No 6

1.6K 47 3
                                    

[12/5, 18:32] Summy Nah: 💦💦💦💦💦💦💦
              💦💦💦💦
                      💦💦
          

     *KAWAR* *'YATA* *CE*


®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }

         🎐 '''G•W•A'''🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*Story & written*
           By
       *Sumy*

'''Dedicated''' to..... 
*My family* 💖🥰



~Vote & Follow 4Wattpad @ GaskiyaWritersAsso.~

         *Page* 3⃣0⃣

*__________📖* Tana gama sallah tunani tashigayi ko dai Daddy bai dawo ba.

Har taso taje  part ɗinshi tagani ko ya dawo amma tana tsoron abunda zata tarar, haka ta hak'ura badon taso ba tace bari ta ɗau waya ta gwada kiran sa taji ko lafiya.


Waya ta ɗauka domin ta kira shi amma sai taga miss call d'in shi kusan har goma, dan haka cikin sauri tadanna masa  kira, tana ringing  amma  ba'ayi picking ba. Saida tayi mishi kusan miss Call uku ba'ayi picking ba dan haka tace bari ta dakata zuwa anjima ƙila baya kusa da wayar.

Har goma ta kusa ta kuma kiranshi,  Amma abin mamaki yanzu wayar ma akashe take.

hankalinta ya soma tashi, don bai taɓayi mata haka ba,  kuma tana son ta fito amma ta kasa.


dan haka ta hak'ura tace inbai zoba da  safe taje tagani ko lafiya.

Da haka ta hak'ura taje ta kwanta. 

Momy ko tana ganin ya samu bacci takoma part ɗinta ciki da farin ciki.




Tana ƙarasawa wayarta ta ɗauka takira Hajiya Shafa.

Ringing da bai wuce uku ba ta ɗaga.

bayan sun gaisa Momy ke faɗamata abinda yafaru, aikuwa murna awajanta ba'acewa komai, dan har rawa saida ta taka kana tace,  "gobe insha Allahu a gidanki za'ayi meeting, dan haka kisa ta haɗa mana lunch mai kyau".

Momy tace, "angama Hajiya tah kada kidamu tunda safe zata tashi ta ɗora".

Haka nakeso kafin itama tabar gidan taci ubanta,gobe ko wani taga zai auri ɗaya daga cikin mazajenmu nasan bazata bashi shawara ba".

Momy tace,  "sosai kuwa,  ko Zainab da take goyon bayanta yanzu ko ta daina dan haka sai gobe ma idan kunzo".

Tace,  "ba damuwa sai munzo".

Sallama sukayi Momy tayi wanka ta koma part ɗin Daddy.

Koda gari ya waye da zazzaɓi ta tashi dan ko baccin kirki bata samu ba dan sai gaf da asuba ta samu  bacci mai ƙarfi ya ɗauke ta.

Tana cikin bacci ta mai daɗi  dan ko sallah asuba bata samuyi ba,cikin barci taji anayi Mata  knocking da ƙarfi kamar za'acire ƙofar.

Tashi tayi da addu'a abakin ta, yadda take jin jikin ta kamar ba zata iya tashi ba amma saboda bugun ƙofar yayi yawa dan haka tayi ƙarfin hali ta tashi ta fara tafiya ahankali har takawo ƙofar dan har jiri take gani.

A hankali ta murɗa handle ta buɗe ƙofar, Momy ta gani tsaye fuskar ta haɗe, jikinta ne yaɗau karkarwa batasan lokacin da ta furta cewa,

ƘAWAR ƳATA CE                              {COMPLETED 01/2020.}   Where stories live. Discover now