Chapter 70

5K 423 59
                                    

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*SHU'UMIN NAMIJI !!*

*Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Brother KHABIER*

*🌈Kainuwa Writers Association*

*WATTPAD*
@fatymasardauna

*Chapter 116*

"ZAID!" ta maimaita sunan abakinta cike da tsananin mamaki.

Yanda yaga jikinta na ɓari shine abun daya basa mamaki, zallan tsoro ya hango kwance akan fuskarta, yayinda cikin idanunta kuwa, suka bayyana soyayyar dake kwance acikinsu, wato soyayyar ZAID, shi yasani ba tun yauba, bakuma zai yaudari kansa ba, yasani ƙwarai Zahrah na son Zaid, so ba irin na wasaba, so matsananci, amma kuma babu yanda zaiyi, dayana da iko to daya cire mata son Zaid acikin zuciyarta, amma wannan banasa bane, na Allah Ne, yasan Zahrah tana sonsa, amma soyayyar da takewa Zaid ta dabance, da ace zai iya, to daya danne zuciyarsa, ya miƙata ga Zaid, yasan hakan zai samarmusu da farinciki, ita da Zaid, amma kuma yasan koda yayi hakan to ba mafita bane, domin ayanzu yasan dole idan baya tare da Zahrah tayi kewarsa, yana sane da cewa yakafa mata tutar son sa, wanda bazata ankara da hakan ba, har sai randa yazama baya tare da'ita, baya fatan wata ƙaddara ta rabasu, amma yasani ko mai daren daɗewa sai sun rabu, saboda akwai mutuwa, koshi ko ita, watarana ɗaya dole zai bar ɗaya, yau idan baya raye, baya fata Zahrah ta auri wani namiji idan ba Zaid ba, tunaninsa yayi nisa, baisan da cewa ta ƙaraso inda yake ba, saida yaga ta zube a gabansa, tana kuka, cikin muryar kukan takecewa.

"Kada kamin haka doctor, wallahi ni banason duk wata kyauta da zatafito daga garesa, namantasa acikin rayuwata, banaso kuma nasake tunasa, kamayar masa da kyautarsa, bana buƙata farincikin da kake bani kaɗai ya isheni"

Tunda tafara maganan yake kallonta, ajiyar zuciya yayi, haɗe da kamo hannayenta, cikin murya me sanyi yace. "Kinsani bakyau maida hanun kyauta baya, meyasa to zakiyi haka? mekike tunani akan Zaid?" ɗan dakatawa da maganar yayi, tare dayin wani murmushi, kana ya miƙe tsaye, daga zaunen da yake.

"Kyautace kawai ya miki, ai atunanina hakan ba wai yana nufin wani abubane, bazan tilasta miki ba, amma nasan abundake cikin zuciyarki, don gashi har a idanunki sun nuna, so ba ƙarya bane Zahrah, haka kuma ba laifi bane, don zuciya na dakon so, wannan ma wata ƙaddarace, wanda babu wani wanda ya isa ya kauce mata" yanakai ƙarshen zancen nasa yanufi hanyar fita daga ɗakin.

Da sauri taje ta faɗa jikinsa, kuka take sosai, durƙusawa tayi haɗe da zube guiwowinta a ƙasa, kana ta riƙe rigarsa, kanta tashiga girgizawa, tana kuka tace. "A da na sosa fiye da yanda naso kaina, amma ayanzu baya acikin zuciyata kamar yanda kake tunani, Inasonka da duka zuciyata, bana fatan wata ƙaddara tazo wacce zata rabani dakai, kabani farinciki, kajiyar dani daɗi, kashayar dani zuman soyayyarka, bazan iya watsa maka ƙasa idanunka ba, kai mijinane wanda bayan kai bani da wani tamkarka, nasan kai ɗin me sonane, amma meyasa kayi haka? mai yasa kai da kanka, zaka amince da na karɓi kyautar wanda yazama silar rugujewar rayuwata?"

Durƙusawa yayi agabanta, haɗe da sanya hanunsa ya share mata hawayen dake gudu akan fuskarta, cike da kulawa yace. "Banason kukanki Zahrah, keɗin wata babban jigo kuma mahaɗi ne acikin rayuwata, nasan Zaid ya cutar da rayuwarki, amma kuma hakan bazai hana ki amshi kyautarsa ba, ayanzu kowa yasan cewa ke matatace, saboda haka Zaid bazaiyi miki kyauta da wata manufa ba, kuma kafun ya miki kyautar saida ya tambayi amincewata tukunna, nakuma amince masa, nayarda da Zaid Zahrah, nasan idan duka mutanen duniya zasu taru su cutar dake, to Zaid bazaiyi hakan ba, haka kuma idan ni zan iya cutar dake, to ina tabbatar miki idan Zaid yasan da hakan, to bazai bari na cutar dake ba, Zaid ɗin da kikasani ada bashine wanda yake a yanzu ba, kada kiyi tunanin wai ko zanji haushi akan kyautar da Zaid yayi miki, niba jahili bane Zahrah, haka kuma halina ya banbanta da na wasu mazan, ni mutum ne me saurin fahimta, sannan kuma abune mawuyaci nayiwa wani na mummunan zato, agurin wasu mazan, hakan zai iya zama matsala, amma a wajena hakan ba komai bane, tunda nasan cewa keɗin tawace ni kaɗai, bakuma wai don bana kishinki bane yasa hakan tafaru ba a'a, ni kalan nawa kishin ba irin na wasu bane, inakishinki sosai, sai dai kuma kome acikin nutsuwa nakeyinsa, ke kinsan inasonki ina kuma kishinki " yaƙare maganar yana me lakace mata dogon hancinta.

SHU'UMIN NAMIJI !!    (completed)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora