Chaper 42

5.5K 317 40
                                    

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

       *SHU'UMIN NAMIJI !!*

 
      *Written By*
*Phatymasardauna*

*Dedicated To My Brother KHABIER*

*🌈Kainuwa  Writers Association*

_{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

         *WATTPAD*
   @fatymasardauna

*(💗Wannan page ɗin baki ɗayansa kyautane agareku my wattpadi'ans  inagodiya sosai a gareku💗)*

*Editing is not allowed📵*

   
     *CHAPTER 72 to 73*

Baki Labisat dake tsaye taturo gaba haɗe da ɓata fuskarta duk wai akan don  Mom ɗinsu tace taƙira mata Zaid a ɓangarensa ne yasa take wan nan abun...

"Tsayuwan uban me kike bacewa nayi ki ƙiramin yayanki ba!" Mom tafaɗi haka cike da faɗa, ganin Labisat ɗin bata da niyar zuwa aiken datayi mata.

"Mom wlhy tsoro nakeji kada naje ya masifance ni!" Labisat tafaɗi haka cikin shagwaɓa. 

Harara Mom tawurga mata bashiri Labisat takama hanyar fita daga cikin falon...
Aranta kuwa roƙon Allah take yasa idan taje kada ya masifanceta saboda shi abun faɗa baya masa kaɗan ko kaɗan,  jiya jiya dawowanta daga boarding school amma Mom zata haɗata da masifan Yaya Zaid (Su yaya manya😂)

Kusan sau huɗu Labisat tana knocking ƙofar daze kaita cikin falonsa, amma shiru ba amsa, hakan yasanya tatura ƙofar tashiga,,   bakowa acikin falon sai daddaɗan ƙamshinsa dake tashi.. Direct ƙofar bedroom ɗinsa tanufa haɗe da soma knocking ƙofar,, jin shiru ne yasanya tashiga ƙiran sunan sa...

"Brother! Brother!"  ko gyaran murya bataji yayiba balle tasa ran zai amsa mata, batama tabbatar yana cikin ɗakin ko baya ciki ba..
Gajiya tayi da knocking ƙofar ta juya tayi tafiyarta...

"Mom inaga fa kamar Bro bayanan domin nayita knocking door ɗinsa amma bai amsa ba"

"Tabbas yana cikin gidan nan Labisat domin kuwa tunjiya daya shigo baifita ba, har me gadi na tambaya naji ko yaga fitarsa amma yacemin tunjiya daya shigo bai fita ba,  miskilancin nasa ne ya motsa, banaje dakaina nasa mesa nikam ae be isa yanunamin halin ƙyaliya ba" Mom tafaɗi haka tana me miƙewa tsaye daga zaunen da take..

Itama ɗin de knocking tayi masa haɗe da ƙiran sunansa amma shiru bai amsata ba, hakan yasa ta murɗa handle ɗin ƙofar ta kutsa kanta ciki bakinta ɗauke da sallama..

Tsuka Mom taja sakamakon ganinsa da tayi kwance akan gado yayi ruf da ciki, lallai ma wato iskancine ya hanasa amsa mata, da fari hartayi zaton ko baya gidan ne..

"Zaid!" taƙira sunansa cikin kakkausar murya... Ko motsawa baiyi ba balle tasaran ze amsa mata..

Kafeshi da idanu tayi tana me nazartarsa, a iya saninta da Zaid baya bacci a irin wan nan lokacin, impact ma shiba mutum bane ma'abocin yawan bacci ba'a bisa ƙa'ida ba, idan kuwa harda gaske baccin yake to baya rasa ɗayan biyu kodai baida lafiya ko kuma yayi halin nasa nashan ƙwayoyi,  "Sai yaushene Zaid ze san ya girma? sai yau shene zai dena nuna rashin damuwa da lafiyarsa?" tajeromawa kanta waƴan nan tambayoyin,  "Haƙiƙa Zaid ɗanta ne amma ita kanta har yau batasan wani irin haline da shi ba, shi mutum ne me nuƙu nuƙu bakoda wani lokaci ne kake sanin gaba da bayansa ba, haka nan yake bakomai ne zaka masa ƙa burgesa ba yanada wani shegen shu'umin hali saide kawai Allah yashirya mata shi"...

SHU'UMIN NAMIJI !!    (completed)Where stories live. Discover now