👸👸 QUEEN FARHA👸👸👸 Matar sarki👸

8.2K 256 7
                                    

*🅱RILLIANT WRITERS ASSOCIATION🖊*
( _Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers_)




👸🏻👸🏻 *QUEEN FARHA* 👸🏻👸🏻
          👸🏻 *Matar Sarki* 👸🏻

                      

  Writing
              And
                    Story

*FAUZIYYA TASI'U UMAR*
® *FAUZAH*


*Wattpad👉🏻* *realfauzahtasiu*

MARUBUCIYAR

JAGORAN RAYUWA
AMINIYA KO KISHIYA
FADIMATUL ZAHRAH
HABIBULLAH
 

WANNAN SHAFI NA MUSAMMAN  NE DOMIN  SADAUKARWA NE GA QUNGIYARMU MAI ALBARKA TA  BRILLIANT WRITTERS ASSO..., WADDA TA QUNSHI  FASIHAN MARUBUTA DA AKE  ALFAHARI DASU A DUNIYAR  ONLINE WRITTEN ALLAH YA QARA DAUKAKA MU YA RABAMU DA SHARRIN  MAQIYA DA MAHASSADA AYI DAMU YAU  AYI DAMU GOBE HAR JIBIN GATA YAZAM MUNE DAI AKE GANI.

SADAUKARWA GAREKU

HALIMATUS SA'ADIYYA MUHAMMAD (COPPER DAN BAUTAR MATA)

JAMILA MUSA (KWARATA)

SURAYYAHMS ( AHUMAGGAH)

ASMEENAT ZEEYAN (RAYUWAR BANUJJAH)

REAL OGANNIYYAH

SISTER LEEMART

MARYAM (YAR BUZUWA)

AND OTHERS

INA JINJINA MUKU DAMIN KUMA KUNA JINJINA MIN

AUNTY BILKISU (MAMAN ABBA KD)

AISHA GAIDAM

FALTEX FARHANA

MMN NABIL

UMMUH SAFWAN        

NAEEMA BALA

HAJJARAH HUSSAIN

HAJJARA IBRAHIM &

KAJURU
     

*BISMILLAHIR RAHAMANUR RAHIM*



🅿1⃣

Yarinya ce qarama da bazata wucce 14 zuwa 15 ba tana tafe cikin uniform din islamiyyar ta da yasha guga tana tafe tana yauqi tana yatsina kamar wata macijiya “Farha! Farha!! Ke Farhana wai ba mgn ake miki bane kika share mutane” tsayawa tayi cak daidai wani dan gulbi da ruwan damuna ya tare a gefan titin ta kebe baki zatayi bala'i kenan wata zindimemiyar mota qirar Jeep tazo giftawa kawai bisa tsautsayi taji ruwa facal a jikinta saurin kallon jikinta tayi tare da cewa “ kam ubancan wlh yau zanyi rotse dagowar da zatayi taga motar tayo ribas a hankali, wawurar wani dutsi tayi ta wulwula kawai sai saman glass din motar ji kake tatsatsaarr da sauri mutun biyu da suke cikin motar suka fito kasancewar gurin babu yalwar mutane sosai yabawa dayan ma damar fitowa daga motar ya tsaya jikinta ya zuba musu ido.

Daya cikin mutanen ta sanya hanu ta cukuma tana surfa bala'i tana cewa“ku wadannan irin unliterers ne kuna tafiya kamar makafi bakusan haqqin hanyaba balle me tafi a qasa daqiqan banza daqiqan wofi wannan ma ai zalinci ne yanzu kunjamin yauma sainayi wankin uniform bayan...” saukar mari taji a kuncinta tayi saurin dafe gurin tare da cewa“Allah ya isana mugu azzalumi kuma wlh bazan fasa fadaba ba ku jahilai ne baku da ilimi Kona sisi” sake daga hanu yayi zai yarfa mata mari can a bayansu taji ance  “Na'im karka qara mace ce fah kuma yarinya qarama kuzo mu tafi” juyawa tayi ta kalleshi gabanta taji ya fadi amma saboda bala'in da yake cinta haka ta taka tana daga hijjab dinta saboda tsoron kada ya manne mata a jiki ta qarasa gabansa ta qare masa kallo a-z sannan tayi tsaki tace.

👸👸 QUEEN FARHA 👸👸👸Matar sarki👸Where stories live. Discover now