🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SHU'UMIN NAMIJI !!*
*Written By*
Phatymasardauna*Dedicated To My Brother KHABIER*
*🌈Kainuwa Writers Association*
_{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*
*WATTPAD*
@fatymasardauna*Editing is not allowed📵*
*CHAPTER 80 to 81*
Kafun mintuna kaɗan dandazon mutane sun cika kan babban titin da hatsarin yafaru, kowa salati kawai yakeyi domin kuwa duk wanda yaga yanda motar Zaid tayi ƙwatsa ƙwatsa bazai taɓa tunanin mutumin dake ciki zai fito a raye ba, gaba ɗaya mutane carko carko sukayi kowa tsoron zuwa wajen motar yake gudun kada wuta ta tashi dashi, domin kuwa har motar tafara tashin hayaƙi, wasu daga cikin mutanen da suka taru a wajenne suka taimaka suka ƙarasa wajen motar, da ƙyar suka iya zaluƙo Zaid wanda gaba ɗaya fuskarsa ta ɓaci da jini duk jikinsa jini ne, kallon gawa kawai mutanen da suka ciro sa suka shiga yi masa, domin kuwa a yanda suka gansa babu alamar rai ajikinsa, babu kuma alamar cewa zuwa nan gaba zai iya farfaɗowa, sai dai kuma ba'aja da ikon mai sama (ALLAH) Dai dai lokacin motar ƴan sanda suka ƙaraso wajen, kai tsaye su suka ɗauki Zaid suka sanyasa acikin motarsu, direct aka wuce asibiti dashi, duk da suma dai basu da tabbacin cewa yana da rai ko bai da shi....
Emergency aka karɓi Zaid yayinda likitoti suka shiga basa taimakon gagawa domin kuwa sun gano cewa akwai rai ajikinsa, kawai de yayi mummunar buguwa ne..... Saida suka share masa jinin dake kan fuskarsa kafun Dr.Bilal ya iya shaida fuskar Zaid ɗin, take hankalinsa yaƙara tashi, tsananin tausayin Zaid ɗin ya kamasa, shin wani irin hali Alhaji Ma'aruf zai tsinci kansa idan yaji wannan mummunar labarin?,,,, haka dai sukayi iyaka ƙoƙarinsu wajen shawo kan al'amarin sai de kuma duk yanda suka so yadawo hayyacinsa abun yaci tura, abu ɗaya suka dogara dashi, idan har baidawo hayyacinsa nan da 3 days ba, to fa lallai akwai matsala.... Kallon sauran abokan aikinsa Dr.Bilal yayi haɗe da soma cire safar hanunsa, ganin haka yasanya suma suka cire nasu safan, daga nan suka fice daga cikin ɗakin...
Kallon sauran Doctor's ɗin Dr.Bilal yayi haɗe da sauƙe ajiyar zuciya. "Mubashi nanda 24 hour maybe zai yi farfaɗowa, sai de kuma Allah yasa buguwan da yayi bai taɓa masa lafiyan kansa ba"
"Insha Allah kansa bazai samu wata matsala ba, sai de kuma yakamata a nemi ahalinsa a sanar musu" Wani Dr. yafaɗi haka..
"Insha Allah" Dr.Bilal yafaɗi haka ga abokan aikin sa, bayan ya soma laluɓan Numbern Dad ɗin Zaid....
Alhaji Ma'aruf ne zaune a cikin katafaren falonsa wanda yagaji da haɗuwa, gefe dashi Hajiya Sajida ce tazuba tagumi daganinta kasan cewa tana cikin damuwa... "Menene abun ɗaga hankali har haka Hajiya? kinfasan Zaid ba yaro bane shi, kuma faɗuwar gaban nan da kikeji nima inajinsa, sai de kuma....." Maganar Alhaji Ma'aruf ne ya katse sakamakon wayarsa da ta soma ruri alaman shigowan ƙira,,, mamakine ya bayyana akan fuskar Alhaji Ma'aruf ganin cewa Dr.Bilal ne ke ƙiransa,, bayan sun gaisane Dr.Bilal yayi gyaran murya haɗe da cewa Alhaji Ma'aruf ɗin yana buƙatar ganinsa,,, murmushi Alhaji Ma'aruf yayi haɗe da cewa "Kakuwa ci sa'a ina gida, sai de ka hanzarta zuwa saboda zuwa ɗan anjima zan fita"
Ajiyar zuciya Dr.Bilal ya sauƙe haɗe da cewa "Kayi haƙuri Alhaji amma maganar bata gida bace, Magana ce me matuƙar mahimmanci kuma yana da kyau kazo ɗin"
Cikin ɗaurewar kai Dad yace da Dr.Bilal gashinan zuwa..
Kallon Alhaji Ma'aruf Mom tayi haɗe da cewa "Wayene, kuma me yake faruwa?" atake Mom taje romawa Dad waƴan nan tambayoyin..
YOU ARE READING
SHU'UMIN NAMIJI !! (completed)
General FictionLabarin Zaid da Zahrah...."Idan har yaudara zata zamemaka abun ado mai zaka amfana dashi acikin rayuwarka ? Miye ribar aikata zina da fasiƙanci ? Natsaneka Zaid ! Natsaneka !! Bana fatan Allah yasake haɗa fuskata da taka fuskar har gaban abada".....