Chapter 64

5.7K 479 34
                                    

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*SHU'UMIN NAMIJI !!*


*Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Lovely Brother KHABIER*

*🌈Kainuwa Writers Association*

_{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain and motivate the mind of readers}_

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

*WATTPAD*
@fatymasardauna


*CHAPTER 110*

A matuƙar ruɗe yake girgizata, yana me ƙiran sunanta, sosai ya tsorita da al'amarinta, gaba ɗaya ya ruɗe, yama manta da cewa shi ɗin likita ne, sungumarta yayi acikin ƙirjinsa, direct sai cikin mota, a gidan baya yasakata, yafigi motar da wani irin gudu, saboda tsabar gudun da yakeyi, mintuna kaɗan, suka kawoshi, cikin asibitinsu, a ruɗe yaje wajan, abokin aikinsa Dr.Salim, yasanar masa abun dake faruwa, emergency aka wuce da ita direct, shikam Dr.Sadeeq kasa shiga cikin emergency room ɗin yayi, suke karɓan emergency patient idan aka kawo, amma kuma sai yau, gashi shine da kansa ya kawo, sai kaikawo yake tayi, aƙofar shiga emergency room ɗin, kwata kwata hankalinsa baya jikinsa..

Bayan Mintuna 30

Yana tsaye ajikin bango, idanunsa a lumshe suke, zuciyarsa kuwa, bugawa takeyi da ƙarfi, tamkar zata faso cikin ƙirjinsa, ta fito.

Dr.Salim da sauran doctors, ɗinne suka fito daga cikin ɗakin, har yanajin tuntuɓe, agarin saurin ƙarasawa inda suke.

"Salim ya ya take? tafarfaɗo ne? Meke damunta dan Allah? Allah Yasa tana lafiya?" Duka waƴannan tambayoyin, Dr.Sadeeq ya jerawa Dr.Salim su.

Murmushi Salim yayi, haɗe da sanya hanunsa, ya dafa kafaɗan Dr.Sadeeq.
"Haba Man, saikace ba doctor ba, duk kabi ka ruɗe, bawata babbar matsala bace bafa, kaida kanka ma zaka iya maganceta, amma duk karuɗa kanka"

Ajiyar zuciya me ƙarfi, Dr.Sadeeq ya sauƙe, sakamakon jin daɗin kalaman da Dr.Salim yayi.

"Masha Allah! kada kaga laifina, wallahi Salim, inasonta sosai ne, banason wani abu, ya sameta shiyasa" Dr.Sadeeq yafaɗi haka, yana me lumshe idanunsa.

Murmushi Salim yayi, haɗe da cewa. "Muje office"
Babu musu Dr.Sadeeq yabi bayan Salim, suka wuce office ɗin Salim ɗin.

Suna shiga suka zauna, su dukansu akan kujera ɗaya, murmushi Salim yayi haɗe da maida kallonsa ga Dr.Sadeeq, hanu yasa ya dafa kafaɗan Dr.Sadeeq ɗin, cikin son kwantar masa da hankali yace.
"Kada ka damu Sadeeq, ba wani abu bane, tsananin tsorone kawai, ya sata suma, amma bayan haka babu wani ciwo dake damunta, sai dai naga tana da hawan jini, amma kuma gaskiya abokina, ka iya aiki, wai ma watanku nawa da aure ne yanzu?"

Harara Dr.Sadeeq, ya jefawa Salim. "Wannan wani irin iskanci ne Salim? me ya haɗa ciwonta da tambayan watannin auren mu? yanzu ba lokacin wasa bane, ina tsananin son matata, bana ƙaunar naga wani abu yasameta, idan akwai wani abu bayan wannan, ka sanar dani, idan kuma kaƙi zan bincika da kaina, daɗin abun nima likita ne" Dr.Sadeeq yafaɗi haka, yana me ƙoƙarin miƙewa tsaye, sarai yasan iskancin Salim, iya shegensa yayi yawa, gwamma ma yaɗauki Zahrah'nsa, kawai su koma gida, inyaso shida kansa, zaiyi checking ɗinta agida, dama ruɗewan da yayine, yasanya ya kawota asibiti.

Hanunsa Salim ya riƙe haɗe da cewa.
"Meyayi zafi kuma? daga tambayar watannin aure, yanzu duk ba wannan ba, miye tukuicina wanda zaka ban, idan nafaɗama wata magana me daɗi?"

"Tukuici kuma? wace magana me daɗi kenan? nida matata bata da lafiya, har akwai wata magana da za'a faɗamin wacce zatayimini daɗi? nace maka kadaina min wasa ko Salim, yanzu ba lokacin wasa bane." Injicewar Dr.Sadeeq.

SHU'UMIN NAMIJI !!    (completed)Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon