Chapter 38

4.8K 306 33
                                    

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*SHU'UMIN NAMIJI !!*


*Written By*
*Phatymasardauna*
_(shalelen kainuwa)_

*Dedicated To My Brother KHABIER*

*WATTPAD*
@fatymasardauna

*(Wannan page ɗin gaba ɗayansa kyautane a gareku Members na BENEFICIAL WRITERS ASSOCIATION haƙiƙa kuɗin na daban ne, sannan kuma kuna da ƙoƙari sosai da sosai wajen sanbaɗomana comment, muna godia Allah yabar ƙauna)*

*Editing is not allowed📵*

*CHAPTER 64 to 65*

Baki da hanci Zahrah ta sake tana kallon waƴan nan ƴan matan da suke tsaye suna me yimawa cikin gidannasu kallon wulaƙanci haɗe da ƙyama..

Cire glass ɗin dake idanunta Salima tayi, haɗe da watsamawa Zahrah wani irin kallo mai ɗauke da mugun tsana, cike da ƙyama ta furzar da yawu, haɗe da kallon Laura "Itace wan nan?" Salima ta tambaya tana me nuna Zahrah da hanunta cike da taƙama.

"Eh itace ƴar matsiyata" Laura ta faɗa tana yanatsina fuska.

"Lafiya kuwa bayin Allah? su waye ku? Zahrah ko kinsan sune?" Inna da fitowarta a ɗaki kenan ta tambaya, Tana me mamakin ganinsu haɗi da aljabi.

"Ba alkhairi bane ya kawomu, saboda baku kai matsayin da zamuzo muku da alkhairi ba, sunana Salima, nazone domin najawa wannan matsiyaciya kuma karuwar ƴar taku kunne, koda wasa Doctor Sadeeq basa'an aurenta bane, saboda yawuce ajin macen da taraba mutuncinta a titi" takawa taci gaba da yi cikin isa harta ƙarasa gaban Zahrah, da ta kasa ko motsi... "Banzo danna cutar dake ba, amma tabbas idan kika sake nakuma dawowa cikin gidan nan to zanyi miki babban illa, rabuwa dashi zai fi miki, idan kuma kika ƙi, hmmmm zakisan cewa bakin rijiya bawajen wasan makaho bane, bake kaɗaiba, hatta tsohon da yake riƙe dake sai ya ɗanɗana" Salima tana kai ƙarshen zancen nata tamaida glass ɗin ta dake riƙe a hanunta, haɗe da kallon su Laura "Muje" tace dasu, babu musu kuwa suka rufa mata baya, suna tafiya suna kareraya...

Tamkar statue haka Zahrah tayi ƙasaƙe tana kallonsu, harsuka fice daga cikin gidan.

Sallallami Inna tashiga yi haɗe da tafa hannuwanta duka biyu, "Lallai kuwa wa ƴan nan ƴan iska masu jajayen fuskar suncika marassa ta'ido, rashin kunya har cikin gida" Inna tafaɗi haka cike da mamaki.

Kai kawai Zahrah ta girgiza, haɗe da jawo kwanon abincinta ta ci gaba da ci, batare da ta tankawa Inna da take ta ɓaɓatu ba,, sai dai kuma sosai maganganun Salima suka daki zuciyarta, har wani ɗaci takeji a cikin maƙoshinta.. Tura abincin takeyi amma jinsa take tamkar maɗacin dayafi kowanne ɗaci, har wani zafi takeji a ƙirjinta. Tana gama cin abincin, ta kora da ruwa, haɗe da tashi kai tsaye tanufi ɗakinta.

"Karuwa" sunan da Salima taƙirata dashi yafiye mata komai ciwo, tunda take a duniya ba'a taɓa ƙiranta da sunan karuwa ba, sai a yau ɗin, wasu irin zafafan hawayene taji sunshiga gangarowa daga cikin idanunta, durƙushewa tayi a ƙasa haɗe da soma rusa kuka, filla filla kalaman da Salima ta faɗa mata suke dawowa cikin kanta, koda wasa bata taɓa tunanin za'afaɗi kalma na ɓatanci masu muni irin haka akan ta ba.

"Kacuceni Zaid, Kacuceni, me yasa ka aikata haka agareni, shin koda sau ɗaya ne bakayi tunanin yanda rayuwata zata kasance ba, bazan taɓa yafe maka ba Zaid har kuwa nakoma ga mahaliccina" cikin kuka ta ƙare maganar, domin kuwa sai yau tasake tabbatar da cewa Zaid ya cuceta, takuma ƙara jin matsanancin zafi dakuma ciwo akan fyaɗen da Zaid yayi mata.. Abu kamar wasa haka Zahrah tayita kuka tamkar ranta zai fita, sai gashi cikin mintuna ƙalilan ciwon kai yakawomata ziyara, wanda har sai da yakaita ga kwanciya.. Ƙiran Dr.Sadeeq ne yashigo cikin wayarta amma tanaji tana gani takasa picking call ɗin har wayan ta tsinke, taƙi ɗaga wayan ne kuma don bataso yafahimci cewa tana cikin damuwa. Wani ƙiran nasa ne kuma yasake shigowa, still dai har wayan ta katse, Zahrah bata ɗauka ba, domin har yanzu bata dawo cikin nutsuwarta ba.. Ƙira na uku ne yakuma shigowa cikin wayarta ta, ƙoƙari tayi wajen ɓoye damuwarta haɗe da ɗaukan wayar ta kara akan kunnenta..

SHU'UMIN NAMIJI !!    (completed)Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt