No 15

789 36 1
                                    

💦💦💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦

*ƘAWAR ƳATA CE*
*1441H/2019M.*



®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata burin mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da lahira}_

'''🎐G•W•A🎐'''
_*GASKIYA DOKIN ƘARFE•*_


Story & Written
By
*SUMMY M NA'IGE*✍🏻




*Didicated to..*
*My Shemah*🥰

~VOTE & FOLLOW 4 Wattpad@GaskiyaWritersAsso.~



*Page 42*



*_________*📖 Har ta kai bakin ta sai taji ƙarnin madarar ya dake hancin ta aikuwa lokaci ɗaya ta fara kakarin amai.


Amayar da wanda ta kurɓa tayi tare da aje kofin dan jin take zuciyar ta na tashi sosai.


Shi ko Daddy duk rikicewa yayi yana ta faɗin,

"Sannu ,meke damunki Fatima?".


Ita ko Mumy ranta ne ya ɓaci sosai gani tabbas Fatima bata sha tea ɗin da ta kawo mata ba.


Sai da aman ya lafa Daddy ya jawo ta jikin tari da faɗi,


"Mekike ji yanzu?".

Ahankali tace, "komai banji Daddy".

Momy ko cikin ranta faɗa takeyi yariyar nan munafukace fah ji yadda ta wani shige masa ajiki wai ita bata da lafiya wai me ciki.



Ƙaraso wa tayi gaban su kana tace ma Daddy, "tunda aman ya lafa kabata ta sha sai tasha magani kaga zata ji daɗin jikin ta".

Ba musu Daddy ya ɗauko kofin tea ɗin ya miƙata yace, " "sha Fatima".


Kai ta girgiza masa kana tafara magana a hankali tace, "Daddy bana son madara amai zanyi".


Sai da Momy ta fake idon Daddy ta wanka mata hara-ra kana tace, "to me kike su sai akawa miki?".


Sai da Daddy ya mai-mai ta mata kana tace,"fura nake su".


Faɗima Momy yayi abunda tace dan ƙasa-ƙasa tayi maganar dan Mumy bata fahin ta ba sai da Daddy ya faɗa mata.


Momy tace, "to bari na kawo mata" tana faɗa tana aikama teema hara-ra.


Tana fita Daddy da kansa ya kai Fatima toilet ya taima ka mata ta gyara jikin ta kana ya fito.



Kuka ta sanya masa tace sai ya kai ta gida.

Da ƙyara ya samu ta haƙura zuwa ajima zai kaita kamar yadda yace.


Mumy ko kitchen ta koma ta ɗauko fura ta sake zuba wannan maganin kana tafito domin ta kai mata.


Salamar da akayi ce ya da katar da ita daga saurin da take.


Kallon-kallon suka fara yi ma juna kana Mumy ta ƙaƙalo murmushin karfin hali tace, "yau wa muke agani agida".


Ita ma Hajiya Sa'a martanin murmushin da tayi mata ta mai da mata.


Gaisawa suka fara yi kana Hajiya Sa'a ta tambaye Mumy yara da kuma Fatima.


Sai da Mumy tayi ajiyar zuciya kana tace, "yara duk suna ɗakin su,Fatima ko batada lafiya dan yanzu itace ma zan kai ma fura tashi".


Hajiya Sa'a tace,"ash-sha meke damun ta?".

ƘAWAR ƳATA CE                              {COMPLETED 01/2020.}   Where stories live. Discover now