11

862 40 0
                                    

💦💦💦💦💦💦💦
            💦💦💦💦
                        💦💦

*ƘAWAR ƳATA CE*
       *1441H2019M.*


®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da lahira}_

     '''🎐G•W•A🎐'''
_*GASKIYA DOKIN ƘARFE•*_

Story & Written
         By
*SUMY M NA'IGE*✍🏻


'''Didicated''' to....
*My Sweet nah*🥰🥰



~VOTE & FOLLOW 4 Wattpad@GaskiyaWritersAsso.~




*Page* *39*




*_________*📖 Fatima tafiya tayi ta shirya suka fita basu tsaya ko ina ba sai gidan iyayen ta.


Sai da suka bari Daddy ya fita suka zo wajan Momy suka tsare ta suna kuka,wai su basu shirya aure yanzu ba.

Momy duban su tayi da muryar rarrashi kana tace,"kuyi hak'uri ku daina kuka ku bani kwana biyu dan wallah ina tabbatar muku tunda tasa  ko kuka, sai tayi wanda ya fishi kunji dan haka ku tashi kuyi abunda ke gaban ku kunji".

Duban ta ta kai  ga Maram kana tace, "ke kuma ki tashi ko kama hanya dan nasan keda kaiwa sai cikin dare dan haku ku tashi Allah ya tsare".

Duban Momy tayi tace, "to yanzu wani mataki zaki ɗauka akan wannan yarinyar?".

Sai da Momy ta numfasa kana tace, "nariga na ɗau mataki kuma cikin kwana biyu komai zai dawo muna dai-dai dan haka ku tashi kutafi".

Tashi tayi suka ɗaukar mata kayan ta suka kai har  mota kana ta shiga driver ya ja suka tafi.

su kuma suka dawo gida duk ba daɗi a zukatan su.

Tana shiga gida kenan ƙannen ta saka fara yi mata "oyoyo ga Aunty Fatima ta zo".


Bata tsaya bin ta kansu ba,dan ɗan gudun ta ta ƙarasa ɗaƙin Umma ta.

Tana zaune ta nike kayan shanyar da ta kwaso,jitaya anfaɗi jikin ta ana faɗin, "Umma tah".

Ɗugo kai tayi ta kalle ta tace, "wai Fatima yaushe za kiyi hankali, ke baki san yanzu kin girma ba?"...ta kai ƙarshin maganar tare da faɗa-ɗa  murmushi a fuskar ta.

Aikuwa yaran gida sai turu-ruwar zuwa ganin ta suke.

Duk murna ta cika ta tama kasa tashi daga jikin Ummah,sai da Ummah ta tace, "to basu ko minti ne kafin su tafi naga suna ta zowa gaisheki ke ko sai hauka kike yi".


Jikar ta ta buɗe ta ɗauko bandur ɗin ƴan hamsin ta fara  raba musu tare da haɗa musu da minti me tsinke.

Akuwa zo kuga murna wajan yara ba'a cewa komai.

Ba ɓata lokaci kowa yasan Fatima ta zo.

Labarin zowan Fatima yana kaiwa ga Hajiya Amo aikuwa ba shiri ta tashi tafara kunfar baki tana faɗin,"shigeyar yarinya taji daɗin aure shine har da raba ƴan hamsin.🤣

Ko tazo ta gaisheni haka ta ƙarasa ɗakin Ummar Fatima tanata sababi.

Sai da taga ma cima Ummah mutunci kana ta dawo ga Fatima   amma du kan su ba wanda yaci mata komai.

Da Fatima ta gaji da faɗan ta bandur ɗaya ta dauko na ƴan ɗari ta ba Hajiya aikuwa lokaci ɗaya ta fara washe baki kana tafara cema Fatima,"ina kika bar Alhaji ?shine ko kije ki gaisheni".

ƘAWAR ƳATA CE                              {COMPLETED 01/2020.}   Where stories live. Discover now