat laƙabi da Ummu Nabil shi kuma Papa ake masa laƙabi da Abu Nabil.
Nabil shine Babban ɗa a wurin mahaifansa, tin Nabil na ƙarami yake da sha'awar karatun engineer har ya girma yakai matakin shiga jami'a daga nan kuma ya sami banbanci ra'ayi daga wurin iyayen nasa saboda kowanne da abinda yake so Nabil ya karanta.
tinda Momma ta haifi Nabil ta ƙudurce a ranta insha'Allahu watan wata rana sai ɗanta ya zama conel ta gansa cikin kakin soja yana taimakon al'umma, inda shi kuma Papa yake bala'in son ɗansa ya zama cikakke kuma ƙwararren likita dan ya zama mai ceton rayukan al'umma musamman daya ga yaron nada baiwar ilimi.
rigima ce taso ɓarkewa tsakanin Papa da Momma saboda kowanne ce yake ai ɗansa dan haka abinda yake so ɗansa yayi shi zaiyi, ɓacin rai har taso ga kai Papa ya saki Momma amma saboda Nabil yaro ne mai hanƙali da sanin ya kamata sai yace masu zaiyi karatun duka kar hakan ya damesu, to duk da hakan ma anan ɗin sai da suka haura sabida Momma cetai sai dai ya fara nata kamin ya fara karatun medincine.
to cikin taimakawar ubangiji Nabil ya fara da karatun medicine ɗinsa a american university washington, batare da Momma ta sani ba ya haɗa karatu biyu alokaci guda yana medicine yana engnerng harya kammala sannan daga baya kuma ya wuce yay aikin soja.
bayan dawowarsa daga america lokacin ya kammala wani course anan yazo ya tarar da gift ɗin Momma data tanadar masa na matar dazai aura.
Aisha Shattima sunan yarinyar ɗalibar Momma ce, hazaƙa da tarbiya irin na Aisha yasa Momma ke masifar sonta har taji taima ɗanta sha'awar auranta.
kamin dawowarsa Momma ta sanya Papa sukaje aka nema masa aurenta aka kuma bashi duk batare da saninsa ba.Nabil bawai ra'ayin mata ne baiyi ba kawai dai shi yarinyar ce bata masa ba kuma batai dai² da ra'ayinsa ba ,danshi a rayuwarsa yana son mace mai tsiwa sannan kuma irinsa wadda bata ɗaukan rainin kowa ,duk daya nunawa Momma cewan bai son auren amma taƙi tace dole sai ya aureta tinda harta zama zaɓinta.
itako Aisha tin a hoto data ga Nabil taji ta aminta dashi har ranta musamman data kuma gansa a zahiri, lalle Nabil ba namijin da mace zata gani taso ƙyalewa bane.
YOU ARE READING
KULLU NAFSIN Completed.
Historical FictionDukkanin mai rai mamaci ne...kuma haƙiƙa mutuwa bata taɓa barin wani dan wani yaji daɗi...ku biyoni dan jin yanda wannan labari nawa zai kasance wanda yazo da sabon salon da ba'a fiya yinsa ba.