Chapter 30

5K 304 26
                                    

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*SHU'UMIN NAMIJI !!*

*Written By*
Phatymerhsardauna

*Dedicated To My Brother KHABIER*

*🌈Kainuwa Writers Association*

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

*WATTPAD*
@fatymasardauna

*Editing is not allowed📵*

*Chapter 48 to 49*

Yajima tsaye a gaban shower ruwa na dukansa, mafarkinsa na yau ne yatsaya masa a rai, duk da kuwa cewa ba wannan bane karo na farko, daya fara yin irin wannan mafarkin. Koda wasa baiyi niyar komawa America a yau ba, amma yanzu yaji ajikinsa cewa komawarsa can ɗin yafi masa, domin kuwa mararsa har ƙullewa take saboda sha'awa, gaba ɗaya kwana biyunnan da suka shuɗe baiyi sex ba. A gurguje ya shirya kansa, bayan yasanar da Abid cewa shima ya kimtsa zasu wuce America a yau. Suna zuwa airport basu wani daɗe ba, jirginsu yaɗaga zuwa sararin samaniya....

Nigeria

Washe garin ranan da Dr yazo da dare yafaɗi muradinsa..

Tun tashinta takejin ƙunci a zuciyarta, hakanan take jin ta tsani komai na duniyar, badon lecture'n da zasuyi yau mai amfani bane, to tabbas da bazata je makarantar bama.

Doctor Sadeeq ne tsaye a tsakiyar ɗakinsa, yayinda hannayensa duka biyu ke sanye cikin aljihun wandonsa, shima kallo ɗaya zaka masa kafahimci cewa yana cikin damuwa, kallon sa yamaida kan agogon bangon dake saƙale ajikin bangon ɗakin na sa, ƙarfe 7 da rabi na safe kenan, tabbas yasan yau ƙarfe takwas suke da lecture, yanaji a jikinsa cewa yayi mata laifi mai girma, sannan idanunsa suna matuƙar son ganinta, to amma a yanda yakeji bazai iya zuwa gareta ba, "idan ma naje nace mata me?" yatambayi kansa. " Nariga dana furta mata abun dake cikin zuciyata, dole zanbata lokaci domin samun dawowar nutsuwar ta" yafaɗi hakan a bayyane, wayarsa ya ɗauka haɗe da kutsawa cikin dialing call ɗinsa, numbern drivernsa yashiga ƙira kai tsaye, ƙara biyu wayar tayi, drivern yaɗauki ƙiran, kasancewar driver'n yasan gidan su Zahrah, yasan ya kai tsaye, bai tsaya yi masa wani kwatance ba, yace masa yaje ya ɗauketa ya kaita makaranta, da "to" kawai driver'n ya amsa masa, katse ƙiran yayi haɗe da cilla wayar tasa zuwa kan gado,
"Yasan balallai ta yarda tabi driver'n ba, domin yanayinta da yagani jiya, kaɗai ya isa ya tabbatar masa da hakan, amma burinsa ne ya bata ingantacciyar kulawa, shiyasa baiyi ƙasa a guiwaba wajen sa driver'n nasa kaita makarnta, saboda baiso ta hau wani abun hawa bayan nasa....

Ko kwalli, yau bata shafa ba, balle kuma uwa uba fawder, zumbuleliyar doguwar riga ta sanya, haɗe da ɗaura ƙaton hijab akai, kallo ɗaya zakayi mata kasan cewa tana cikin damuwa da ƙunci.

Koda tayi mawa su Baffa sallama, suma sun fahimci cewa yanayinta ya sauya, amma sai suka share babu wanda ya tambayeta.

Tana kai ƙofar gida zuciyarta tayi wani irin bugawa, sakamako'n ganin motar Dr Sadeeq, da tayi fake a ƙofar gidan nasu, tsayawa tayi cak ganin cewa driver'n sane yafito daga cikin motar, saɓanin shikansa Dr ɗin.
Cike da girmamawa Mudi driver ya ƙaraso inda Zahrah ke tsaye.

" Ranki shi daɗe barka da safiya! dama yallaɓoi ne yace nazo na kaiki makaranta, shi ba zai samu daman zuwa ba, wani aiki ne ya riƙesa, kawo jakar na karɓamiki" Mudi driver ya ƙare zance'n nasa yana mai ƙoƙarin karɓan jakar dake riƙe a hanunta. Saurin ja da baya tayi haɗe da fusge jakarta, cike da ɓacin rai tace.
"Kakoma kace masa bana buƙatar kulawarsa koda kaɗanne, ka kuma ce masa injini yafita a rayuwata, saboda bana buƙatarsa!" tanakai ƙarshen zancennata tasakai tayi tafiyarta.

SHU'UMIN NAMIJI !!    (completed)Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin