Chapter 25

4.9K 293 19
                                    

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*SHU'UMIN NAMIJI !!*

*Written By*
phatymasardauna

*Dedicated To My Lovely Brother Khabier*

*🌈Kainuwa Writers Association*

*{United we stand & succeed; our ambition is to entertain and motivate the mind of readers}*

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

*WATTPAD*
@fatymasardauna

*Editing is not allowed📵*

*( My Lovely, My Sweetness, My Happiness, My Best Friend ever, inasonki sosai da sosai ƙawata rabin raina, wannan page ɗin gabaki ɗayansa kyautane a gareki HAUWA Kulun MAJADAN 😂, JIDDATUL HUSSARY kiji daɗinki ki mo re ƙawata takaina HOUWER )*


*Chapter 40 to 41*

Nannauyar ajiyar zuciya Doctor ya sauƙe, haɗe da zura hannayensa a cikin aljihun wandon sa, "Shikenan to tunda kince haka, na baki two minute kacal kisameni a waje, idan kuwa bakifitoba zan dawo na sake iskeki, kuma wlh sai na danneki na jamiki zip ɗin da ƙarfin tsiya" dagajin yanda yayi maganar kasan cewa tsokana ce kawai.

Kai kawai ta iya jinjina masa alamar cewa taji zata fito ɗin,

Ɗan gun tun murmushi Dr yayi haɗe da sakai yafice daga cikin ɗakin.

Yana fita ta sauƙe nannauyar a jiyar zuciya, haɗe da sanya hanunta a bayanta, taƙarasa jan zip ɗin rigarta, zunbuleliyar hijabinta ta zura akan rigar haɗe da ficewa daga ɗakin, saboda tasan idan bata je bama tabbas zai biyota.

Zaune ta iskesa a cikin rumfar dake barandar gidan nasu, can gefe dashi ta zauna haɗe da kawar da kanta gefe domin kuwa ta lura gaba ɗaya idanuna akanta suke,

"Banason wasa matso kusa kisha maganinki !" yafaɗa babu alamar wasa akan fuskarsa.

Ɗan ƙaramin bakinta tacunno gaba haɗe da sake ɓata fuska, Allah ya sani ta tsani magani sosai da sosai, batama so ayi mata ko da zancen magani ne.

Batare da ya sake ce da ita komaiba yashiga ɓallo ƙwayan maganin daga jikin tablet ɗinsu, yana sawa a hanunsa, har sai da yagama ɓare iya wanda zatasha a yau ɗin, miƙo mata maganin yayi haɗe da bata goran ruwa,

Fuska a daƙune haka ta karɓi magananin saida ta rumtse idanunta sosai kafun ta iya haɗiye maganin, gashi dama irin magani mai ɗacin nan ne,

"Kishirya next week zaki koma makaranta " Dr Sadeeq ya faɗa yana mai latsa wayar da dake riƙe a hanunsa, bakuma alamar wasa akan fuskarsa.

Saurin dawo da kallonta garesa tayi, haɗe da girgiza kanta, "A gaskia ni bazan sake komawa makaranta ba !" Zahrah tafaɗa cikin ɓata rai,

"Maiyasa ? " Dr Sadeeq ya tambaya kai tsaye.

"Saboda babu amfanin hakan, ana karatune don a inganta rayuwa, to nikuma tawa rayuwar tajima da rugujewa, mai yasa zanɓata lokacina wajen gyara abun da bashi da kyau, bakuma zai gyaruba, na haƙura da komai zanjira mutuwata kawai !" Zahrah taƙare maganar cikin yanayi mai nuni da cewa zuciyarta tagamayin rauni,

" Idan ginin gida ya ruguje, ƙoƙari ake a sake gyarasa, akuma sabuntasa har yafi nada ɗin daya ruguje kyau, da kuma ƙawatuwa, shin kinsan maiyasa ake yin hakan? " Dr Sadeeq ya tambayeta bayan yamai da gaba ɗaya nutsuwarsa gareta.

"A'a" tafaɗa a taƙaice.

"Saboda yanada matuƙar amfani gamasu shi, sannan kuma yana da kyau idan karasa dama ta farko, kasake neman wata damar, domin sau dayawa anasamun nasara ne a gaba, bawai a farko farko ba, idan kika ci gaba da kashewa kanki ƙargin guiwa, to zuciyarki zata zama mai tsananin rauni, babu amfani idan kikace bazaki inganta rayuwarki ba, amma inaso kisanar dani fa'idan yin hakan, nuna kin yarda da ƙaddara yana ɗaya daga cikin mantawa da komai, idan kika zauna a gida, bazaki taɓa samun cigaba ba, nasan abun da Zaid yayi miki har yau yana cikin zuciyarki, kuma inada tabbacin cewa idan kinsamu wadataccen ilimi nan gaba, zaki iya yaƙi da azzalumai irin su Zaid, please Zahrah kada kicemin a'a, nayi hakanne saboda samamiki sauƙi, da kuma cireki a kaɗaici !" Dr Sadeeq yaƙare maganar cikin muryan tausasawa, dason ƙara mata ƙarfin guiwa.

SHU'UMIN NAMIJI !!    (completed)Where stories live. Discover now