🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SHU'UMIN NAMIJI !!**Written*
Phatymasardauna*Dedicated To My Brother KHABIER*
*🌈Kainuwa Writers Association*
_{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*
*WATTPAD*
@fatymasardauna*Editing is not allowed📵*
*CHAPTER 108*Kaikawo take tayi a cikin kitchine ɗin, sauri take ta kammala aikinta, tsaye take acikin kitchine ɗin, tana wanke wani plate dake riƙe a hanunta, sosai nayi mamakin ganinta a haka, rigace irin T-shirt me faɗinnan sanye ajikinta, duka duka tsayin rigar ko rabin cinyanta bai ƙarasa ba, bata kuma sanya wando dan rufe cinyoyinta ba, wani irin slipper ne me kyaun gaske sanye aƙafarta, wanda aka ƙawata samansa da wani kyakkyawan follower,
Irin yanayin shigar nata yasanya tayi kama da irin yaran turawan nan.Sam bata ji motsin shigowarsa ba, hakan yasa bata kawo cewa akwai wani mahaluƙi dake kallonta ba.
Sake gyara tsayuwarsa yayi, haɗe da jingina bayansa, da jikin ƙofar fita daga kitchine ɗin, sosai tayi masa kyau, babu abun daya fi ɗaukar hankalinsa ajikinta, kamar hips ɗinta, ga santala santalan cinyoyinta, da suka bayyana kansu, gwanin ban sha'awa, gaskiya komai na Zahrah me kyau ne, ta cika mace hundred percent, yajima yana fata da burin samun cikakkiyar mace, me cikar halitta ka marta, a matsayin matar aurensa, sai gashi Allah Ya dubesa ya basa Zahrah.
Ɗan tsayawa tayi, haɗe da sanya hannayenta bisa ƙugunta, tana me sauƙe numfashi, a hankali, da'alama dai akwai gajiya a tattare da'ita.
"Kin gaji ko?"
Cike da mamakin jin muryarsa, acikin kunnuwanta, da tayi ta juyo, tana me fuskantarsa.
Murmushin sa me kyau, ya sakar mata, haɗe da soma takowa zuwa gareta.
"Yaushe kadawo bansani ba?" ta tambayeshi, cike da tsananin mamaki.
"Najima da dawowa, nadai tsaya kallon abar sona ne" yafaɗi haka yana me lumshe gajiyayyun idanunsa, sosai yakejin gajiya ajikinsa, baƙaramin aiki yau yasha a office ba.
"Sannu da dawowa!"
tafaɗa tana sakarmasa murmushi.Jawota cikin jikinsa yayi, haɗe da rungumeta, kansa ya ɗaura akan wuyanta, wata ajiyar zuciya, me ƙarfi ya sauƙe.
"Nayi kewarki sosai my lovely wife!" cikin murya, me sanyi, ya yi maganar.
Murmushi takuma sakar masa, haɗe da langwaɓar da kanta gefe gudu. "Nima nayi kewarka Hubby na!" cikin salo ta ƙare maganar.
"Dagaske kema kinyi kewata my wife? nifa dukanki nayi kewarki!" yafaɗi haka yana meyi mata wani irin kallo, dake ɗauke da wani tarin ma'anoni masu yawa.
Ganin kallon dayakeyi mata, yasa tasaki murmushi me ɗan sauti, ƙoƙarin janye jikinta daga nashi tasoma yi.
Ƙam ya riƙeta, haɗe da sake mannata acikin chest ɗinsa, da alama dai bayason tacire jikinta acikin nasa jikin."Uh dan Allah, Kabarni na ƙarisa aikina, kuma mafa duk ƙauri nake, amma kaketa mannani a jikinka, kaɗan bari nayi wanka kaji!" tayi maganar cikin yanayi na lallashi, tasani sarai, idan dai ba lallashinsa tayi ba, to bazai bari ta kammala aikin data fara ba.
YOU ARE READING
SHU'UMIN NAMIJI !! (completed)
General FictionLabarin Zaid da Zahrah...."Idan har yaudara zata zamemaka abun ado mai zaka amfana dashi acikin rayuwarka ? Miye ribar aikata zina da fasiƙanci ? Natsaneka Zaid ! Natsaneka !! Bana fatan Allah yasake haɗa fuskata da taka fuskar har gaban abada".....