🔘 *KULLU NAFSIN* 🔘
*1441H/2020M.*💥 *FICTION STORY.* 💥
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•🏇🏼_**BY MISS XERKS✍🏼.*
🅖🅦🅐 ᏟᎬᎾ.
*WATTPAD@ OUM-RAMADHAN1433.**DEDICATED TO UMMU NABIL.*
*IN THE HONOUR OF:-*
*{ANTY NICE & BINTA G. DAUDAWA.}**[SPECIAL GIFT TO MAMAN JIDDA & MRS KHALEED.]*
~Wattpad @ GaskiyaWritersAsso.~
*~ASH-SHAKOOR:-THE MOST APPRECIATIVE.~*
3985words.
20148 characters with spaces.
16250 characters no spaces.*Ꮢ-XLV*
*45**__________📖* "yauwa ko kefa".
haka Nabil yaci gaba da lallame ta da kalamu ka masu daɗi har ta sauko ta haƙura, sai daya tabbatar ta daina fushin kana yace mata.
"wai HeartBeat zaki iya aika ta abinda kika ce jiya?".
ɗan yatsine fuska tayi tace, "hmmm Dee kenan, kasan Allah a yanda nike jin zuciya ta jiya babu abinda ba zan iya aikatawa saboda ina da tsananin kishi, sai a jiya na ƙara tabbatar wa da ina son ka, amma daga jiya zuwa yau wannan son na ka ya ragu".
ta ƙarasa faɗi tana ɗan ɓata fuska.
Murmushi mai fidda sauti ya saki ya lakuci hancin ta, harar ƙauna ta watsa masa sannan ta miƙe tace da shi,
"kasan mi Dee, na yarda da duk abinda kace mani amma ban yarda da cewan baka son matar ka ba, kai dai kawai kace kowa da matsayin soyayyar ta a zuciyar ka, amma batun cewa zaka ninke ni da faɗin baka son matar ka ban yarda ba, yanzu dai ta shi ka koma parlo tunda na haƙura".
"hakan ma babu laifi tunda dai Allah yasa kin gane cewar da gaske ke ɗin kece a zuciya ta".
"ka ta shi ka fita kar Kakus ta dawo ta same ka anan".
"ko ta dawo babu abinda zata ce domin ita ta bani izinin shigowa na lallashi bugun zuciya ta"."hmmm". shine abinda ta faɗi sannan tai hanyar ƙofa ta fita ta barsa a ɗakin.
tana fita ya sauke nauyayyar ajiyar zuciya taɗe da numshe idon sa, bai taɓa tunanin zai iya shawo kanta da wuri haka ba.
sai kuma ya saki murmushi ya miƙe shima ya fita yana saƙa abubuwa da dama a cikin ransa na game da auran su.lokacin daya fito tana kitchen, kusan 5mints da zaman sa sai gata ta fito cikin takun yangar ta mai ɗaukan hankalin sa, tunda ya ɗora idon sa akan ta koda ƙiftawa ya kasa yi, ita kam idon ta a ƙasa take takowar saboda idon sa har tana jin kawa zata faɗi, sai data ƙaraso gare shi tasa iskar bakin ta ta hure masa ido.
"yallaɓai kallon ya isa haka".
ido ya lumshe ya buɗe yana murmushin leɓe yace, "HeartBeat ena bana gajiya da ganin ki ko kaɗan, komi naki mai kyau ne ke har kinfi ma shi kan sa kyau kyau".
ido ta ɗan waro tana ƴar dariyar data bayyanar da haƙoran ta tace,
"hmmm na gode".
cike da zolaya kuma sai yace, "amma fa duk kyawun nan naki baki kai matata ba".
YOU ARE READING
KULLU NAFSIN Completed.
Historical FictionDukkanin mai rai mamaci ne...kuma haƙiƙa mutuwa bata taɓa barin wani dan wani yaji daɗi...ku biyoni dan jin yanda wannan labari nawa zai kasance wanda yazo da sabon salon da ba'a fiya yinsa ba.