4

996 53 1
                                    

*NAYI DACE*

Maryam💕
Wattpad@mamsuhaimerh

*IV*
         Not only vote,comment Domin nasan me kukeso tunani akan abinda na rubuta,tnxx

D'auke kwanon abincin gabana
yayi yace

"Idan kina cin abinci saboda fushi to kin kusa yin kiba,nikuwa bazanyi kanwa da lukuta ba"

Dariya nayi ba tareda nace komai ba,anan muka zauna muka sha Hira Kala kala,Yana bani labarin shagonsu na kfintanci Ina bashi labarin aikina,Ina jin dad'i sosai yanda yake nuna shaawar karatuna

Har saida aka Kira magrib sannan ya tashi Domin ya tafi,rakashi nayi har gate Ina mamakin yau wani irin zance nayi?

Kwashe kwanukan nayi Ina shiga d'aki umma tace

"Sai yanzu?"

"A'a tuntuni sulaiman ya tafi Saleh ne ya zauna mukayi Hira"

"Okay" umma ta fad'a Tana tada sallah,nasan baza tayi wani tunani ba Domin Saleh kaman da take a wurinta,Domin tun secondary suka manne da jabir har yanzu

Sallah nayi Ina idarwa na zuba tagumi Ina tunanin irin cakwakiyar da nake Shirin hadawa kaina,nasan idan ba wani miracle din ne zai faru ba sulaiman shine mijina,Amma meyasa zan sakawa raina son Saleh?Allah yasa attraction ne kawai,Domin idan sonshi nake nasan zansha wuya,Domin ban iya so ba

Ina wannan tunanin naji sallamar su zulaihat tareda sallamar baba,fita nayi na gaidashi baba yace na d'auko masa abinci yunwa yakeji

Tare da su zulaihat muka shiga kicin d'in,jingina nayi zulaihat tace

"Albishirinki,baba ya kawomin wani"

Flask din abincin baba na d'auka nace

"Wannan zumudin naki da alamu yayi miki"

Har wani tsalle tayi Cike da murna tace

"Ai alhamdulillah ya had'u wallahi,xuwansa na farko bazaki ce lokacin muka fara Hira ba,ya iya Raha da barkwanci"

"Kinyi sa'a,nikuwa wani Dan iska baba ya turo,Bari muje d'aki na baku labari"

Daukan tray din nayi na fita dashi,samin albarka baba yayi ya kalli mama yace

"Kinga kuwa munyi magana akan masu zuwa wurin yarannan,habibu yace yafiso ayi komai da wuri"

Ji nayi gabana ya fad'i Colin sauri nabar wurin Ina dafe kirji,a Kan gadona na samu su zulaiha da rukayya,zama nayi na fara musu bayanin sulaiman da Kuma abinda naji baba ya fad'a yanzu,saidai na boye musu abinda nakeji game da saleh

Kallon juna sukayi rukayya tace

"Ni Ina ganin ruwan wajen ne bai sakeshi ba,ki fara daurashi a hanya sai kiga an Dace"

Kwanciya nayi nace

"Allah yasa,ke zulaiha bamu bayani,ke Kuma rukayya Babu ke ne a rabon?"

Murmushi tayi tace

"Harda ni,Amma ya fadamin zai Karo karatu ne sai bayan shekara biyu,Amma kullum muna waya,har video call munayi baida matsala gaskiya,Kuma sau d'aya dai yazo yacemin zai le'ko weekend,Yana can maiduguri"

Allah sarki,ni kadai ce banyi Dace ba,zuba musu ido nayi suna Koda mazajen da baba yayi musu,saidai ni Saleh kawai nake gani a idona

Washegari jabir da ya daukoni daga aiki ban ganshi da Saleh ba,tambayarsa nayi ya sanar dani ya tafi kotu Ana raba musu gadon mahaifinsu da ya rasu shekara daya baya

Haka mukayi tafiyarnan babu wani dad'i,ko da mukaje gida sai naga gidan yayimin wayam da yawa,gizo ya faramin Ina Jin kaman sallamarsa,duk nayi sanyi tun Ina zuba Ido har na Dena

NAYI DACE.Where stories live. Discover now