No 3

1.7K 39 1
                                    

[10/29, 08:04] Sumayya: 💦💦💦💦💦💦💦
              💦💦💦💦
                      💦💦
          

     *KAWAR* *'YATA* *CE*


®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }

         🎐 '''G•W•A'''🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*Story & written*
           By
        *Sumy*✍



*BISMILLAH RAHAMAR RaHIM*

       *Page* 1⃣5⃣

Tunda safe Hajiya Sa'a ta shirya taje gidan Hajiya Ummu, koda taje a d'akin da Fateema take acan tasamu Hajiya Ummu, tana k'ara gyaran ta.

Bayan sun gama gaisawa sai Hajiya Sa'a "tace Fateema ke kika ba Zainab number ki?".

Fateema "tace a'a Hajiya bani nabata ba".

Tace "to sai in shi  Mansur d'in yabata?"

Fateema tace, "wallahi bansani ba".

Sai Hajiya Sa'a tace  ma Hajiya Ummu, "kinsan gobe ne zasu wuce."

Hajiya ummu tace, "ina sane shiyasa nak'ara k'ok'artawa kafin gobe mukammala komai".

Sai Hajiya Sa'a tace," yauwa."sannan ta mayar da kallon ta ga Fateema taci gaba da cewa," kina bukatar wani Abu? dan kila har gidan ku zanje."

Fateema tace," a'a Hajiya, ki dai ce ina gashesu.

Hajiya sa'a tace," insha Allah zangaya musu".

Hajiya Sa'a da fitar ta,bata tsaya ko inaba ba sai gidansu Fateema.

Da fara'a Ummu Fateema ta tarb'e ta.

Bayan sun gama gaisawa, Hajiya Sa'a tafad'ama ta tafiyar Fateema gobe.

Mahaifiyar Fatima tayi murmushi, sannan tayi musu  fatan alhairi.

Mik'e wa tayi ta d'auko wasu Kaya aleda ta mik'awa Hajiya sa'a tace,"ga sak'o ki Kai wa fatima.

Hajiya sa'a ta amshi kayan, sannan sukayi bankwana ta tashi ta tafi.

Ab'angaren su Mummy tunda safe taje gidan Hajiya Safa,basu b'ata lokaci ba suka kama hanya sukaje wurin malamin su.

Koda sukaje mutane sunyi yawa, sai da suka bari mutane sun rage sannan suka shiga.

Bayan sun kai gaisuwa gareshi sannan suka k'ara kora musu bayani, Hajiya Safa tace, "Malam gamida maganar da kasani ce har yanzu abu yak'i k'arewa.

Malam Yayi murmushi irin na mayaudaran malamai yace,"ku tsaya na duba maku na gani."

Wani babban faranti yajawo wanda aka zuba yashi aciki.

yatsun hannun sa d'aya, yasa yafara layi _layi, jin kad'an kana yad'ago ya kallesu yace," gaskiya gamida ita Fateema, akwai wani b'oyayyen wani abu, wanda nakasa ganin miye shi, amma kubari nan da kwana biyu kuda wo, amma gami da wannan auren da kuke tsammani, to baza'ayi shi ba, amma kusa ido kuyi kallo".

Sukace," to Malam, dan Allah ak'ara dubamana, dan Yanzu ma haka sun d'auke ta daga gida, kuma Malam, dan Allah ina son acire son da 'yata Zainab kema Fateema, saboda abun nadamu na.

Malam  yace,"bakida matsala.

Wani d'aurin magani yabata, yace kizoba mata ga abinci ko lemu tasha ki tabbatar da tasha shi.

ƘAWAR ƳATA CE                              {COMPLETED 01/2020.}   Where stories live. Discover now