No 20

984 34 2
                                    

💦💦💦💦💦💦💦
           💦💦💦💦
                      💦💦







*ƘAWAR ƳATA CE*
    *1441H/2019M.*


®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da lahira}_

     '''🎐G•W•A🎐'''
_*GASKIYA DOKIN ƘARFE•*_



Story & Written
         By
*SUMMY M NA'IGE*✍🏻


*Didicated to*
  *Family*😘


~VOTE & FOLLOW 4 Wattpad@GaskiyaWritersAsso.~



*Page 47*


*_________*📖 Kafin suyi mata magana tace, kone ƴan uwan Fatima ?".


Kaka Amo tayi sauri tace ta haihune?".

Sai nurse  ɗin tace "eh ta  haihu amma bazan faɗe me aka samu ba sai kun ban goron albishir".



Rigan-gan akayi wajan bata Daddy da Hajiya Sa'a,Daddy kuɗe ya bata masu yawan gaske wanda shi kansa bai san yawan su ba.

Hajiya Sa'a ma haka,ita kanta nurse ɗin abun ya bata mamaki sosai godiya ta musu kana tace musu "an haife kyawa-wan twins maza gasu can ana gyaransu bari na ɗauko muko ku gani".

Ai tun bata rufe bakin ta ba Daddy ya fara yiwa Allah kirari yana masa gode akan kyautar da ya bashi.


Itako Hajiya Sa'a har da biye ma Kaka Amo tayi wajan rawa sunayi suna godeya ga Allah da ya sauke ta lafiya.


Hajiya Sa'a kiran ƴan uwa da abukan arziki tayi ta faɗa musu suma sun taya su murna sosai.


Suna cikin haka sai ga nurses sun fito kowace ɗauke da daya ahannun ta.

Da sauri suka ƙarasa garesu suka karɓe yaran suna murna.

Sai da suka gama gani Daddy ya karɓa yayi musu huɗe  kana yasama rayuwar su albarka ciki da so da ƙaunan yaran.

Nurse ɗin ya kalla yace "ina ita Mamar su?".

Sai nurse ɗin tace "tana ɗaki tana hutawa amma zaga iya shiga ka ganta".



Tun bata refe baki ba Daddy yace "muje ki kaini".


Suma su Hajiya Sa'a da Kaka Amo bin su sukayi ɗakin da Fatima take.


Kuda suka shiga tana zaune saman gado kamar ba ita ce Daddy ya ɗauko ba rai a hannun Allah.

Ƙarasuwa sukayi wajan ta suka fara yimata yajiki .

Bayan ta amsa suka bata yaran da ta haifa tagani amma saboda kunya cemusu tayi ta gansu.

Da ƙyar suka samu ta karɓa yaran.

Bayan awa biyar aka sallame ta dan ba abunda ke damun ta sai rashi ƙarfin jikin da bata da, koshi sunce zowa wani lokaci zataji ta dai-dai.



Gaba ki ɗaya Daddy ya manta bai kira Mumy ya faɗa mata ba.


Hajiya Shafa ce ta kira ta dan suma har sunji labarin haihuwar  Fatima ransu baiyi daɗe ba dan ba haka suka so ba.


Dan kishayar ta Nafisa har rawa sai da tayi ita da sauran amaren saboda murna.


Sai da takira har sau biyu kana Mumy ta ɗauka dan tana ɗaki tana bakin cikin zowan Daddy gida dan son tayi abar ta har ta gama shan woya kafin akai ta hospatal  kafi wani lokaci komeye acinkin ya mutu.


Tana cikin haka wayar ta ta fara rura har taso taƙi ɗagawa amma data ga andame ta dakira dan haka ta ɗauka.

Sunan Hajiya Shafa tagani dan haka tayi sauri ta kara akunnen ta.


Bayan sun gaisa sai Hajiya Shafa tace "ko har dake kuna hospatal?".


Sai Mumy tace "warin me?".

Sai Hajiya Shafa tace, "au baki masan ki shiyarki ta haihuba kenan dan naga ko kiran mu bakiyi ba".



Tana cewa haka sai da gaban Mumy ya faɗ baki na karkarwa Mumy tace "yaushe ta haihu kuma  me ta haifa, taƙara da cewa nasan kome ta haifa ya mutu".


Sai da tagama jerama Hajiya Shafa tambayoye kana ta buɗe baki tace "ko ɗaya dan niman yanzu naji mutumi  yar ta ta fito tana guɗa tana rawa wai anhaifar musu ƴan biyu kuma gaba ɗayan su maza ne".


Ai tun Hajiya Shafa bata kai ƙarshin zancin ba Mumy ta sake waya ta faɗi ƙasa tace tas...

Tan gaɗi ta farayi kamar zata faɗi,kujerar dake kusa da ita tariƙe kana ta fara magana cikin wata muryar kamar ta ƙatti.



Tana faɗin wallahi ƙarya ne ba wata wadda zata haife ɗa namiji a wannan gidan ta zauna lafiya matuƙar ina raye".


Hauka Mumy ta farayi har da cewa ba jinin Daddy ne ba in ma da gaske anhaihu ɗin.

Tana cikin wannan haukar Daddy ya shigo da sauri ta ƙarasa gareshi tace "Daddy  Zainab ina Fatima ɗin? tunda har zaka ɗauke ta amma baka sanar dani ba".


Yace "albishirin ki
kin samu yara biyu dukan su maza".


Wannan karun Mumy ta sauya ba kamar da ba dan ƙiri-ƙiri tace "da gaske ko ɗiyan kane? kodai wani wajan tasa musu ta ƙaƙabamaka kai ko ido rufe zaka karɓa".....bai bari ta kai ƙarshin zancin ba ya wanke ta da mari har bayu.


Yana huci yana nunin ta da ɗan ya tsa kana yace "kin san me kika faɗa  kowa, yaran nawa zaki fara sheganta su kuma ina raye".



Ba'abun da bai ce mata ba itama haka daga bisani yaga abun nata kamar da taɓin hankali dan haka yafice yabar mata gidan gabaki ɗaya.


Duk abunda akeyina hidamar suna Mumy bataje taga yaran nan ba kuma ta hana yaran ta zowa Zainab ka dai ce taje amma batare da sanin Mumy ba dan tace duk wanda yayi mata maganar Fatima sai ta illatashi.


Mumy takoma kamar sabon kamun hauka dan bataji bata gani ko ina zowa takeyi dan akashe yaran ita dai burin ta su bar numfashi.

'''(Allah sarki su yara mesuka sani ko me suka yamata.

Dan Allah ƴan uwana mu daina ƙazamin kishi dan bashida anfani wallahi wani kishi illah ne ga remu.

Kowa na dakishe amma kada kishi yasa muhaɗa Allah dawani,dan haka mukeyaye ƴan uwana.

Allah yasa mufi ƙarfin zukatan mu kuma ya kare mu daga ƙazamin kishi ameen. ''')



Inyi shagalin wajan sunan yaran inda Daddy yace ba zai sauya musu suna ba haka zai a barsu.

Sosai nera tayi kuka dan ba abunda Daddy bai yi mata ba, har  sauyama iyayen ta gida yayi kuma yaba mahaifin ta mota har ƙanwar ta sai da yaba mota itama Kaka Amo sai da yayi mata kyau ta mai girma Hajiya Sa'a ma tawa Kaka Amo, aikuwa Kaka Amo kamar tayi hauka dun daɗi.


Duk hidamar da akeyi ta sunan su alhasan bawan da group7 suka je kuma basuyi murna ba.


Watan Fatima ɗaya da haihuwa akayi auren su Zainab da Nabila,anyi shagalin biki sosai anka kashe nera Mumy ma ta narke nara sosai.


Bayan bikin su Zainab da sati uku Daddy yama tsama Hajiya Sa'a amaidam masa  da Fatima.

Ba yadda ta iya tashirya taje gidan iyayen ta ta faɗa musu saƙon Daddy kafi kowa yayi magana Kaka Amo tace wani sati da kanta zata maida Fatima ita kam Ummah  bata so haka ba, dan taso abar Fatima har tayi arba'in biyu amma ga yadda Kaka Amo tace kuma yadda tace haka za'ayi dan haka bata ce komai ba tayi shuru dan bata iyawa da yayyaƙar da zata mata.







*#Vote*
*Comment*
*Shere*



*Summy M Na'ige*🌸

ƘAWAR ƳATA CE                              {COMPLETED 01/2020.}   Where stories live. Discover now