Chapter 49

4.9K 308 112
                                    

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

            *SHU'UMIN NAMIJI !!*

 
    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Brother KHABIER*

*🌈Kainuwa Writers Association*

_{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

            *WATTPAD*
      @fatymasardauna

*Editing is not allowed📵*

        *CHAPTER 86 to 87*

Sunkuyar dakai ƙasa Zahrah tayi  gaba ɗaya ita kunyar mutanen dake tare a wajen takeyi, tunda take bata taɓa shiga irin wannan taron ba, sai gashi yau akanta ma akeyin taron,   ba abun dake damunta kamar yanda idan taɗaga idanunta take ganin idanuwan mutane akanta kowa ita yake kallo da waƴanda suka santa haddama waƴanda basu santa ba,,    matso da kansa yayi kusa da'ita haɗe da kawo bakinsa wajen kunnenta  "Anan ma kunya zaki nuna?" ƙasa ƙasa yayi maganar.    satan kallonsa tayi haɗe da ɗan sakin murmushi  amma kuma batace dashi komai ba, haka dai masu yin vedio suka ci gaba da ɗauka yayinda..... Hmmmm kamu dai yayi kamu  yakuma ƙawatar amma kuma sai dai sam amarya Zahrah ta kasa sakewa komai a ɗari ɗari takeyinsa,  abu biyune suka haɗe mata kunya dakuma rashin sabo, saboda bata taɓa zuwa irin waƴannan wajen ba, wannan ne karonta na farko, gashi kuma kamun yatara mutane sosai,  su Husnah sunyi rawa sosai sun raƙashe Amarya kuwa ae ko taka kafarta bata'iya ba gaba ɗaya nauyi da kunya sun hanata sakat.... sai gab da magrib aka tashi  daga kamu kowa yasamu abun arziƙi ankuma cika ciki da abinci na musamman da kuma lemuka...    Yanzu kam mota ɗaya Zahrah da Husnah harma da Suhaima suka shiga, yayinda Dr.Sadeeq shikuma yashiga wata motar ta daban...  Jingina bayanta tayi da kujera haɗe da kwantar da kanta akan kafaɗan Husnah, duk hiran da  Husnah da Suhaima keyi jinsu kawai takeyi, sosai sanyin AC'n dake cikin motar yake ratsata har hakan yaso sanyamata zazzaɓi, haka dama ita take matuƙar ta shiga  hayaniya to kanta sai ya ɗanyi mata ciwo, uwa uba kuma idan sanyi yayimata yawa saita ɗanyi zazzaɓi..  Harsuka isa gida Zahrah ko uffan batace ba duk da kuwa yanda su Husnah kejanta da hira, amma iya abun da take iyayimusu shine murmushi...  Fitowarta a wanka kenan,  sauri sauri ta zura wata doguwar riga me kauri ajikinta,,, kallon ta ta mayar ga Husnah wacce taketa faman chatting a wayarta sai nurmushi kawai take zubawa..

"Wai ke da waye ne haka?  a iya sanina dake ke ba mutum bace me yawan chatting da'alama dai munsamu ƙaruwa" Zahrah tafaɗi maganar cikin sigar tsokana... Dariya Husnah tayi haɗe da ɗage giranta sama.    "Ƙwarai kuwa tawan, wallahi ɗazu na haɗu da wani guy a wajen kamunki, ina tunanin ya kwantamin arai"

Dariya Zahrah ta sanya haɗe da neman guri ta zauna akusa da Husnah haɗi da kwantar da kanta akan kafaɗan Husna'n....

"Husnah kinsan ya so yake?"  tambayar da ta fito daga bakin Zahrah kenan..

Mamaki tambayar da  Zahrah tayi mata  ya bata amma kuma batasan menene dalilin dayasanya Zahrah tayi mata wannan tambayar ba...

"Eh zan iyacewa nasansa zankuma iya cewa  bansan saba, saboda banyi wani zurfi acikinsa ba, amma kuma ke kinsan bana yaudaran kaina Zahrah, duk wasu alamomin so nasansu, saboda hakane ma nayardarwa kaina cewa nakamu da soyayyar Yazeed so matsananci!" Husnah tafaɗi haka tana me wasa da wayar hanunta, da'alama sunan Yazeed kaɗai da ta ambata yasanyata cikin shauƙi..

Ajiyar zuciya me ƙarfi Zahrah ta sauƙe haɗe da ɗago kanta daga kan kafaɗar Husnah, hannayen Husnah takama cikin murya me sanyi tace da  Husnah "Wasu irin alamomi ne kesanyawa mutum yagane cewa yakamu da so?  sannan kuma inaso ki sanar dani menene hukuncin zuciyar da ta makance har take ƙoƙarin sake son wanda yacutar da'ita, wanda kuma baida wani amfani a wajenta"

SHU'UMIN NAMIJI !!    (completed)Where stories live. Discover now