Chapter 18, kuyi haƙuri na goge wancan ɗinne by mistake

5.2K 264 11
                                    

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*SHU'UMIN NAMIJI !!*

*Written By*
phatymasardauna
*🎈Mrs Sardauna🎈*

*Dedicated To My Brother Khabier....*

*🌈Kainuwa Writers Association*

*((United we stand ans succeed our ambition is to entertain & motivate the mind of readers))*

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

*WATTPAD*
@fatymasardauna

*Chapter 25 to 26*

"Yanzu likita ya za ayi kenan ?" Baffa yatambaya fuskarsa ɗauke da damuwa, ajiyar zuciya Doctor S.S yasauƙe haɗe da cewa " asamu wanda zai kwana da'ita, kafun gobe Idan Allah yakaimu " yanaƙare zancen, yasoma tattare files ɗin dake baje kan table ɗin dake gabansa..

Tuƙi yakeyi amma gaba ɗaya jinsa yake wani iri, duk wata ƴar walwala da kuzarinsa sun ƙaura daga garesa, sosai fyaɗen da akamawa yarinyar yataɓa ransa, hakanan yakejin matsanancin tausayin yarinyar na ratsa zuciyarsa,gaskia wasu mazan basu da imani, ka suma ƴar ƙaramar yarinya kamar wannan, ka danneta kakuma yi mata fyaɗe da ƙarfin tsiya, idan kai akamawa taka kuma bazakaji daɗi ba, ya Allah kasakama bayinka,... Horn biyu yayi kacal maigadi ya wangale masa tankamemen gate ɗin gidannasu, a parking space yayi parking motar tasa, haɗe da fitowa, kai tsaye ɓangarensa yanufa, domin yana da yaƙinin zuwa yanzu su Hajiyarsa sunshiga, ko yaje ɓangarensu bazai tadda suba,

"SADDIQ!!" wata ƴar dattijuwar mata dake tsaye a bayansa taƙira sunansa,, ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya Doctor S.S yayi haɗe da juyowa, ƙoƙarin ƙaƙalo murmushi yayi ya aza akan fuskarsa, "Hajiya barka da dare" yafaɗa cike da girmamawa, "Yauwa barka dai, sai yanzu kake dawowa ?" sunkuyar dakansa ƙasa yayi haɗe da sanya hanunsa abayan kansa yashiga shafa ƙeyarsa, "Hmm da kyau, duk nasan mai yajawo hakan, rashin iyali ne, kuma wallahi komai yakusa zuwa ƙarshe, a wannan karon ko kana so ko baka so,yazama dole kafitar da mata ko kuwa, in zaɓa maka cikin ƴaƴan ƙannena, bazanci gaba da sanya maka idanu ƙato dakai ace baka da mata ba !!" Hajiya tafaɗa cikin faɗa, "Kiyi haƙuri Hajiya Insha Allah nan ba da jimawa ba komai zai dai dai ta"

"Koda yaushe haka kake cewa, inanan inasa ido, idan naji shiru kuma kasan sauran " Hajiya tafaɗa, juyawa tayi kaitsaye tanufi ɓangarenta, shima nasa ɓangaren yanufa, jinsa yake amatuƙar gajiye, wanka yayi haɗe da bin lafiyar gado ya kwanta, abu na farko daya fara ziyartan idanunsa bayan yarufesu, shine hoton fuskar Zahrah, sosai hoton fuskarta keyi masa gizo,acikin idanunsa, da sauri yabuɗe idanun na sa, a zuciyarsa yana mai mamakin faruwar hakan, dayaga abun bana ƙare bane, kawai saiya dangana hakan, dacewa tsananin tausayinta ne yajawo hakan......

ZAID kuwa yana barin Zahrah kai tsaye TRANSCORP HILTON yanufa, domin dai yauma yana da meeting a can... Bayan sunkammala meeting ɗinne, kai tsaye yawuce ɗakinsa dake ɓangaren V.I.P,, yanashiga yasoma rage kayan dake jikinsa, direct bathroom yashige yasakarmawa kansa shower,, wani irin sanyi da nishaɗi yakeji a cikin zuciyarsa, tun bayan abun daya shiga tsakaninsa da Zahrah, yakejin ransa yayi fari, nishaɗi kawai yakeji acikin zuciyarsa, gaskia yau yasha zallan madarar daɗi, domin kuwa sosai ɗanɗanon Zahrah yayi masa hundred percent, yanason mace mai ɗanɗano sosai... Yana fitowa daga wanka, wayarsa dake aje kan gado, tasoma ƙara haɗe da kawo haske, alamar shigowar ƙira, saida wayar tasa takusa katsewa kafun yaɗauki wayar haɗe da karawa akan kunnensa, "Shigo ciki" Zaid yafaɗa a taƙaice haɗe da cilla wayartasa kan gado,, Abid ne yaturo ƙofar ɗakin yashigo,, rungumar juna sukayi, kamar yanda suka saba koda yaushe idan sun haɗu,,

"Daga ina haka ?" Zaid ya tambayi Abid, murmushi Abid yayi haɗe da zama akan hamshaƙiyar kujeran dake gefen gadon ɗakin, " yau nasha sweet abokina, wata babe nasamu mai zafi, inagayamaka tashayar dani zuma !!" Abid yafaɗa cike da nishaɗi,, Dariya sosai Zaid yayi hadda ƙyaƙyatawa, shiru kawai Abid yayi yatsaya yana kallon Zaid, domin dai Zaid baya dariya abanza, abune mai wuya kaga dariyansa, sai dai idan ya ƙulla wani abun... " Final !!" Zaid yafaɗa yanamai cije laɓɓansa,, zaro idanu Abid yayi cike da mamaki yace " what ! ? badai kanaso kacemin harka gama da Zahrah ba ??" ƙayataccen murmushi Zaid yayi haɗe da cewa "Tuntuni harma anwuce wajen " dariya Abid yayi haɗe da cewa " Har yau bansan kai wani irin mutum bane Zaid, idan kaso abu, to ko ta wani hali sai ka sameshi, Allah sarki, Innocent girl, tanacan tana fama, nasan kabata kaya da yawa, may be ma haryanzu bata san awace duniya take ba " Abid yafaɗa... Still murmushi Zaid yayi haɗe da gyara zamansa, wayarsa yajawo yashiga latsawa, amma fuskarsa ɗauke take da murmushi... Ganin haka yasa Abid sha re maganar domin yafahimci me abokinnasa yake nufi,, Jefi jefi suke hira da Abid.....

SHU'UMIN NAMIJI !!    (completed)Where stories live. Discover now